Cutukan da za ku iya ganewa ta girma ko sirantar wuyanku

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Chandan Kumar Jajwade
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi
- Marubuci, Sarah Bell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health Team, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Mu kam gane lokacin da muka ƙara ƙiba ne idan muka cikinmu ya zama ƙato ko kuma idan kayan sawarmu suka matse mu.
To amma wani wuri a jikinmu da ke nuna mana mun yi ƙiba ko mun rame wanda ba ma mayar da hankali da yadda yake nuna irin lafiyar jikinmu shi ne wuya.
Idan ya yi ƙiba ko ya rame fiye da ƙima, to hakan ka iya yiwuwa wata alama ce ta wata cutar a jikinmu.
Yaya wuyan mutum ya kamata ya kasance?
Yadda ake gane yawan ƙibar da jikin ɗan'adam da ita shi ne ta hanyar haɗa nauyin mutum da tsawonsa da ake kira da.
Sai dai kuma duk da cewa wannan wani abu ne da ke fayyace lafiyar mutum to amma al'amarin ba haka yake ba ga mutane irin su masu motsa jikin domin samun ƙwanji kasancewar ƙwanjin nasu yana ƙara musu nauyi.
Hakan ne ya sa auna yanayin girma ko ƙanƙantar wuyan mutum ka iya fito da irin lafiyar da mutum din ke da ita.
Idan kana da zaren awo da ake kira tef a hannunka za ka iya aunawa da shi.
"Kamata ya yi a ce wuyan mata ya kasance tsakanin sentimita 33 zuwa 35, inda kuma na maza ya kamata kasance tsakanin 37 zuwa 40," in ji Dr Shiv Kumar Sarin, shugaban kwalejin nazarin kimiyyar magunguna ta ƙasar India.
Wane amfani kaurin wuya yake da shi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu mutanen suna matosa jiki na ɗaga nauyi domin su mayar da wuyansu babba - kamar masu motsa jiki da ƴan dambe da masu wasa rugby duk suna kurin samun ƙaton wuya. To amma idan aka cire batun motsa jikin, hakan ba wani abun burgewa ne ba.
"Idan wutanka yana da ƙiba fiye da ƙima, hakan na nuna cewa mutumin da matsalar lafiya wato kana zama mai teɓa," in ji Amitav Banerjee, farfesa a Kwalejin likitanci ta DY Medical College, da ke Pune. "Da dama cutukan na da alaƙa da matsananciyar ƙiba."
Ƙiba a wuyan mutane na da bambanci da kitsen da ke ciki ko ƙarƙashin fatar ɗan'adam - man da ke kwance a ƙarƙashin fata a wasu sassan jiki kamar kwankwaso.
Idan kana da ƙibar da ta wuce ƙiba, jikinka na ɗauke da kitse da ke ɓoye a cikinka wanda ake kira da "visceral fat". Shi irin wannan kitsen ba wai ba shi da tasiri ba ne a jikinka a'a yana aiki a tsarin yadda jikinka ke gudana, ta hanyar shafar sukarin jikin ɗan'adam da kitsen da ke jijiyoyin jini da kuma hawa da saukar jini.
"Shi wuya yana wurin da da zarar an gan shi za a gane irin yawan kitsen da ke jikinku," in ji Dr Ahmed Elbediwy, malamin da ke koyar da nazarin sinadarai da rayuwarsu wato Biochemistry, a matakin digiri, a jami'ar Kingston da ke London.
"Iya teɓarka, iya girman wuyanka."
Mene ne illar teɓar wuya?
Idan mutum yana da babban wuya wanda ya wuce ƙima, hakan na nuni da rashin lafiyar gudanarwar da jikinsa ke yi - wani rukunin matsalolin lafiya da ke jefa mutane fuskantar cutar suga aji na 2 da ka iya shafar zuciya ko jijiyoyin jini.
Saboda idan kana da kitsen da ya wuce ƙima a jikinka, to hakan na nufin kana da kitsen fiye da ƙima a cikin fatarka da ka iya narkewa zuwa cikin jini, da gaggawa.
"Mutumin da ke da ƙaton wuya ka iya samun yawaitar kitsen da ke toshe jijiyoyin jini da hanta mai kitse da cutar suga da hawan jini. Wannan na buƙatar bincike na musamman," in ji Dr Mohsin Wali, ƙwararren likita, a asibitin Sir Ganga Ram Hospital da ke Delhi.
Abin ka iya haddasa ɗaukewar numfashi a yayin bacci, wanda kan shafi hutawar da ƙwaƙwalwar mutum ke yi.
Me sirantar wuya ke nufi?
"Bai kamata masu siririn wuya su samu fargaba ba," in ji Dr Ahmed Elbediwy. "Cin abinci mai gina jiki da yawaitar motsa jiki na taimakon rayuwar ɗan'adam har ma da yadda zai ku rage ƙiba."
Motsa jikin da ke taimakawa zuciya da na rage teɓa ka iya taimakawa wajen rage teɓar da ke sama jikin mutum, inda shi kuma samun isasshen barci ke daidaita tsarin gudanarwar jiki da kuma tayar da komaɗa. Abinci lafiyayye mai gina jiki da ke ƙara jini mai ɗauke da harza da ganye na samar da sinadaran gina jiki ba tare da samar da sinadaran da ke sa teɓa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Me ramammen wuya ke nufi?
Ramammen wuya na da alaƙa da kyawu kamar yadda aka daɗe ana faɗi. Mutane kan saka kayan ƙawa domin jan hankalin mai kallo.
A wasu ƙasashen Afirka, mata kan saka wani nau'in warwaro a wuyansu ta yadda wuyan zai zama siriri kuma dogo.
A daidai lokacin da ake bayyana siririn wuya da alamun kyawu, idan wuya ya zama siriri fiye da ƙima hakan ka iya zama alamun kansar jini da ake kira "anaemia" in ji likitoci.
"Ana bai wa irin waɗannan mutanen sinadaran da ke ƙara kuzari kamar kalmatako da bitamin da sauransu. A wasu lokutan ma al'amarin ka iya kai wa ga sauya jinin jikin mutum," in ji Atreya Niharachandra, likita da ke zaune a Bengaluru.

Asalin hoton, Getty Images
Bugu da ƙari, mutanen da ke da ramammen wuya ka iya zama alamar mallakar ƙarin ƙashin gadon bayansu. Akwai kasusuwa bakwai a ƙashin bayan ɗan'adam sai dai kuma akwai mutanen da ke da takwas kwatankwacin mutanen da ke da yatsu shida maimakon guda biyar.
Wani yanayin da ake fahaimta daga tsananin sirantar wuya shi ne kumburun hakin wuya da ake kira da "Goitre".
Shi hakin wuya na can ƙasan gaban wuyan mutum da ka iya kasancewa sumul ko mai gargada ko kuma ma wani lokaci ya kumbure a ɓangare ɗaya.
Yawanci ba sa ciwo ko kuma yin illa amma kuma hukumar insorar lafiyar Burtaniya, ta ba da shawarar cewa ya kamata likitoci su duba su gani.
Saboda haka nan gaba idan ka dubi muadubi ka kula da kyau da wuyanka - zai iya fahimtar da kai wasu abubuwan da ba ka tunani ba.











