Chelsea ta sayi Quenda da Essugo daga Sporting

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta kammala ɗaukar 'yanwasa Geovany Quenda da Dario Essugo daga ƙungiyar Sporting ta Portugal kan kuɗi kusan fam miliyan 62.4.
Sporting ta ce kuɗin ɗanwasan gefe Quenda mai shekara 17 ya kai kusan fam miliyan 44, amma kuma sai an kammala kakar wasa ta baɗi 2025-26 sannan zai koma Chelsea.
A wannan kakar matashin ya fara buga wa babbar ƙungiyar Sporting wasa, har ma ya fara buga gasar zakarun Turai ta Champions League a watan Satumba.
Essugo mai shekara 20 kuma ɗanwasan tsakiya ne, wanda zai koma Stamford Bridge a ƙarshen wasa ta bana bayan buga wasan aro a Las Palmas ta Sifaniya. Sporting ta ce kuɗin da aka saye shi sun kai fam miliyan 18.4.
Ya yi ƙoƙari a Sifaniya duk da jan kati biyu da aka ba shi a wasansa huɗu na farko.
Essugo zai haɗe da mai horarwa Enzo Maresca yayin buga sabuwar gasar Kofin Duniya ta Kulob-Kulob a Amurka.
Ɗanwasan biyu ne na baya-bayan nan da Chelsea ta ɗauka bayan 'yan shekara 17 biyu da ta sanar da ɗauka a bazarar bana.
Ɗan Brazil Estevao Willian da ɗan Ecuador Kendry Paez za su koma Chelsea a bazara mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images











