Gwamnan Jihar Imo ya biya manoma albasa diyyar naira miliyan 10

.

Kungiyar manoman albasa ta Najeriya tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Imo da ke kudancin Najeriya Hope Uzodinma, ya biya wasu daga cikin ƴaƴan ƙungiyar naira miliyan goma diyya biyo bayan asarar da suka tafka a bara.

Manoman sun tafka asarar ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai masu hari a kasuwar sayar da albasa da ke Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise da ke Jihar Imo.

Haka zalika an bayyana cewa gwamnan ya kuma bai wa masu sayar da shanu da lamarin ya shafa naira miliyan 20 a matsayin diyya.

Halilu Muhammed, wanda shi ne shugaban kungiyar ta masu nomawa da sarrafa albasa reshen Jihar Imo, ya shaida wa BBC cewa asarar da manoman suka tafka ta wuce ta miliyan goma, inda ya ce ta kai ta sama da miliyan 13 amma a cewarsa gwamnan ya ce "ba za a yi ɓari a kwashe duka ba".

Halilu Muhammad ya ce a halin yanzu miliyan goman da suka samu, tuni shugaban ƙungiyar manoma albasa ta Najeriya baki ɗaya Aliyu Maitasamu Isa ya kasafta su inda ya bai wa waɗanda lamarin ya shafa.

"Duk mai buhu ɗaya ya samu kuɗinshi, an kira mutanen Sokoto an tabbatar wa kowa an ba shi kuɗinshi, in ji Halilu.

Haka kuma ya ce gwamnan jihar ya ba su tabbacin cewa irin haka ba za ta sake faruwa ba inda ya ce tun bayan iftila'in da ya faru da su, gwamnan ya ƙara tsaurara tsaro a wuraren da suke sana'ar tasu.

Haka kuma ya ce duk da haɗurra da sukan faɗa ciki sanadiyyar hare-haren ƙungiyoyin ƴan bindiga, ƙungiyar tasu za ta ci gaba da kai hajarta zuwa kudancin kasar.