Napoli na son de Bruyne, watakil Rashford ya koma Barcelona

Lokacin karatu: Minti 2

Napoli na son dan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne mai shekara 33, idan kwantiraginsa da Manchester City ya kare a kakar nan. (Times - subscription required)

De Bruyne na son ci gaba da zama a Turai, kuma da alama Aston Villa na daga wadanda za su bayyana makomar dan wasan nan gaba. (i paper)

Napoli dai na sanya ido kan dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Manchester City, Jack Grealish mai shekara 29. (Sun)

Dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Manchester United, Marcus Rashford, 27, da k zaman aro a Aston Villa, na son komawa Barcelona a kakar nan. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan baya na Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong na da sama da fam miliyan 29 a kwantiraginsa, hakan ya janyo garabasa ga Liverpool da ke son dan wasan na Netherland, mai shekara 24. (Talksport)

Kungiyoyin Liverpool, Arsenal da Manchester City duk na tuntuba kan dan wasan Brazil Rodrygo, 24, mai taka leda a Real Madrid. (Tbrfootball)

Crystal Palace na da karfin gwiwa kan dauko dan wasan tsakiya na Ingila, Joe Willock mai shekara 24, daga kungiyar d ya ke takawa leda wato Newcastlea kakar nan. (Chronicle Live)

Borussia Dortmund ta bi sahun kungiyoyin da suke zawarcin matashin dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Sunderland, Jobe Bellingham, mai shekara 19, wanda ake rade-radin kungiyar Manchester United na zawarcinsa. (Talksport)

Aston Villa ba ta son yin asarar fam miliyan 90, kan dan wasan tsakiya na Ingila Morgan Rogers, wanda kungiyar Chelsea ke so, sai dai dan wasan mai shekara 22 ya ce zai koma wata kungiya da zarar ya ga wadda ta yi ma sa. (Teamtalk)

Al Hilal ta nuna sha'awa kan dan wasan Uraguay, mai taka leda a Liverpool Darwin Nunez mai shekara 25, da kuma dan wasan Clombia, Luis Diaz mi shekara 25. (Caught Offside)