Bajinta ko rashin kwazon da za a yi a Gasar Kofin Duniya a Qatar

Qatar World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Qatar za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Duniya a 2022 da za a fara tsakanin Nuwamba zuwa Disamba, karo na 22 da Fifa za ta gudanar.

Akwai tarihin bajinta da rashin kwazo da yawa da aka kafa a baya tsakanin tawagogi da 'yan wasa da dukkan abin da ya shafi babbar Gasar Kwallon kafa ta duniya.

Katin gargadi 123 da jan kati 11

Argentina ce kan gaba a yawan karbar katin gargadi wato mai ruwan dorawa 123 da kuma brazil mai jan kari 11 tun bayan da aka kirkiro bayar da kati a gasar.

Uruguay tana da jan kati tara a tarihi, wadda itama tana cikin wadanda za su buga wasannin Qatar.

Tawaga biyu ta buga wasa 109 kowacce a Gasar Cin Kofin Duniya

Brazil da Jamus kowacce ta buga wasa 109 a Gasar Cin Kofin Duniya da Fifa ke gudanarwa, kowacce na fatan taka rawar gani a Qatar.

Argentina ce ta uku mai wasa 84 idan ta kara da Poland a rukuni na uku a Qatar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan ta cinye dukkan wasa uku a cikin rukuni za ta yi nasara 46 keann ta zama ta uku bayan Brazil da ci fafatawa 73 da Jamus mai nasara 67.

Tawagar Ingila za ta buga wasa na 70 a karawa da Iran

Ingila za ta buga karawa ta 70 a Gasar Cin Kofin Duniya, idan ta fafata da Iran, za ta koma ta biyar a jerin wadanda suka buga gasar da yawa a tarihi.

Netherlands za ta sha gaban Sweden a yawan yin wasannin Kofin Duniya idan ta fafata da Ecuador wasa na 51 a gasar, za ta fada cikin goman farko.

Mexico ta yi rashin nasarar wasa 27 a Kofin Duniya

Mexico ta yi rashin nasara karo 27 a fafatawa 57, ita ce kan gaba a jerin wadanda suka buga Gasar da yawa amma ba ta lashe Kofin ba.

Saura kwallo daya a zura mata 100 a raga ta uku da kwallaye da dama suka shiga ragarta bayan Jamus mai 125 da kuma Brazil mai 105.

'Yan wasa 11 sun yi karawa 20 ko fiye da haka a Kofin Duniya

'Yan wasa 11 ne suka buga karawa 20 ko fiye da hakan a Gasar Kofin Duniya, saura daya Messi ya cika wasa na 20.

Shi kuwa Ronaldo zai shiga wadannan sawun idan ya kammala karawa uku a cikin rukuni a Qatar.

Messi zai yi kan-kan-kan da Maradona a buga wasa 21 a Kofin Duniya

Saura wasa biyu ya rage Messi ya yi kan-kan-kan da Diego Maradona a buga fafatawa 21 a Gasar Kofin Duniya.

Idan Argentina da Messi suka kai wasan karshe a Qatar, sannan ya buga dukkan wasa bakwai, zai yi kan-kan-kan da Lothar Matthaus mai tarihin wasa 25 a Gaadr.

Kociyoyi takwas ne ba daga kasashensu ba za su horar a Qatar

Takwas daga kocin da za su ja ragamar tawagogi a Qatar ba 'yan kasar bane.

Sauran Gasa 21 da aka yi a baya masu horarwa daga kasar ne kan lashe Kofin Duniya a tarihi.

Ronaldo ya ci kwallo a kowacce Gasa hudu baya da ya buga Kofin Duniya

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo a kowacce Gasa hudu da ya buga a Kofin Duniya, bajintar da Pele da Uwe Seeler da kuma Miroslav Klose suka yi a baya.

Idan ya ci kwallo a Qatar zai kafa tarihin na farko da ya zura kwallo a raga a Gasar Kofin Duniya biyar a tarihi.

A Gasa uku baya an yi waje da mai rike da kofin duniya bayan wasannin rukuni, inda Italiya ta fice a 2010 a Afirka ta Kudu, sai Sifaniya a Brazil 2014 da a 2018 da Jamus ta yi ban kwana da wasannin da ak yi a Rasha.