Real Madrid za ta kara da RB Leipzig a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
RB Leipzig za ta fuskanci Real Madrid gida da waje a zagaye na biyu a Champions League na bana.
Mai rike da kofin bara, Manchester City za ta kara da Copenhagen da wanda za a yi tata burza tsakanin Arsenal da Porto.
Copenhagen, wadda ta yi ta biyu a rukunin farko da Manchester United take, ta kai zagaye na biyu a karon farko tun 2011.
Za a fara wasannin farko tsakanin 13-14 ko 20-21 ga watan Fabrairu, sannan a buga zagaye na biyu daga 5 -6 ko kuma 12-13 ga watan Maris din 20224.
City da Arsenal za su fara wasannin farko a waje, kamar yadda gasar take duk wadda ta ja ragamar rukuni za ta fara wasan farko a waje a zagaye na biyu.
Sauran wasannin da za a kara Inter Milan - wadda ta yi ta biyu a gasar bara za ta hadu da Atletico Madrid da gumurzu tsakanin Bayern Munich da Lazio.
Jadawalin Champions League zagaye na biyu:
- Porto da Arsenal
- Napoli da Barcelona
- Paris St-Germain da Real Sociedad
- Inter Milan da Atletico Madrid
- PSV Eindhoven da Borussia Dortmund
- Lazio da Bayern Munich
- Copenhagen da Manchester City
- RB Leipzig da Real Madrid
Arsenal mai buga Premier League, wadda ta ja ragamar rukuni na biyu, wadda ba ta taba daukar Champions League ba ta doke Porto 5-0 a Emirates a 2010.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Porto ta ci wasa hudu daga shida a rukuni na takwas, wadda ta kare a mataki na biyu da maki iri daya da na Barcelona, wadda ta yi ta daya.
Man City ta lashe dukkan wasanninta na cikin rukuni, ita kuwa Copenhagen, wadda ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Man United daga baya ta ci 4-3, ita ta yi ta biyu a rukunin farko da Bayern Munich ta daya.
Kaka shida da ta wuce City tana kai wa zagayen kungiyoyi 16 da suke ci gaba da wasannin.
Jadawalin da aka raba ranar Litinin ya amfani kungiyoyin Ingila biyu, abinda ya rage musu yadda za su taka rawar gani a gasar, bayan da aka fitar da Newcastle United da Manchester United.
Arsenal ta yi nasarar doke Porto a wasa uku baya da suka kara, amma Gunners ba ta taba cin Porto a Estadio do Dragao.
Man City ta fafata da Copenhagen a karawar cikin rukuni a bara, inda ta tashi 0-0 a Denmark, sannan ta dura 5-0 a Etihad.
Jadawalin gasar Europa League wasannin zagaye na biyu
Haka kuma a ranar ta Litinin an raba jadawalin zagaye na biyu a Europa League.
Za a fara wasannin farko ranar 15 da kuma karo na biyu ranar 22 ga watan Fabrairun 2024.
- Feyenoord da Roma
- Lens da Freiburg
- Benfica da Toulouse
- Galatasaray da Sparta Prague
- AC Milan da Rennes
- Young Boys da Sorting Lisbon
- Sporting Braga da Qarabag
- Shakhtar Donetsk da Marseille











