Matar baturen Binance ta buƙaci Najeriya ta sakar mata miji

Asalin hoton, Yuki Gambaryan
- Marubuci, Nkechi Ogbonna
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
"Wannan lamari bai kamata ba. Babu wani laifi da ya yi," Kamar yadda Yuki Gambarayan wadda ke zaune a Amurka ta shaida wa BBC.
Yuki ita ce mai ɗakin baturen kamfanin hada-hadar kuɗin intanet na Binace da aka kama a Najeriya, wato Tigran Gambaryan, wanda yanzu haka ake zargi da laifin halasta kuɗin haram.
Mista Gambaryan babban jami'i ne a kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto mafi girma a duniya.
Binance, kamfanin da aka yi wa rajista a tsibirin Cayman na fuskantar tuhume-tuhume a Najeriya, inda Hukumar tattara kuɗin haraji ta cikin gida ta shigar da kamfanin ƙara kan tuhume-tuhume guda biyar, waɗanda suka shafi kauce wa biyan haraji.

Asalin hoton, Reuters
Haka nan kuma Hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta Najeriya (EFCC) ta zargi Binance da manyan jami'an nasa biyu, Mista Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da laifin halasta kuɗin haram na dalar Amurka miliyan 35.4.
A cikin watan da ya gabata, Mista Gambaryan ya musanta tuhumar da ake yi masa sai dai har yanzu yana tsare a Najeriyar.
Shi kuwa ɗan'uwan aikinsa kuwa, Mista Anjarwalla, hukumar ƴansanda ta Najeriya na neman sa ruwa-a-jallo bayan da ya tsere daga ƙasar a cikin watan Maris.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A can Amurka kuwa, a ranar Talata wata kotu ta yanke wa mutumin da ya samar da kamfanin na Binance, Changpeng Zhao hukuncin ɗaurin wata huɗu a gidan yari bayan kama shi da laifin barin masu aikata laifi suna almundahanar kuɗi ta shafinsa.
A watan Nuwamba Mista Zhao ya sauka daga muƙaminsa a kamfanin sannan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na saɓa wa dokar hada-hadar kuɗi ta Amurka.
An kuma umarci Binance ya biyar tarar dala biliyan 4.3 bayan da aka gano cewa shafin ya taimaka wa wasu mutane tsallake hukunci.
Masu gabatar da ƙara sun so ne a ɗaure tsohon shugaban kamfanin na Binace tsawon shekara uku.
A cikin watan Nuwamba mahukunta a Amurka sun bayyana cewa matakin da shafin Binance da mamallakinsa Zhao suka ɗauka na "karya dokoki da gangan" ya yi barazana ga harkar kuɗi na Amurka.
Mamallakin shafin wanda ake yi wa laƙabi da CZ, yana da dukiyar da ta kai darajar kuɗi dalar Amurka biliyan 33, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
Matar Gambaryan ta ce "Idan Najeriya na bin Binance bashin wasu haraje-haraje ko wasu ƙ'idoji da bai cika ba a ƙarƙashin dokokin Najetiya, to ya kamata kamfanin ya gyara inda ya yi kuskure. Amma maigidan nata shi karan kansa bai da wata tuhuma da za amsa."
Ta ce ba ya da laifi kuma bai kamata a ɗauke shi a matsayin wakilin kamfanin ba.
Kamfanin Binance ya bayyana tuhume-tuhumen da ake yi wa Gambaryan a matsayin "marasa tushe" tare da kira kan cewa a sake shi.
"Ba mu ji daɗi ba yadda ake ci gaba da tsare Tigran Gambaryan duk kuwa da cewa ba shi da ƙarfin faɗa a ji a kamfanin." in ji mai magana da yawun Binance lokacin da ya yi magana da BBC.
Ana tsare ne da Gambaryan, tsohon jami'in tsaro a Amurka mai shekara 39 a duniya a gidan yari na Kuje da ke babban birnin Najeriya kafin lokacin da za a tantance buƙatar bayar da belin sa.
Mai ɗakin Gambaryan ta ce "Ina cikin tashin hankali kan ci gaba da tsare shi a cikin mummunan hali, kawai domin ya amsa gayyatar ganawa da jami'an gwamnatin Najeriya."
Mai magana da yawun Binance ya ce kamfanin na buƙatar a saki jami'in nasa yayin da suke ci gaba da tattaunawa da hukumomin Najeriya.
A watan Fabarairu ne Gambaryan da abokin aikinsa Anjarwalla suka isa Najeriya domin yin wata ganawa kan ayyukan shafin a ƙasar, a maimakon haka sai hukumomi suka tsare mutanen biyu a wani wuri da ba a bayyana ba har zuwa lokacin da Mista Anjarwalla ya tsere.

Asalin hoton, Yuki Gambaryan
Matar da Gambaryan ta ce ta shiga wani mawuyacin hali tun bayan tsare maigidan nata.
"Na gaji baki ɗaya, domin bana ganin wani ci gaba.
A cikin watan Mayu ne wata babbar kotu da ke Abuja za ta fara sauraron ƙarar tasa.
Lokacin da BBC ta tuntuɓi ofishin jakadancin Amurka a Najeriya kan shari'ar ta Gambaryan, sai ofishin ya ce suna "samar da duk wani taimako" ga duk wani ɗan ba'amurke da ake tsare da shi a ƙasar waje.






