Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sanar da kuɗin aikin hajji a Najeriya
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da farashin kujerar aikin Hajjin bana.
Sabon farashin aikin Hajjin na shekarar 2026 miladiyya ya nuna cewa an samu ɗan ragi idan aka kwatanta da na 2025.
Shugaban hukumar farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda ya sanar da hakan a wata hira da BBC daga birnin Makka na Saudiyya, ya ce sanar da sabon farashin ya biyo bayan amincewar da gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi da shi.
Ya ce an tsara farashin aikin hajjin ne ta la'akari da shiyyoyin ƙasar, ta yadda kowacce shiyya aka ƙayyade kuɗin da maniyyatan ta za su biya domin sauke farali.
Farfesa Abdullahi Usman ya ce ''akwai shiyyar Maiduguri/Yola wanda ya ƙunshi Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba, waɗanda a bara (2025) sun biya kuɗi naira 8,327,125.57 kuma a yanzu za su biya 8,118,333.67 wato idan ka dubi wannan an samu ragin naira 208,791.92''
Ya ƙara da cewa ''Idan ka dawo sauran jihohi gaba ɗaya na arewacin Najeriya, a bara sun biya naira 8,457,685.59 amma a yanzu za su biya 8,244,813.67 inda aka samu ragi na naira 212,871.92''
Sauran jihohin kudancin Najeriya kuma ''bara suka biya naira 8,784,085.59 amma a bana za su biya naira 8,561,013.67, sun samu ragin naira 223,071.92.''
Shugaban hukumar aikin hajjin ya ce an samu ragi a farashin aikin hajjin ne saboda wasu abubuwa guda biyu.
''Na farko dai damu mu da yake babbar manufar mu, yaya za a yi alhajinmu ya samu sassauci, mun samu ƙarin ragi a Misha'ir, da muna biyan riyad 4,770, bara muka yi ƙoƙari aka samu ragin riyad 720 a kan kowanne alhaji. Da muka zo bana sai aka samu ƙarin ragi na riyad 150, kuma ya zamu za mu biya riyad 3,900.''
Farfesa Abdullahi Usman ya ƙara da cewa ''Abu na biyu, bara mun yi ƙiyasin dala a kan 1,600 amma bana mun yi ƙiyasin a kan naira 1,550
Zuwa yaushe za a rufe biyan kuɗin aikin hajjin bana?
Dangane da wa'adin da za a ɗauka ana biyan kudin aikin hajjin kuwa, Farfesa Abdullahi Usman ya ce akwai buƙatar dukkan masu ruwa da tsaki su wayar da al'umma muhimmancin fitowa a biya aikin hajji da wuri.
''Mun sanya ranar 31 ga watan Disamba na 2025, ita ce ranar ƙarshe da za a karɓi kuɗin duk wanda ke da niyyar zuwa aikin hajji a bana.''
Ya ce akwai banbanci tsakanin irin sanya ranar da suka saba yi a baya da kuma wannan ta yanzu, domin sai da hukumomin saudiyya suka zauna dasu kuma suka gindaya sharaɗin kammala biyan kuɗin aikin hajjin a kan lokaci.
A kwannan nan dai Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin hajji waɗanda ta tsaya kai da fata domin ganin an aiwatar da su, duk da cewa ana fargabar sababbin ka'idojin za su tilastawa maniyyatan Najeriya da dama kasa zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba.