Mazaɓu 14 da ba su da wakilci a majalisun dokokin Najeriya

Yayin da wasu daga cikin ƴan majalisar suka bar giɓi a gundumominsu sanadiyyar rasuwa, wasu sun ajiye aiki ne domin karɓar wasu muƙaman na daban

Asalin hoton, facebook/Multiple

Bayanan hoto, Yayin da wasu daga cikin ƴan majalisar suka bar giɓi a gundumominsu sanadiyyar rasuwa, wasu sun ajiye aiki ne domin karɓar wasu muƙaman na daban
Lokacin karatu: Minti 5

Mace-macen da aka samu a baya sun bar giɓi a majalisar dokokin Najeriya, daga majalisar dattijai zuwa ta wakilai da kuma majalisun dokokin jihohi.

Sai dai baya ga mutuwa, wani abin da ya ƙara haifar da giɓin wakilci a mazaɓun Najeriya shi ne karɓar wasu muƙaman na daban da wasu wakilan suka yi.

Sai dai irin wannan giɓi na wakilci a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya ya fara tayar da ƙura da muhawara a faɗin ƙasar.

Ko a ranar Talata, majalisar dokokin Najeriya ta buƙaci hukumar zaɓen Najeriya ta Inec ta gurfana a gabanta domin yin bayani kan dalilan da suka sanya har yanzu ba a yi zaɓukan cike gurbi a irin waɗannan mazaɓu ba.

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya na da jimillar wakilai 469 ne, inda majalisar dattijai ke da sanatoci 109 sai kuma majalisar wakilai mai ƴan majalisa 360.

To sai dai a yanzu majalisar dattijai na tafiya ne da sanatoci 107 bayan rasuwar sanata ɗaya, yayin da sanata ɗaya kuma ya lashe zaɓen gwamna.

Ita kuma majalisar wakilai na tafiya ne da wakilai 355, bayan rasuwar ƴan majalisa huɗu, yayin da ɗan majalisa ɗaya ya ci zaɓen mataimakin gwamna.

BBC ta duba mazaɓun da a yanzu ba su da wakilci a majalisar dokokin, kamar haka:

Anambra ta Kudu (Anambra) -Sanata Ifeanyi Ubah (Mutuwa)

Patrick Ifeanyi Ubah

Asalin hoton, Facebook/Senator Dr. Patrick Ifeanyi Ubah

Bayanan hoto, Patrick Ifeanyi Ubah

Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya kasance ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ya rasu ne a ranar 27 ga watan Yulin 2024 a birnin Landan.

Kafin rasuwarsa ya kasance ɗan majalisa dattijai mai wakiltar mazaɓar Anambra ta Kudu.

Edo ta tsakiya (Edo) - Sanata Monday Okpebholo (Ajiye aiki)

Monday Okpebholo

Asalin hoton, facebook/Monday Okpebholo

Bayanan hoto, Monday Okpebholo

Monday Okpebholo ya bar muƙaminsa na sanata ne bayan ya lashe zaɓen gwamna a jihar Edo a watan Nuwamban 2024.

Ya wakilci mazaɓar Edo ta tsakiya a majalisar dattijai ne daga shekarar 2023 zuwa 2024 lokacin da ya zama gwamna.

Ikenne/Sagamu/Remo North (Ogun) - Adewumi Oriyomi Onanuga (Mutuwa)

Adewumi Oriyomi Onanuga

Asalin hoton, facebook/Adewunmi Oriyomi Onanuga

Bayanan hoto, Adewumi Oriyomi Onanuga

A watan Janairun 2025 ne Adewunmi Oriyomi Onanuga ta rasu, kamar yadda majalisar wakilan Najeriya ta sanar.

An zaɓe ta zuwa majalisar dokoki ne karon farko a shekara ta 2019. Ta kasance shugabar kwamaitin majalisa kan harkokin mata a majalisar wakilan ta Najeriya.

Ovia ta arewa maso gabas da kudu maso yamma (Edo) Dennis Idahosa (Ajiye aiki)

Dennis Idahosa

Asalin hoton, facebook/Dennis Idahosa

Bayanan hoto, Dennis Idahosa

Dennis Idahosa ya bar majalisar wakilan tarayyar Najeriya ne bayan zaɓen da aka masa a matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo a shekarar 2024.

Kafin lokacin, ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar Ovia ta arewa mao gabas da kuma Ovia ta kudu maso yamma a majalisar wakilai, daga shekarar 2019 zuwa 2024.

Garki/Babura (Jigawa) - Isa Dogonyaro (Mutuwa)

Isa Dogonyaro

Asalin hoton, facebook/Isa Dogonyaro

Bayanan hoto, Isa Dogonyaro

Ɗan majalisa mai wakiltar Garki da Babura a majalisar wakilan tarayya, Isa Dongonyaro sanadiyyar rashin lafiya.

Ya lashe zaɓe ne a 2023, bayan kotu ta soke nasarar da Aminu Kanta ya yi a zaɓen fitar da gwani.

Chikun/Kajuru (Kaduna) - Ekene Adams (Mutuwa)

Ekene Adams

Asalin hoton, facebook/Ekene Adams

Bayanan hoto, Ekene Adams

Ekene Adams ya rasu ne a watan Yulin 2024 bayan fama da rashin lafiya. Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban kwamitin majalisar dokoki kan wasanni.

Ibadan ta Arewa (Oyo) Musiliudenn Akinremi (Mutuwa)

Musiliudenn Akinremi

Asalin hoton, facebook/Musiliudenn Akinremi

Bayanan hoto, Musiliudenn Akinremi

Haka nan ma a watan na Yulin 2024 ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Arewacin Ibadan a majalisar wakilan Najeriya, Musiliudeen Akinremi ya rasa ransa, tare da barin giɓin wakilci a majalisar.

Kafin rasuwarsa ya kasance shugaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya kan binciken kimiyya.

Majalisun dokokin jihohi

Mazaɓun majalisar dokokin jihohi da ba su da wakilci a halin yanzu kuwa su ne:

  • Adamawa: Mazaɓar Ganye - Abdulmalik Jauro Musa (Mutuwa)
  • Kaduna: Mazaɓar Zariya/Kewaye - Muhammed Dan Asabe (Ajiye aiki)

Mazaɓar Basawa - Jamil Albany (Ajiye aiki)

  • Kano: Mazaɓar Bagwai/Shanono - Halilu Ibrahim Kundila (Mutuwa)
  • Kogi: Mazaɓar Dekina - Enema Paul (Mutuwa)
  • Rivers: Mazaɓar Khana II - Loolo Dinebari (Mutuwa)
  • Neja: Mazaɓar Munya - Joseph Haruna Sduzaof (Mutuwa)

Hakan ya nuna cewa giɓin wakilci a majalisun dokoki ya shafi mazaɓu 14 a jihohi 11 da ke faɗin Najeriya.

Me ya sa INEC ba ta yi zaɓen cike gurbi ba?

...

Asalin hoton, X/Inec

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar zaɓe ta Najeriya ta ce akwai dalilai da dama da suka hana Inec din gudanar da zaɓukan cike guraben na ƴan majalisa.

A tattaunawarta da BBC, Zainab Aminu, wadda jami'a ce a hukumar zaɓe ta Najeriya ta bayyana dalilan kamar haka:

Rashin kuɗi:

"Zaɓen cike gurbi abu ne da ke zuwa ba tare da an shirya ba, kamar misali mutuwa, abu ne da ke zuwa ba a shirya ba, ko masu ajiye muƙami, waɗanda doka ta ba su damar yin hakan, saboda haka hukumar zaɓe ba ta sanya zaɓukan cikin kasasfin kuɗinta na shekara ba".

A cewar ta hakan na nufin cewa Inec ba ta da kuɗaɗen da za ta gudanar da zaɓukan.

Sai dai Zainab Aminu ta ce tuni hukumar ta buƙaci gwamnati ta samar mata da kudin da za ta aiwatar da zaɓukan, kuma da zarar suka samu dama za su gudanar da zaɓukan.

Wasu ayyukan da aka tsara:

Jami'ar hukumar zaɓen ta kuma bayyana cewa hukumar tana da wasu zaɓukan da ta riga ta tsara, kamar zaɓen gwamnonin jihar Anambra, da zaɓukan ƙananan hukumomi a yankin babban birnin tarayya (Abuja).

Haka nan akwai kuma batun ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri'a, kamar yadda jami'ar ta Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta shaida wa BBC.