Wace ƙungiya ce Miyetti Allah, wadda Amurka ke zargi kan ayyukan rashin tsaro a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
A cikin makon da ya gabata ne ƴan majalisar wakilan Amurka suka gabatar da wani ƙudiri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.
Ɗan Majalisa Riley Moore da takwaran aikinsa Chris Smith ne suka jagoranci gabatar da ƙudurin, inda suka ce kwamitinsu ya gano abubuwa da dama da suka nuna cewa "an daɗe ana musguna wa Kiristoci a Najeriya".
Ƴanmajalisar waɗanda na jam'iyyar Republican ne sun nemi Amurka ta sanya takunkumai kan wasu kungiyoyi, da kuma ɗaiɗaikun ƴan Najeriya saboda zargin da hannu a kisan Kiristoci.
Sauran matakan da ƙudurin ke son a ɗauka su ne hana waɗanda ake zargi da hannu a 'cin zarafin' kiristoci shiga Amurka da riƙe kadarorinsu.
Cikin waɗanda sunansu ya fito ɓaro-ɓaro a ƙudirin akwai ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da kuma abin da ƙudurin ya kira "ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai a Najeriya."
Mutane da dama na ɗaukar ƙungiyoyin biyu a matsayin abu daya, kodayake sun sha bamban ta fuskar muradunsu.
Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ƙungiya ce da ke kare muradun makiyaya, ba tare da bambancin ƙabila ko addini ba.
Yayin da ita kuma Kautal Hore ƙungiya ce da ke kare muradin ƙabilar Fulani zalla.
Wace kungiya ce Miyetti Allah Cattle Breeders (MACBAN)?

Asalin hoton, Getty Images
''Miyetti Allah'' kalmomin Fulatanci ne guda biyu da ke nufin ''Na gode wa Allah''.
An yi wa ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) rajista a matsayin ƙungiyar ƙasa, ranar 12 ga watan Fabrairun 1986, kamar yadda shugaban ƙungiyar na ƙasa Baba Usman Ngenzarma ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce kafin wannan lokaci ƙungiyar na aiki da rajista ta jihohi daban-daban galibi na arewacin ƙasar.
''Kafin nan tana aiki a matakin jihohi, alal misali Borno da Kaduna, kafin a haɗe ta ta zama ta ƙasa baki ɗaya'', in ji shi.
Kuma ƙungiyar na da shalkwatarta ta ƙasa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wace kungiya ce Miyetti Allah Kautal Hore?

Asalin hoton, Getty Images
Miyetti Allah Kautal Hore, kalmomi ne na Fulatanci da ke nufin ''Mu haɗa kai wajen gode wa Allah''.
Bayanai sun nuna cewa Miyetti Allah Kautal Hore ƙungiya ce da aka kafa domin kare muradun ƙabilar Fulani kamar yadda sauran ƙabilun Najeriya ke da ƙungiyoyin da ke kare muradunsu.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa shi ne Bello Abdullahi Bodejo, yayin da Saleh Alhassan ke matsayin sakatarenta na ƙasa.
Kamar dai MACBAN ita ma Kautal hore na da rassa a jihohin Najeriya, musamman inda Fulani ke da yawa.
Mene ne manufofin ƙungiyoyin?
Baba Usman Ngenzarma ya ce an kafa ƙungiyar MACBAN kan manufofi kamar haka:
- Kare muradun makiyaya ba tare da la'akari da ƙabila ko addini ba
- Bunƙasa harkokin kiwon dabbobi
- tabbatar da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma
- Ilimantar da makiyaya kan dabarun kiwo
- Kare haƙƙoƙin Makiyaya da suka shafi kiwo kamar wuraren kiwo, da na ban ruwa da kula da labi (hanyoyin da dabobi ke bi don zuwa wuraren kiwo)
- Warware rikice-rikicen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.
Ita kuwa Kautal Hore na da manufofi da suka sha bamban da na MACBAN kamar yadda Saleh Alhassan sakaten ƙungiyar na ƙasa ya taɓa bayyanawa cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a 2018, kamar haka:
- Kare muradun al'ummar Fulani tsantsa (makiyaya da marasa kiwo).
- Tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai
- Tabbatarwa tare da kare al'adun Fulani
- Sasanta rikice-rikice tsakanin al'ummar Fulani
- Wanzar da zaman lafiya tsakanin Fulani da sauran ƙabilu

Asalin hoton, Getty Images
Iyayen ƙungiyar MACBAN
Baba Usman Ngenzarma ya ce ƙungiyar Miyetti Allah MACBAN na da manyan sarakunan arewacin Najeriya biyar a matsayin iyayenta.
Jagoran iyayen ƙungiyar shi ne Mai alfarma sakin Musulmin Najeriya Muhammad Sa'adu Abubakar III.
Sauran iyayen ƙungiyar, kamar yadda shugaban MACBAN ya yi bayani sun haɗa da:
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
- Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman
- Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli
- Lamidon Adamawa, Alhaji Barkindo Aliyu Mustapha
Mene ne martanin ƙungiyoyin kan iƙirarin Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyar makiyayan ta ce ta yi mamakin yadda wasu ƴan majalisar Amurka suka zarge ta, ba tare da neman bahasi daga gare su ba.
"Ba mu taɓa tsammanin irin wannan zargi daga Amurka ba, dalili kuwa shi ne ƙungiyarmu ba ta masu ɗauke da makamai ba ce, kuma tana aiki ne da gwamnati da ƙungiyoyin manoma domin kawo zaman lafiya'', in ji shi.
Haka kuma ya ce a tarihihin ƙungiyar ba a taɓa zargin ta da wani laifin tallafa wa ta'addanci ko matsalar tsaro a hukumance a Najeriya ba.
Baba Usman Ngenzarma ya ce ƙungiyarsu na aiki da jami'ai da hukumomin tsaron Najeriya domin tabbatar da aiki bisa doka da oda.
Ya kuma ce sakamakon aiki da jami'an tsaro ma wajen fallasa masu laifi ya sa wasu masu laifin na kashe jagororin ƙungiyar.
''Ƙungiyarmu na cikin kwamitoci da dama na gwamnati, kuma da gwamnati ta san muna da wani laifi ba yadda za a yi ta saka mu cikin ayyukanta,'' in ji shi.
Ya ce hasali ma ƙungiyar na daga cikin waɗanda suka fi shan wahalar matsalar kashe-kashe da rashin tsaro a Najeriya.
''A jihar Kogi kaɗai an kashe mana shugabannin jihohi uku, haka ma a jihar Kwara a 2025 aka kashe mana shugaban ƙungiyar na jiha, sannan an kashe shugabanmu na jihar Katsina shekara biyu da suka gabata,'' in ji shi.
Ya bayyana wasu daga cikin fitattun shugabannin ƙungiyar da aka kashe sakamakon matsalar tsaron da ake fuskanta a ƙasar.
Baba Usman Ngenzarma ya ce ƙungiyar MACBAN na aiki da takwarorinta ƙungiyoyin al'umma a Najeriya domin warware duk wani saɓani da aka samu tsakani.
''Mun taɓa zama da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN don samun kyayyawan fahimta, a haka ma akwai lokacin da muka ziyarci ƙungiyar ci gaban al'ummar Igbo da Ohaneze don samun fahimtar juna,'' in ji shi.
Da gaske ƙungiyoyin Miyetti Allah na da alaƙa da ta'addanci a Najeriya?
Masanin tsaro a Najeriya, kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting and Intelligence Limited mai nazari kan tsaro a yankin Sahel, Kabiru Adamu ya ce ƙungiyoyin biyu ba sa cikin waɗanda ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.
''Dalili kuwa shi ne akwai dokar hana yaɗuwar ta'addaanci ta 2022 a Najeriya, dokar ce ke lura da komai da ya shafui ta'addanci, kuma a ƙarƙashin dokar akwai wasu ƙungiyoyi shida da gwamnati ta ayyana a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci, kuma a duka shidan babu wata ƙungiyar Fulani a ciki,'' in ji shi.
Haka kuma masanin tsaron ya ce a ƙarƙashin dokar akwai jerin wasu ƙungiyoyi 135 da aka ayyana da cewa sun taimaka wa ayyukan ta'addanci ta hanyar kuɗi ko wasu hanyoyin.
''To kuma duka cikin wannan jeri babu ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Miyetti Allah ko Kautal Hore a cikinsu,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya kuma ce bisa binciken da kamfaninsa yake yi sun gano cewa ƙungiyoyin - da ke neman Amurka ta ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake gallaza wa Kiristoci - sun sha zargin ƙungiyoyin Fulani da hannu a kashe-kashe Kiristoci, kodayake babu wata shaida da suka gabatar kan hakan.
''Amma sun sha cewa akwai lokutan da mambobin ƙungiyoyin suka fito suna nuna cewa da hannunsu ko suka goyi bayan kashe-kashe, ko su ce ƙungiyar ba ta taɓa fitowa ta musanta ba,'' in ji shi.
Sai dai Kabiru Adamu ya ce wannan magana ba haka take ba, ''Domin ni na san cewa akwai lokuta da dama da ƙungiyar Miyetti Allah ta sha fitowa tana ƙaryata hannu a kashe-kashen tare da neman shaidar a gabatar mata da mambanta da yake da hannu, domin ta hukunta shi''.
Daga ƙarshe Kabiru Adamu ya ce abinda ƴanmajalisar Amurka suka yi sun yi shi ne ba tare da tartibiyar hujja ba.
''Suna yi ne saboda siyasa, don su nuna cewa gwamnatin Trump na kare Kiristoci a faɗin duniya, ciki har da Najeriya'', in ji masanin tsaron.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa ake zargin ƙungiyoyin da ta'addanci?
Kabiru Adamu ya ce abin da ya sa ake zargin ƙungiyoyin Fulanin da aikata ta'addanci ba ya rasa nasa da ayyukan ƴanbindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
''Abin da ke faruwa shi ne yawanci za ka ga ƴanbindiga da ke aikata laifuka a Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Najeriya mafi yawansu Fulani ne,'' kamar yadda masanin tsaron ya bayyana.
Ya ce baya ga hakan kuma sai aka samu wani yanayi da ake yin jam'i kan masu aikata laifuka.
''An samu yanayin da ba a bambancewa tsakanin masu aikata laifuka, idan an samu wani mutum daga wata ƙabila ya aikata laifi sai kawai a yi wa ƙabilar jam'u, ba tare da la'akari da cewa kowace ƙabila akwai nagari akwai kuma ɓata-gari ba'' in ji shi.
Kuma hakan ce take yawan faruwa a yankin Arewa ta Tsakiya, inda ake samun rikici galibi tsakanin manoma da makiyaya, to idan wasu suka tashi sai su ce ƙungiyoyin Fulani ba tare da la'akari da cewa rikici ne na al'umomi wato mazauna garuruwa ba.











