Hotunan jana'izar Muhammadu Buhari a Daura

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talata ne aka yi jana'izar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura, inda isar gawar zuwa filin jirgin sama na birnin Katsina daga birnin Landan.

BBC ta tsakuro wasu hotunan na yadda jana'izar ta wakana.

Buhari

Asalin hoton, Rahma Abdulmajid/Facebook

Bayanan hoto, Yadda aka sauko gawar Muhammadu Buhari daga jirgin shugaban ƙasa bayan isar gawar daga birnin Landan.
Buhari

Asalin hoton, Rahama Abdulmajid/facebook

Bayanan hoto, Lokacin da sojoji ke wucewa da gawar Muhamamdu Buhari bisa rakiyar Shugaba Tinubu domin faretin bangirma.
Jana'izar Buhari

Asalin hoton, Rahma Abdulmajid/Facebook

Bayanan hoto, Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima na yi wa gawar Muhamamdu Buhari rakiya a lokacin da ake yi masa faretin bangirma a filin jirgin saman Katsina bayan sauka daga Landan.
Jana'izar Buhari

Asalin hoton, Miqdad/Facebook

Bayanan hoto, Faretin bangirma da girmamawa da sojojin Najeriya suka yi bisa umarnin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jana'izar Buhari

Asalin hoton, Miqdad/Facebook

Bayanan hoto, Yadda aka saka gawar Muhammadu Buhari a motar ɗaukar gawa bayan yi mata faretin bangirma zuwa Daura inda aka binne shi.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Shugaba Tinubu yana kaisuwar bangirma ta ƙarshe ga gawar Muhammadu Buhari
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Lokacin da aka ajiye gawar Muhammadu Buhari a gaban kabarin da za a binne shi a ciki, inda kuma ake karanta tarihin tsohon shugaban kafin binne shi.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar da shugaba Bola Ahmed Tinub;da gwamnan Malam Dikko Radda; da ɗan gidan Buhari, Yusuf Buhari da sauran mahalarta jana'izar marigayi Muhammadu Buhari a Daura.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Lokacin da ake shirin naɗe tutar Najeriya da aka naɗe gawar Buhari tare da hula da takalmi da kuma takin girmamawa domin bai wa Shugaba Tinubu ya miƙa wa iyalin Buhari.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Shugaba Tinubu yana miƙa wa Yusuf Buhari tutar Najeriya wadda aka naɗe gawar Muhammadu Buhari a ciki da takalmi da hula da takobin girmamawa.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Nan sojoji ne suke ninke tutar Najeriya wadda aka naɗe gawar marigayin domin miƙa ta ga iyalan mamacin.
Yusuf Buhari, ɗa ga marigayin ya kasance a gaba wajen jana'izar mahifin nasa.

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Yusuf Buhari, ɗa ga marigayin ya kasance a gaba wajen jana'izar mahifin nasa.
..

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Maiɗakin marigayi Muhammadu Buhari, Aisha Buhari tana lallashin ƴar marigayin, Zahra Buhari wadda ke alhinin rashin mahaifinta.