Yadda aka gudanar da bikin Kirsimeti a faɗin duniya

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar 25 ga watan Disamba mabiya addinin Kirista sun gudanar da bukukuwa albarkacin wannan rana ta hanyoyi daban-daban.

Yayin da wasu suka yi tururwa zuwa majami'u, wasu sun je wuraren hutu inda wasu kuma ke zuwa manyan shagunan alfarma domin siyayya sannan wasu na ta faman ziyara domin sada zumunci ga ƴan uwa da abokan ariziƙi.

BBC ta yi duba dangane da ƙasashe da wurare daban-daban a faɗin duniya kan yadda suka gudanar da bukukuwan na Kirsimeti.