Sojojin Kenya da ba a samu labarinsu ba tun bayan tafiya yaƙin duniya

Wani tsohon hoto kenan, inda wasu mutane shida da suka tsaya, don a dauke su hoto. Ɗaya daga cikin su na sanye da holar soji irin ta Turkiya.

Asalin hoton, National Army Museum

Bayanan hoto, Dubban sojojin Kenya ne su ka taya sojojin Birtaniya yakin duniya
    • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wata ranar, kimanin shekaru 85 da suka gabata, Mutuku Ing'ati ya bar gidansa da ke kudancin Kenya, wanda tun daga sannan ba a kuma ganinsa ba.

Mr. Ing'ati da sukarunsa ba su wuce 30 da ƴan kai ba, ya yi ɓatan dabo ba tare da wani cikaken bayani ba, tsawon shekaru danginsa sun yi iya ƙoƙarinsu wajen gano inda yake, ta hanyar bin dukkan wasu bayanai da suka samu da suke fatan zai iya kai wa ga gano inda yake, suka ƙure musu.

Bayan wucewae gwammanon shekaru, an fara mantawa da Mr Ing'ati. Bashi da ƴa ƴa kuma da yawa daga cikin waɗan da suke da kusanci da shi sun mutu. Sai dai bayan kusan shekru 80, kwatsa, sai sunan sa ya futo a wata rajistar sojin Birtaniya.

Hukumar kula da ƙaburburan mayaƙa rainin Birtaniya wato Commonwealth War Graves Commission (CWGC), da ke aiki don tunawa da waɗan da suka mutu, a yaƙin duniya biyu da aka yi, sun tuntuɓi ɗan ga ɗan uwan mr Ing'ati, Benjamin mutuku, bayan nazarin wasu tsofaffin takardu.

Ya ce ya sami bayanai cewa, ranar da kawun nasa ta bar ƙauyensu, yayi tafiya mai nisan kilomita 180 (mil 110) yamma da Niarobi, inda gwamantin birtaniya da ke milkin mallaka a ƙasar.

Anan ne suka yi rajista a matsayin ƴan Scouts masu zaman kansu a yankin Gabashin Afrika, wani sashe na dakarun birtaniya da suka yi yaƙin duniya na biyu. Sojin Britaniya sun dauki miliyoyin maza daga yankin zuwa yaƙe-yaƙen duniya a ƙarini na 20.

Abun d abai iya futowa fili ba shi ainihin lokacin da shi Mr Ing'ati ya amince da shiga aikin, idan kuma a ranar 13 Yunin 1943 aka halaka shi yana tsaka da gwabza yaƙi, kamar yadda bayanan CWGC.

Hoton wata tsohuwar takarda. Ɗauke da bayanan sojojin Kenya a ƴan Scouts a yankin Gabashin Afrika,

Asalin hoton, CWGC/Kenyan Defence Force/British Library

Bayanan hoto, Wani kundi da ke nuna jerin sunaye wandan da aka shigar da sunayensu rajista a matsayin ƴan Scouts masu zaman kansu a yankin Gabashin Afrika,

Kamar dubban ƴan Kenya da suka yi yaƙi a ƙarƙashin sojin Birtaniya, ya mutu ba tare da an sanar da danginsa ba, sannan aka binne shi a wani waje da ba a sani ba, har kawo yanzu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

tsawon gomman shekaru, Birtaniya ke bikin tunawa da yan mazan jiya da suka bayar da gudunmawa a yakin, da irin saudakar da kai da dakaru masu yawa na Kenya, irinsu Mr Ing'ati suka bayar da, ba a iya ganin irin bajintar da suka yi ba.

Duniya ba ta san irin rawar da suka taka ba, domin kuwa ba a bikin tunawa ko girmama su ba kamar yadda ake yi wa takwaraorinsu fararen fata ba.

Bayan tsawon waɗan nan shekaru, Mr Matuku, ya ji daɗin gano inda kawunsa ya ɓata, da lokacin da ya mutu. duk da cewar an haife shi bayan Mr. ing'ati ya bar ƙauyensu, Mr Mutuku na ji a jikansa cewar akwai dangantaka mai ƙarfi tsakaninsa da kawunsa, wanda aka sa masa sunansa.

"Na kan tambayi mahaifi na, ina mutumin da aka sa mun sunansa? Mr Mutuku da yanzu shekarunsa 67 ya ce shaidawa BBC.

Duk da cewar ya yi maraba da waɗan nan bayanai, Mr Mutuku na jin haushin cewar gawar kawunasa na chan uwa duniya, ba a binne shi ba a Syamatani.

Danginsa daga ƙabilar Akamba, da ke da al'adar binne mamaci, a kusa da gidan danginsa, na da matuƙar mahimmanci.

"Ban sami damar ganin ƙabarin kawunsa ba,," a cewar Mr Mutuku. "Na so a ce na ga hakan,".

"I never got a chance to see a tomb where my uncle got buried," Mr Mutuku says. "I would have liked so much to see that."

Benjamin Mutuku na tsaye a gabanin gidansa. Ya na sanye da riga taguwa mai gajeren hannu, ya dafa wata fulawa da ke kusa da inda yake tsaye.

Asalin hoton, Nellyson Mutuku

Bayanan hoto, Benjamin Mutuku, da aka raɗa masa sunan kawunasa Mutuku Ing'ati, na neman buƙatar ƙarin bayanai na yadda kawunsa ya mutu

Hukumar CWGC na ƙoƙarin gano idan Mr Ing'ati ya mutu, da inda aka binne gawar tasa, tare da bayanan sauran sojojin Kenya da aka manta da su.

haka kuma anan ci gba da neman bayanai na ƙarin wasu yan yankin gabashin Afrikan da suka mutu a lokacin yaƙin duniya na ɗaya.

Da taimakon hukumar tsaro ta Kenya, Hukumar ta CWGC a baya-bayan nan, ta haƙo wani abu mai daraja na bayanan na sojin mulkin malaka da ba a fiye samu ba, da suka shafi wannan yaƙin. Wanda hakan ya sa ma su bin cike su ka iya gano sunayen da labarin fiye da sojoji dubu uku da suka yi aikin soji a wannan chan lokaci.

Bayanan, waɗan da a baya aka yi tunanin cewar ana lalata su, gomman shekaru da suka gabata. Sun dai haɗa da sojojin Gabashin Afrika, rundunar da ta yi yaƙi da dakarun Jamus a yankin, a yankin da yanzu ake kira Tanzaniya, dakarun Japan da yanzu ake kira da Myanmar a yaƙin duniya na biyu.

"Ba iya fayil ba ne da kawai yayi ƙura ba, takarda ce da ta ƙunshi bayanai na ƙashin kai. Ga dangi masu yawa a Afrika, wannan zai iya zama karo na farko da suka taɓa samun bayanai na wasu makusantansu kan lokacin yaƙi, " kamar yadda George Hay, wani masanin tarihi a CWGC ya shaidawa BBC.

Misali, akwai George Williams, da aka naɗa sajan manjo na rudunar sojin sarauniya a Afrika. An bayana shi da yana da tsayin ƙafa 5 da inci 8 (170cm), da ke da tabo a kumatunsa na dama, Mr Williams ya sami lambar girmamawa masu yawa saboda irin bajintar da ya yi, kuma aka sahida kwarewarsa wajen iya harbi. Ya mutu yana da shekaru 44, a Mozambique, wattani hudu gabanin a ƙare yaƙin.

Sannan akwai bayanai na Abdulla Fadlumulla, wani sojan Uganda, da shi ma ya shiga aikin sojan sarauniya na Afrika a 1913, a lokacin yana da shekaru 16. An kashe shi wattanin 13, a lokacin da ya ke kai hari kan abokan gaba a Tanzania.

Hoton wata tsohuwar takarda ruwan ƙasa. Tana ƙunshi bayanai na sojan Uganda Abdulla Fadlumulla.

Asalin hoton, CWGC/Kenyan Defence Force/British Library

Bayanan hoto, Bin cike ya haƙo dubban tsofafin bayanan na soji

Bayanai dai sun nuna yadda yaƙin ya " taɓo ɓangaroro daban daban a Kenya", a cewar Patrick Abungu, wani masanin tarihi a ofishin CWGC da ke Kenya.

"Saboda labarin yadda ya ke shi ne, sun tafi amma ba su dawo ba. Yanzu gashi mun amasa waɗan nan tambayoyi: ina suka je, ina gawar ta su ta ke," ya ƙara.

Masanin tarihin na son baiwa dubban dangi masu yawa a Kenya, amsoshin wadan nan tambayoyi, ciki har da na sa.

Kawunsa Ogoyi Ogunde, shi ma an shigar da nasa bayanan cikin kundin sojojin birtaniyar, a lokacin yaƙin duniyar na ɗaya, kuma bai dawo gida ba.

"Abun ne mai mutuƙar damuwa ka rasa waɗan da ke ke so, kuma baka san idan suke ba," ya na mai shaidawa BBC.

"Ba abin da muwa ba ne irin tsawon shekarun da aka ɗauka ba, tabbas mutane na ta duba kofa da fatan wata rana zai dawo gida."

Mr Abungu da CWGC na fatan gina wani dandali na tunawa da jarumtar da dubban sojojin da aka gano a baya bahaun a cikin takardun.

Wani Hoto da ke nuna wasu sojoji na ƙoƙarin harab igwa

Asalin hoton, National Army Museum

Bayanan hoto, Sojojin Sarauniya, da aka ɗauki hotansu a 1914, da suka gwabza yaƙi a sassan duniya

Hukumar dai tana kuma so ta ajiye bayana don taimakawa wajen shigar da shi cikin tsarin koyarwa na Kenya, don yan ƙasar masu tasowa, su fahimciirin gudnumawar da irinsu suka bayar, da rawar da ƴan Afrika suka bayar a yaƙi duniya da aka yi.

"Mafita a irin wannan yanayi shi ne, ba wai tana zuwa ne daga mutane iri na da ke cewa "wannan shi ne tarihin ka," a cewar Mr Hay na CWGC.

"Batu ne na mutane su ce 'wannan tarihin mu ne, kuma su yi amfani da bayanan da muke aiki akansu."

Hukumar ta CWDC za ta ci gaba da tattara wadan nan bayanai, na dukkan ƴan kenyan da suka yi aiki a ƙarƙashin dakarun Sojan Birtaniya, har sai an girmama wadan da suka mutu a lokacin yaƙin duniyar na ɗaya da na biyu.

"Babu wata rana da aka iyakance na kammalawa.. zaa iya daukar shakaru kusan dubu," a cewar mr Abungu.

"Tsarin da ake bi shi ne a tabbatar cewar dubban mutanen da suka tafi amma basu dawo ba, a ci gaba d atunawa da su, don kar a manta da su."