Ɗanbindiga ya kashe mutane huɗu a birnin New York na Amurka

New York shooting
Lokacin karatu: Minti 2

Wani mutum ɗauke da bindiga ya kashe mutane hudu a birnin New York na Amurka, ciki harda wani ɗansandan birnin.

Maharin ya kuma yi wa wani mutum mummunan Rauni, kafin daga baya ya kashe kansa.

Maharin ya yi tattaki riƙe da bindiga a hannu daga wajen ajiye motoci zuwa cikin ginin da ya aikata ɓarnar, inda ya kutsa kai sannan ya buɗe wuta kan mutane.

Ya kuma shige har hawa na 33 na ginin, kuma a can ma ya aikata kisa.

A yayin taron manema labarai ɗazunnan, kwamishinan ƴansandan birnin New York, Jessica Tisch, ta yi bayanin yadda lamarin ya faru.

Ta ce: ''Bidiyo ya nuna wani mutum ya fita daga cikin wata baƙar mota ƙirar BMW da aka ajiye a gefen ginin, kuma yana riƙe da bindiga ƙirar M4 a hannunsa na dama, inda ya doshi ƙofar shiga ginin.

''Na'urar ɗaukar bidiyo ta nuna yadda mutumin ya shiga cikin ginin, ya kuma buɗe waw ani ɗansandan birnin New York wuta nan take. Daga nan kuma ya harbi wata mata da ta ɓoye a jikin turken ginin, sannan ya kutsa kai ciki, ya kuma buɗe wuta.'' In ji Jessica Tisch.

Ƴansanda sun ce sunan maharin Shane Tamura, kuma matashi ne mai shekara 27 ɗan asalin Las Vegas.

Hukumomi sun ce kawo yanzu babu masaniya kan dalilinsa na aikata wannan ɓarna, amma ana ci gaba da bincike.

Abin da hukumomi suka gano kawo yanzu

A wajen wani taron manema labarai a birnin New York City, magajin garin birnin, Eric Adams ya bayyana abubuwan da suka gano kawo yanzu kamar haka:

Maharin ya kashe mutane hudu.

Hukumomi a birnin New York sun ce sunan maharin Shane Tamura, kuma matashi ne mai shekara 27 da ya fito daga Zevada kuma ya kashe kansa bayan ya kashe mutanen huɗu.

As soon as

Tamura ya buɗe wuta kan mutane inda ya kashe harda ɗansandan birnin New York ɗaya.

Tamura na da lasisin mallakar makami, kuma yana da tarihin fama da matsalar ƙwaƙwalwa, amma kawo yanzu babu tabbacin dalilinsa na aikaa wannan ɓarna.

Ɗansandan da aka kashe

DIDARUL ISLAM

Rundunar ƴansandan birnin New York ta fitar da bayanin ɗansandanta da maharin ya kashe, inda ta ce sunansa Didarul Islam.

Marigayin yana da mata da ƴaƴa biyu, kuma matar tana ɗauke da cikin na uku a yanzu haka.

Rundunar ƴansandan ta ce yana daga cikin jami'anta da suka yi fice wajen tsare aiki da jajircewa.