Me ya sa hukumomin zaɓen jihohi ke 'tsawwala kuɗin' fom?

Masu zaɓe

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Tun bayan hukuncin kotun Ƙolin Najeriya da ya tabbatar da ƴancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi, tuni wasu jihohin ƙasar suka bazama domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihohinsu.

Hukuncin kotun ƙolin ya tanadi cewa duk jihar da ba ta da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi, to gwamnatin tarayya ba za ta tura wa ƙananan hukumominta kuɗaɗensu kai-tsaye ba, maimakon haka gwamnatin tarayya za ta riƙe kuɗin.

Masana da masu sharhi dai na ganin cewa, wannan dalilin ne ya sa gwamnonin suka tashi haiƙan domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihohin nasu.

Tuni dai aka gudanar da zaɓukan a jihohin Adamawa da Yobe, kuma kawo yanzu wasu jihohin ƙasar aƙalla 13 sun bayyana aniyar gudanar da zaɓukan cikin watanni masu zuwa.

Wasu daga cikin jihohin da suka bayyana aniyarsu ta gudanar da zabukan ƙananan hukumomin sun haɗa da Jigawa da Kano da Katsina da Kaduna da Kebbi da Zamfara da Ogun da Enugu da sauransu.

Jihar Bauchi ta sanya ranar 19 ga watan Agusta domin gudanar da zaɓukan, haka ma jihar Kogi ta sanya ranar 19 ga watan Oktoba domin gudanar da zabukan ƙanan hukumomin.

To sai dai wani babban abu da ke jan hankali game da zaɓukan ƙananan hukumomin shi ne zargin da waau jam’iyyu ke yi kan cewa hukumomin zaɓen jihohin sa tsawwala wa kuɗin sayen tsayawa takara, wato fom.

Ko a baya-bayan nan ma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya koka kan yawan kuɗin form ɗin takarar da hukumar zɓen jihar ta saa, ga duk wanda ke sha'awar tsayawa takarar.

Nawa ne kudin fom a jihohin?

Hukumar zaɓen jihar Jigawa da sanya naira miliyan biyar a matsayin kuɗin takardar neman tsaya takarar shugaban ƙaramar hukuma, yayin da ta sanya naira miliyan biyu, ga mai sha'awar tsayawa takarar kansila.

Haka ma a makwafciyar jihar, Kano hukumar zaɓen jihar ta sanya naira miliyan 10 ga duk wanda ke sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma, sannan naira miliyan biyar ga mai sha'awar tsayawa takarar kansila a faɗin jihar.

Koken jam'iyyun hamayya

Ma'akacin INEC

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tuni jam’iyyun hamayya a waɗanan jihohi suka fara kokawa kan abin da suka kira ‘tsawwala musu kuɗin fom’ da hukumomin zaɓen jihohin suka yi.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce “babu jam’iyyar adawar da ta isa ta biya naira miliyan biyar domin shiga zaɓen ƙananan hukukomin” jihar, don haka ne ma ya ce “jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta riga ta lashe zaɓen tun ma kafin a a yi shi”.

Ita ma jam'iyyar APC mai hamayya a jihar Kano - wadda ta ce za ta shiga zaɓen ‘duk da tsadar’ kuɗin fom, amma ta koma kan matakin hukumar zaɓen jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce “abin da hukumar zaɓen jihar ta yi ba komai ba ne face koya wa masu mulkin cin hanci da rashawa.”

“A jihar Kano an ce idan kawai za ka tsaya takarar kansila sai ka biya miliyan biyar, kuma kar ka manta sai ya biya kudin fom na jam’iyya, zai buga bana, da sauran abubuwa, kuma dududu albashin kansila bai wuce (naira) 180,000 ne a wata, to ka ga albashinsa na shekara guda ba lallai ya saya masa fom ba, kuma shekara uku kawai zai yi, to me kake tsammani zai yi idan ya ci zaɓen,’’ kamar yadda ya shaida wa BBC.

'Daƙile mutanen da suka cancanta'

Hoton hannu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zaben kananan hukumomi

A kan wannan lamari, tuni wasu kungiyoyin fararen hula sula fara tsokaci.

Kabiru Sa’id Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al’umma a kan shugabanci nagari da tabbatar da adalci, CAJA, ya ce wannan lamari ne ke hana mutanen da suka cancanta shiga zaɓukan samun muƙami.

Ya ƙara da cewa idan ana sassauto da kudin tsayawa takara, to mutanen da suka cancanta a matakin ƙasa ba za su samu damar shiga a dama da su a zaɓukan ba.

''Idan ka duba galibi mutanen da ke tsayawa takarar kansila, mutane ne da sun san kashi 80 zuwa sama na mutanen da suke wakilta kuma su ma sun san shi, don haka a nan ne mutane suka san mutumin da ya cancanci ya jagorance su, to idan ba shi da wannan kuɗi, ai ba zai iya shiga zaɓen ba'', in ji shi.

''Duk mutumin da ya biya wadannan maƙudan kuɗi don shiga takara, to tabbas akwai tunanin sai ya mayar da kuɗinsa idan ya samu damar ɗarewa kan kujerar da yake neman,'' in ji Kabiru Dakata.

Ba mu da ta cewa a zaɓen ƙananan hukumomi - INEC

Akwatin zabe

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ce ba ta da hannu ko hurumin shirya zaɓukan ƙananan hukumomi, don haka ba za ta ce komai ba kan batun.

Mai magana da yawun hukumar, Hajiya Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa abin da kawai ke tsakanin hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da hukumomin zaɓen jihohi, shi ne INEC kan ba su rajistar masu zaɓe na kowace rumfar zaɓe.

‘’Amma in banda wannan komai nasu ne, su ne ke ɗaukar nauyin kansu, su ke shirya zaɓukansu da kansu, mu ba mu da hurumin wannan,’’ in ji ta.

Martanin hukumar zaɓen jihar Kano

Shugaban hukumar zaɓen jihar Kano Farfesa Malumfashi

Shugaban hukumar zaɓen jihar Kano Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya kare matakin da cewe kuɗin bai yi tsada ba la’akari da darajar muƙaman da ake magana a kai.

‘’Duk wani abu mai kyau ai ba shi da sauki, kujerar ciyaman kuraje mai kyau ce a yanzu fiye da baya’’, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Farfesa Malumfashi ya ce dokar zaɓen jihar ta ba su damar sanya kudin da suka ga ya dace don gudanar da zaben jihar, sannan kuma sun yi la’akari da halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake ciki wajen sanya kuɗin fom ɗin.

‘’Komai ya tashi, kuɗin takardun ya tashi, kuɗin mai da na sufuri komai ya tashi, kuma ma’aikatan da za mu ɗauka don gudanar da wannan zaɓe, za mu ɗauki ma’aikatan wucin gadi fiye da 40,000’’, in ji shi.

Me doka ta ce kan kuɗin takardar tsayawa takara?

kotu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zabe

Barista Abba Hikima Fagge wani lauya ne a Najeriya, ya ce kundin tsarin mulki bai hana hukumomin zaɓukan jihohi sayar da takardar tsayawa takara ba.

Kindin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ne da aka yi wa gyaran fuska ya tanadi kafa hukumomin zabe na jihohi a sashe na 197(1), inda ya ce “za a kafa hukumar zabe mai zaman kanta a kowace jihar da ke cikin tarayyar.”

Sai dai duk da haka an dade ana zargin irin wadannan hukumomin zabe da zama masu aiwatar da ra’ayin gwamnoni, duk da cewa sun sha musanta hakan.

Dalilin da ya sa ake wa hukumomin zaben irin wannan kallo shi yadda a jihohi da dama jam’iyyar da ke da mulki ne kan lashe akasarin kujerun shugabannin na kananan hukumomi da kansiloli, a wani lokacin ma sukan lashe irin wadannan kujeru ne dari bisa dari, lamarin da ke sanya shakku game da sahihancin zabukan.

Hakan ya sa a baya-bayan nan wasu kumgiyoyi masu lura da harkar tafiyar da dimokuradiyya a kasar ta Najeriya suka rika kiraye-kirayen ganin an mayar da alhakin gudanar da zaben a hannun Hukumar zaben tarayya (INEC) ko kuma a kirkiro wata hukumar a matakin tarayyar wadda za ta rika gudanar da zabukan na kananan hukumomi.