Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne ba zai bar Man City ba - Guardiola
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya sanar cewar fitatcen ɗan wasa Kevin de Bruyne ba zai bar ƙungiyar Etihad ba.
Ana ta alakanta De Bruyne da cewar zai bar City a bana, zai koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.
Ɗan wasan tawagar Belgium, wanda yake da sauran yarjejeniyar kaka ɗaya ya sanar a watan jiya cewar yana duba yiwuwar tayi daga Saudi Arabia, bisa kudin da zai samu.
Guardiola ya tattauna da ƴan jarida kafin su fara wasannin atisayen tunkarar kakar bana, wanda ya ce "Kevin ba zai bar Man City ba,".
Ranar Laraba City za ta fara wasan sada zumunta da Celtic a Chapel Hill a Arewacin Carolina a Amurka.
A kakar da ta wuce De Bruyne ya taka rawar da City ta lashe Premier League kuma na hudu a jere, shi kuma na shida da ya ɗauka a ƙungiyar.
Ana alakanta ɗan wasan tawagar Ingila da Crystal Palace, Eberechi Eze da cewar zai koma City a bana, yayin da ake cewar mai tsaron raga ɗan kasar Brazil, Ederson zai je Saudi Arabia.
To sai dai Guardiola ya ce yana fatan zai ci gaba da wasa da dukkan ƴan kwallon da suka buga wa City tamaula a bara.
''Idan wani zai bar City, za mu yi magana kan batun, amma daga nan har zuwa karshen ranar rufe kasuwar cinikin ƴan kwallo ta bana, muna sa ran za mu ci gaba da aiki tare.
''Ba zan ce ɗaukar sabbin ƴan wasa shi ne mafita ba, amma muna tsammanin kaso 85 ko 90 ko kuma 95 cikin 100, za mu ci gaba da taka leda da dukkan ƴan wasan mu.''
City za ta fara wasan Premier League a kakar 2024/24 da Chelsea ranar 18 ga watan Agusta.