Yadda aka gudanar da bikin Kirsimeti a faɗin duniya

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani matashi sanye da kayan Santa Claus a birnin Belgrod da ke Rasha.
Lokacin karatu: Minti 2

A ranar 25 ga watan Disamba mabiya addinin Kirista sun gudanar da bukukuwa albarkacin wannan rana ta hanyoyi daban-daban.

Yayin da wasu suka yi tururwa zuwa majami'u, wasu sun je wuraren hutu inda wasu kuma ke zuwa manyan shagunan alfarma domin siyayya sannan wasu na ta faman ziyara domin sada zumunci ga ƴan uwa da abokan ariziƙi.

BBC ta yi duba dangane da ƙasashe da wurare daban-daban a faɗin duniya kan yadda suka gudanar da bukukuwan na Kirsimeti.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jerin gwanon wasu mabiya addinin Kirista a cocin asali ta Nativity da ke Bethlehem, garin da aka haifi Yesu Almasihu, suna ibadoji a ranar Kirisimeti.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Leo XIV lokacin da dandazon mabiya ke yi masa maraba zuwa dandalin cocin ST. Peter's.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mabiya addinin Kirista ke zagaye a kan tituan birnin Karachi da ke ƙasar Pakista a jajiberin Kirsimeti
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda sojojin Amurka sanye da kayan sarki suka yi bikin Kirsimeti a sansanin sojin Amurka da ke Saudiyya
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shi ma Shugaban Amurka, Donald Trump ba a bar shi a baya ba dangane da wannan rana ta Kirsimeti.
..

Asalin hoton, IWM/Getty Images

Bayanan hoto, Sarkin Ingila, Charles III da Sarauniya Camilla sun halarci taron addu'o'in safe na ranar Kirsimeti a cocin St Mary Magdalene.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka ƙawata wani titi a birnin Abuja domin bikin na Kirsimeti.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu Indiyawa mabiya addinin Kirista ke addu'o'in ranar Kirsimeti a coci inda suke roƙon ubagiji tare da zubar da hawaye.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka ƙawata dandalin Festilumi Light Park da ke birnin Wan Chai na ƙasar Hong Kong.
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zuwa dandalin wasanni a Belgrod da ke Rasha domin bukukuwan Kirsimeti.