Mece ce Unrwa, kuma me ya sa Isra'ila ta haramta ayyukanta a Gaza?

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ɗaukar hukumar Unrwa a matsayin abin dogaron rayuwa a Gaza
Lokacin karatu: Minti 5

An umarci Isra'ila ta sake duba matakin da ta ɗauka na haramta ayyukan hukumar bayar da agajin Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya a ƙasar Falasɗinawan.

An kallon Unrwa a matsayin abin dogaron rayuwa a Gaza, inda ayyukan jin ƙai ke ci gaba da taɓarɓarewa. ƙasashen duniya da dama ciki har da manyan ƙawayen Isra'la irinsu Amurka da Birtaniya da Jamus, sun bayyana matuƙar damuwa kan haramta ayyukan hukumar.

Matakin zai yi sake munana ayyukan jin ƙai na hukumar Unrwa, wadda tuni dama ke fama da ƙarancin kayan agajin da ake tsananin buƙata a Gaza.

Haka kuma a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, dokar za ta taƙaita ayyukan hukumar.

An sa ran fara aiki da haramcin nan da wata uku masu zuwa.

“Wannan matakin shi ne na baya-bayan nan cikin gangamin ɓata wa Unrwa sun,” in ji Phillipe Lazzarini, babban kwamishinan Unrwa.

“Wannan mataki ba abin da zai haifar sai ƙara wa falasdinawa wahala,” in ji shi.

Mece ce Unrwa?

Unrwa na nufin Hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hukumar na gudanar da makarantu da wasu asibitoci da sauran ayyukan yau da kullum, da rabar da abinci da kayan agaji ga Falasɗinawa 'yan gudun hijira a Gaza da sauran yankuna.

Yaushe aka kafa Unrwa?

An kafa ta a shekarar 1949 domin tallafa wa 'yan gudun hijirar Falasɗinawa, daga yaƙin 1948 - wanda ya haifar da kafa ƙasar Isra'ila.

Aƙalla Falasdinawa 750,000 aka raba da muhallansu a wannan lokaci, a wani abu da suka bayyana da 'bala'i' (Nakhba)

Hukumar ta ce ta tallafa wa rayuwar 'yan gudun hijirar Falasɗinawa kama da kan kakanni da 'ya'ya da jikoki da tattaɓa-kunne.

Bayanan Unrwa

Wane mutum Unrwa ke ɗaukar nauyi?

A yanzu haka, akwai kimanin 'yan gudun hijirar Falasɗinawa miliyan 5.9 da suka cancanci samun tallafin Unrwa.

Daga cikin wannan adadi, fiye da miliyan 1.5 na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira 58 da Unrwa ke kula da su.

Waɗannan sansanoni kuwa na ƙasashen Jordan da Lebanon da Syria da Zirin Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jodan ciki har da gabashin Birnin Kudus.

Akwai fiye da 'yan gudun hijira 871,000 da aka yi wa rajista a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, kuma kusan kashi ɗaya bisa ukunsu na zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira, kamar yadda Unrwa ta bayyana.

Manyan cibiyoyin hukumar na birnin Amman na ƙasar Jordan, da kuma yankin Zirin Gaza, yayin da take da rassan ofisoshi a wuraren da take ayyukanta: Jordan da Lebanon da Syria da Gaɓar Yamma (ciki har da Gababashin Birnin Kudus), da kuma Zirin Gaza.

Me Unrwa ke yi a Gaza?

Akwai kimanin 'yan gudun hijira miliyan 1.4 a Gaza, sannan akwai sansanoninsu takwas da Unrwa ke kula da su.

Tun bayan fara yaƙin, Da yawa cikin mutanen Gaza miliyan 2.3 sun fice zuwa kudancin yankin, kuma aƙalla Falasɗinawa miliyan guda ne ke zaune a cibiyoyin Unrwa.

Hukumar na da ma'aikata 13,000, kuma ita ce babban hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Gaza.

Unrwa na gudanar da cibiyoyin lafiya da na ilimi, ciki har da cibiyoyin horars da malamai da gudanar da makarantun firamare kusan 300, tare da samar da littattafan karatu don koyar da yaran Falasɗinawa.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makarantar Unrwa da ke birnin Gaza ta koma sansanin masu neman mafaka.

Me ya faru tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Gaza?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fiye da Falasɗinawa 42,000 aka kashe a Gaza, mafi yawancinsu mata da ƙananan yara, tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa don mayar da martani kan harin 7 ga watan Oktoba.

Unrwa ta ce akalla ma'aikatanta 231 aka kashe a Gaza.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutum miliyan 1.9, ko kusan kashi 90 cikin 100 na mutanen Zirin Gaza sun rasa muhallansu. Da dama an yi ta sauya musu wuraren zama, wasu har fiye da sau 10.

Tun bayan da Isra'ila ta sabunta kai hare-hare zuwa arewacin Zirin Gaza a watan Oktoban 2024, ƙungiyoyin agaji ke cewa babu wani kayan agaji da ya shiga yankin.

Alƙaluman Isra'ila sun nuna cewa ayyukan agaji sun tsaya idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci a watan Samunba.

Kafin harin 7 ga watan Oktoba, a kowace rana manyan motocin dakon kayan agaji 500 ne ke shiga Gaza, Amma a cikin kwanaki 10 na farkon watan Oktoban wannan shekara mota 30 kawai ake bari su shiga a kowace rana, adadi mafi ƙaranci tun bayan watan farko na fara yaƙin.

Shirin samar da abinci na Majalisar dinkin Duniya, IPC ya ce kusan mutum miliyan 1.84 ne ke fuskantar matsanancin rashin abinci Hukumar samar da abinci ta, inda 664,000 daga cikinsu ke maakin buƙatar kulawar gaggawa, yayin da 133,000 ke fuskantar 'mummmuna bala'i' a Gaza

Ta yaya Unrwa ke samun kuɗi?

Mafi yawancin kuɗaɗen da take samu suna zuwa ne daga masu tallafi na ƙashin kai, da waɗanda wasu ƙasashe ke bayarwa.

Babbar ƙasar da ta fi bai wa Unrwa talllafi ita ce Amurka, wadda ta bayar da tallafin dala miliyan 422 a 2023, yayin da Jamus ke matsayi na biyu, inda ta bayar da dala miliyan 212.8.

Waɗannan ƙasaseh biyu sun bayar da mafi yawan kuɗin da Unrwa ta ɗaukar nauyin ayyukanta, a kusan dala biliyan 1.46.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani harin Isra'ila ta sama a gaza ra ruguza wata makarantar Unrwa.

Me ya sa Isra'ila ta haramta Unrwa?

Isra'ila na zargin Unrwa da haɗa kai da Hamas a Gaza.

Isra'ila ta shafe gomman shekaru tana adawa da hukumar, amma batun ya ƙara ta'azzara bayan harin 7 ga watan Oktoba, inda ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa masu ɗauke da makamai ta kai hari tare da kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 250.

Daga baya Isra'ila ta yi iƙirarin cewa akwai hannun wasu ma'aikatn Unrwa cikin harin.

Majalisar Dinkin Duniya ta binciki zargin, inda ta kori ma'aikatan hukumar tara cikin watan Agustan da ya gabata.

Hukumar ta ce ta ɗauki bayanan duka ma'aikatanta tare da bai wa Isra'ila jerin sunayen.

Ƙasashen da suka dakatar da tallafin dasuek bai wa hukumar kan wannan zargi, sun ci gaba da bayar da tallafin, in ban da Amurka, wadda ita ce babbar mai mai wa hukumar tallafi.

Amurkan ta ce ba za koma bai wa Unrwa tallafin ba, har sai ta samu abin da ta kira ''cikakken ci gaba''

Me MDD ta ce?

UN Secretary General António Guterres has warned of "devastating consequences" if the banning laws are implemented and said they would be "detrimental for the resolution of the Israeli-Palestinian conflict and for peace and security in the region as a whole".

Babban sakataren Majalisar Dinikin Duniya, António Guterre ya yi gargaɗin cewa za a samu ''mummunan sakamako'' idan aka aiwatar da dokokin da suka haramta Unrwa, kuma hakan zai kawo cikas ga ''yunƙurin sasanta rikicin Isra'ila da Falasɗinawa, da kuma zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya''.

Daraktan hukumar, William Deere, ya ce hukumar "ba ta da wani madogara'' bayan da Isra'ila ta ɗauki aniyar haramta ayyukanta.

"Mu ne ƙashin ayyukan agaji a Gaza,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.