Barcelona ba ta da sha'awar ci gaba da riƙe Lewandowski, Arsenal na son Agoume

Asalin hoton, Getty Images
Golan Ingila Jordan Pickford, mai shekara 31 na shirin tsawaita zamansa a Everton ta hanyar sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci da Toffees. (Times)
Barcelona ba za ta sabunta kwantiragin dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37 ba, idan kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa. (Sports)
A shirye kungiyar ta Barcelona take ta tabbatar da dan wasan gabanta Marcus Rashford mai shekaru 27 da ke zaman aro daga Manchester United a matsayin na dindindin sakamakon yadda ya taka rawar gani a farkon kakar wasa. (Sun)
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane na shirin komawa aiki kuma yana son ya jagoranci wata tawaga a Faransa. (Mirror)
Newcastle United za ta yi tunanin barin dan wasan Danish William Osula, mai shekara 22, ya tafi aro a watan Janairu idan ya zamana tashinsa ba zai haifar mata da wata matsala ba. (Mirror)
Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan tsakiyar Sevilla Lucien Agoume, mai shekara 23, a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Fichajes)
Chelsea na sha'awar sayen dan wasan bayan Barcelona Ronald Araujo, mai shekara 26, amma da wuya ta yi zawarcinsa a cikin watan Janairu. (Footbal Insider)
Tottenham Hotspur, da Liverpool da Aston Villa na daga cikin kungiyoyin gasar Premier da suka aike da wakilai don kallon dan wasan bayan FC Nantes Tylel Tati, mai shekara 17. (CaughtOffside)










