Ƙarfe nawa ne yanzu a duniyar wata?

...

Asalin hoton, Getty Images

Babu wanda zai iya cewa yanzu ƙarfe nawa ne a duniyar wata.

Amma kamar yadda ake iya tantance lokaci a duniya, haka ma ana iya tantance lokaci a sararin samaniya.

Sai dai a daidai lokacin da ƙasashe da dama ke shirin aika mutane zuwa duniyar wata da yin aiki a can, an tafka muhawara kan ko za a sanya lokacin agogo a hukumance a duniyar wata.

Hukumar kula da sararin samaniyar Turai ta ce samun lokacin agogo a hukumance a duniyar wata zai kasance abu mai amfani ga ƙungiyoyin binciken sararin samaniya daban-daban a duniya.

Ƙungiyar ta ce ya zama dole a yi taswirar duniyar wata a kan lokaci, domin tantance wuraren da wata ke da shi ta yadda zai riƙa tafiya daga wannan yanki zuwa wancan.

Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai tana aiki tare da NASA ta wannan hanyar.

A halin yanzu, ana amfani da lokacin Universal Time (UTC) a duk ayyuka saboda duniyar wata ba ta da yankin lokacinta.

Sai dai Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai ta ce ba za a iya dogaro da UTC ba har tsawon lokaci yayin da yunƙurin tafiya duniyar wata ke ƙaruwa a kowa ce rana.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanya lokaci na da matuƙar mahimmanci don jiragen sama su yi aiki yadda ya kamata.

Jami’an kula da sararin samaniyar Turai sun ce ya kamata hukumar kula da sararin samaniya ta ɗauki nauyin tsara lokaci a duniyar wata.

Dole ne a yanke shawara kan ko wasu ƙasashe za su ɗauki ƙa'idar lokaci na duniyar wata ko kuma duniyarmu.

Idan aka kwatanta da sa'o'i 24 na duniyarmu, agogon duniyar wata yana da ƙarin daƙiƙa 56.

Domin kuwa ƙarfin girabiti a kan duniyar wata yana da rauni.

Wannan na iya zama dalilin da ya sa 'yan sama-jannati a duniyar wata suke shirya ayyukan da za su yi kafin lokaci saboda lokacin duniyar wata ba ɗaya ba ne da lokacin duniyarmu.

Lokuta sun kasu daban-daban a duniya dangane da yanki daga maƙurar duniya ta kudu da ta arewa

Lokacin Greenwich Standard Time (GMT) shi ne lokacin da aka ƙayyade wanda aka raba rana a duniya zuwa sa'o'i 24.

Ƙasashen da ke gabas din layin Greenwich ne ke gaban Birtaniyya kuma ƙasashen yammacin duniya na bayan Birtaniya.

Lokuta a Indiya na da banbancin sa'o'i biyar da rabi da na GMT.

Masanin kimiyya na Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai, Bernhard Hufenbach ya bayyana cewa kayyade lokacin da aka tsara a duniyar wata zai yi amfani ga ‘yan sama jannatin da ke aiki a saman duniyar wata wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta a duniyar.

Kwana daya a duniyar wata ta yi daidai da kwanaki 28 a Duniyarmu.

Baya ga haka, muna iya sanin makonni biyu na sanyin dare a duniyar wata.

Amma akwai kuma tambayoyi da dama game da lokaci a duniyar wata da suka kunshi ko a haɗe Lokacin duniyar wata da na Duniyar mu? Ko a bar lokacin duniyar wata ya yi zaman kansa? Dole ne a yanke shawara kafin komai.

NASA na shirin kaddamar da aikinta na farko zuwa duniyar wata cikin shekaru 50 a shekarar 2025.

Amurka kuma za ta tura mace zuwa duniyar wata a karon farko a aikin Artemis.