Ƙasashe 24 da za su halarci gasar da za a yi a Moroko

Asalin hoton, CAF
Kasashe 24 da suka samu tikitin gasar Nahiyar Afrika ta 2025 wadda za a yi a Moroko sun kamma haɗuwa bayan kammala wasannin neman gurbi da aka yi guda shida.
Za a yi wasanni gasar ta 2025 ne a Moroko tsakanin 21 ga watan Disambar 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026.
Hankali ya tashi a ranar ƙarshe ta wasannin neman gurbin saboda rashin tabbas da wasu ƙasashe da dama suke ciki, waɗanda sai a ranar ƙarshe suka san makamarsu.
Kazalika kasashe 10 na Afrika da ke cikin jadawalin Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa za su halarci wannan gasa wanda suka hada da Morocco, Senegal, Egypt, Nigeria, Algeria, Cote d’Ivoire, Tunisia, Cameroon, Mali, DR Congo.
Akwai waɗanda suka halarci gasar waɗanda suka lashe ta a baya da suka haɗa da Cameroon, DR Congo, Nigeria, Tunisia, Zambia South Africa, Egypt, Sudan, Senegal, Morocco sai kuma Ivory Coast waɗanda duka fitattun 'yan wasansu za su halarta.
Bostwama, ta samu tikitin gasar a ƙarshe, bayan kunnen dokin da ta yi da Egypt 1-1. Gabanin wasan Bostwana na matsayi na uku a rukunin.
Zimbabwe, wadda rabonta da gasar tun 2021, yanzu ta samu gurbin shiga gasar inda ta ƙare a matsayi na biyu a Rukunin J wanda Kamaru ta jagoranta.
A gasar za a kalli Benin da rabonta da gasar tun 2019, Botswana kuma tun 2012, Gabon tun 2021, Uganda itama tun 2019 sai Sudan da ta halarci gasar a ƙarshe 2021 kuma duka ƙasashen nan da shirinsu suka dawo.
Akwai 'yan wasa da dama da za su halarci gasar waɗanda a ƙage suke su nuna kansu yayin wasannin.
Cikakken jerin jadawalin ƙasashen da za su halarci gasar 2025
Moroko ita ce mai masaukin baƙi, Algeria, Angola, Benin, Botswana, Burkina Faso, Cameroon, Comoros, Cote d’Ivoire, DR Congo, Egypt, Equatorial Guinea, Gabon, Mali, Mozambique, Nigeria, Senegal, South Africa, Sudan, Tanzania, Tunisia, Uganda, Zambia, Zimbabwe.











