Najeriya na neman shafin kirifto na Binance ya biya ta diyyar dala biliyan 81.5

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta sake maka shafin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance a kotu, inda take buƙatar ya biya ta diyyar kuɗi dalar Amurka biliyan 81.5.
Najeriya na zargin kamfanin da cutar da tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar kauce wa biyan haraji.
Shari'ar, wadda Hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta cikin gida ta Najeriyar ta shigar ranar Talata, a wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja, na neman kamfanin ya biya dala biliyan 79.5 ne kan asarar da ƙasar ta tafka sanadiyyar ayyukan kamfanin Binance a Najeriyar.
Sai kuma dala biliyan biyu na bashin haraji da ake bin kamfanin.
Hukumomin Najeriya na ɗora laifin zubewar darajar kuɗin ƙasar a kan kamfanin na Binance, lamarin da ya sanya aka tsare manyan jami'an kamfanin biyu, bayan matakan da ƙasar ta ɗauka kan ayyukan masu hada-hadar kuɗin kirifto a ƙasar cikin shekara ta 2024.
Kamfanin Binance, wanda ba ya da rajista a ƙasar ta Najeriya, bai mayar da martani a hukumance kan ƙarar ba, sai dai a baya, ya bayyana cewa yana aiki tare da hukumar tattara kuɗaɗen harajin ta Najeriya (FIRS) domin warware saɓanin da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
Dama dai Binance na fuskantar tuhuma kan kauce wa biyan Najeriya wasu haraje-haraje, ciki har da rashin biyan harajin cinikayya na VAT, da harajin kuɗaɗen shiga na kamfanoni da kuma tuhuma kan taimaka wa wasu wajen kauce wa biyan kuɗin haraji ta hanyar hada-hada a shafinsa.
Sai dai kamfanin ya musanta zargin.
A watan Maris ɗin 2024, Binance ya dakatar da hada-hada da kuɗin naira a shafinsa, kuma kamfanin na ci gaba da kare kansa game da ƙarar da hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasar ta shigar a kansa.
Mene ne shafin hada-hadar kirifto na Binance?
Binance shi ne babban shafin hada-hadar kudin kirifto a duniya da ake amfani da shi ta hanyar saye da sayarwa na wasu kadarorin intanet.
An yi kiyasin cewa akwai mutum miliyan 150 da ke amfani da Binance. Da farko kamfanin na da shalkwata a kasar China kafin daga baya ta koma Malta, duk da cewa an yi mata rajistar biyan haraji a tsibirin Cayman.
Ta yaya ake amfani da kudin kirifto?
A takaice a iya cewa kudin kirifto kudade ne na intanet. Ba a saka su a aljihu kamar sauran takardun kudi ko sulalla, su kudi ne da hannu ba ya iya taba su.
To sai dai duk da cewa ba ma iya ganinsu ko taba su, kudaden na da daraja.
Ana taskance kudaden kirifto a wani asusun ajiya na intanet da ake kira 'Wallet' da ake samu a wayar hannu ko kwamfuta, inda mai shi zai iya aika wa mutanen da ya sayi wani abu daga gare su. Haka kuma ana iya yin hada-hadar musayar kudi da su kamar yadda Binance ke yi.











