Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne zai bar Manchester City a ƙarshen kakar bana
Ɗanwasan tsakiya na ƙungiyar Manchester City, Kevin de Bruyne zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.
Daga komawarsa ƙungiyar ta City daga ƙungiyar Wolfsburg ta Jamus a shekarar 2015, De Bruyne mai shekara 33 ya lashe kofuna 16.
Daga cikin kofunan da ya lashe akwai premier guda shida da zakarun turai da ya lashe a 2023 da sauransu.
Ya ci ƙwallo 106 a wasa 413 da ya buga, amma a kakar bana wasa 19 kawai aka fara da shi.
"Komai yana da farko yana da ƙarshe, amma lallai ba zan taɓa mantawa da zamana a wannan ƙungiyar ta Manchester City ba," in ji shi.
Ɗanwasan ɗan asalin ƙasar Belgium ya yi ta fama da jinyar raunuka, wanda hakan ya sa bai buga wasanni da dama ba.
Ƙwallo huɗu kawai ya zura a kakar bana, sannan ya taimaka an ci guda bakwai, wanda ke nuna tauraronsa ya fara dusashewa.