'Dole ne a sa Ukraine a duk tattaunawar zaman lafiya'

Shugaba Macron na Faransa da Zelensky na Ukraine da kuma Kier Starmer na Birtaniya

Asalin hoton, EPA

Lokacin karatu: Minti 3

Kawayen Ukraine na Turai sun bukaci a kara matsa wa Rasha lamba kafin taron koli da za a yi ranar Juma'a tsakanin Donald Trump na Amurka da kuma takwaransa na Rashar Vladimir Putin kan yakin na Ukraine din.

A wata sanarwar hadin gwiwa da Tarayyar Turai da Birtaniya da sauran kasashe abokan burmi suka fitar sun jaddada goyon bayansu ga cikakken 'yancin Ukraine.

Kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da tallafa wa Ukraine ta kowace fuska a yakinta da Rasha.

Wadanna kawaye na Ukraine a Turai sun fitar da sanarwar ta hadin gwiwa ne wadda a ciki suke jaddada goyon bayansu ga Ukraine na tabbatar da 'yancinta a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Sun jaddada cewa za su ci gaba da ba ta duk wani goyon baya ta fuskar kudi ne da kayan soji a yakin da take yi da Rasha.

Yayin da za a yi ganawar koli tsakanin Shugaba Trump da kuma takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Alaska ta Amurka a ranar Juma'a kan batun yakin na Ukraine , shugabannin kasashen aminan Ukraine – da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya da Poland da Finland da kuma shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen sun ce dole ne a shigar da Ukraine duk wata tattaunawa da za a yi a kanta ta zaman lafiya.

Shun kara da cewa Ukraine tana da 'yancin zabi a kan makomarta – da cewa ba ta yarda za a sauya iyakar kasashe da karfin tsiya – wato dangane da batun matsayar Rasha ta Ukraine din ta sallama mata yankunan da ta kwace a sakamakon mamaye ko kutsen da ta y iwa Ukraine din.

Ita dai Rasha ta kafe a kan lalle sai Ukraine din ta hakura da yankunan, sannan ta kwance damarar yaki ta kuma yi watsi da burinta na shiga kungiyar tsaro ta Nato – wanda wadannan su ne za su kai ga Rasha ta dakata da yakin da take yi da Ukraine din.

Haka shi ma jagoran shirya taron kolin na Alaska, Shugaba Trump – ya kunshi wannan aniya ta Rasha ta ganin Ukraine ta sallama wasu yankunan nata ga Rasha domin zaman lafiya.

Sai dai a n martaninsa a sakon da ya sanya a shafin sada zumunta da muhawara Shugaba Zelensky duk da cewa ya yi taka tsantsan, bai soki Trump a kan wannan batu na hakura da wasu yankunan kasar tasa ba - ya nuna cewa ba za ta sabu ba.

Kuma ya jaddada batun cewa wajibi ne Ukraine ta kasance a duk wata tattaunawar zaman lafiya.

A bangare daya kuma mataimakin shugaban Amurka JD Vance tare da Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy sun gudanar da taron Jami'an tsaro a kusa da London inda suka tattauna kan yakin Ukraine.

Bayanai sun nuna cewa Amurka ce ta shirya taron – wanda ya samu halarcin jami'ai da masu bayar da shawara na kasashen Turai.