'Muna cikin zulumi saboda wa'adin Turji na biyan diyya na dab da cika'

Asalin hoton, Sheikh Gumi
Al'ummar garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin yanayi da zullumi da zaman dar-dar, yayin da wa'adin da madugun 'yan fashin dajin nan Bello Turji, ya ba su ke daf da cika a ranar Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.
Turji dai ya bukaci jama'ar garin su biya shi Naira miliyan 50 diyyar dabbobinsa da wani kwamandan rundunar sojin Najeriya da aka aika garinsu ya kashe a yayin fada da 'yan bindigar, ko da yake daga baya jama'ar sun roki Turjin ya sassauta masu zuwa Naira miliyan 30.
Tuni dai mazauna garin suka fara yin karo-karo a tsakaninsu, inda masu iyali ke biyan naira dubu 10, marasa iyali kuma ke bayar da naira dubu guda, domin a samu a tattara a kai wa Turjin.
Wasu daga cikin mazauna garin sun shaida wa BBC cewa, tun da Turji ya sanya musu biyan wannan kudi suka shiga zaman dar-dar, saboda rashin sanin abin da zai iya biyo baya.
Mutanen sun ce, bayan tarar, akwai kuma mutanensu da Turjin ke rike da su wanda ya yi barazanar cewa zai kashe su idan har aka ki tara masa kudin.
Wani mazaunin garin da BBC ta tattauna dashi da kuma muka sakaya sunansa, ya ce Turjin ya shaida musu cewa sai an biyashi diyyar sannan zai bari a kwashi amfanin gona.
Ya ce, "Idan mun ce zamu gudu ina zamu, muna ganin wannan shi ne zabi mafi sauki da aka bamu na mu tara wannan kudi don mu bashi."
Wani mai fashin baki kan ayyukan 'yan bindiga a arewacin Najeriya, Mannir Fura Girke, ya shaida wa BBC cewa, ba mutanen Moriki bane suka kashe masa dabbobin, kwamandan sojan da ke Moriki shi ne ya aikata hakan, kuma jajirtacce ne da ya hana barayin daji kai komo a wajen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, dalilin wannan kwamandan ya sa Turji bai isa ya kai hari garin Moriki da kauykan da ke wannan yanki ba, to hakan shi yasa Turjin ya ce sai an biya shi diyyar dabbobinsa.
Daga bangaren gwamnatin jihar ta Zamfara kuwa, mai taimakawa gwamnan jihar kan kafafan yada labarai Mustapha Jafaru Kaura, ya ce a gaskiya gwamnatinsu bata da masaniya a kan wannan mataki na Turji da kuma halin da al'ummar Moriki ke ciki.
Ya ce, "Matsayar gwamnatinmu ita ce ba zata tattauna ko sulhu da 'yan bindiga ba, a don haka a yanzu zamu yi kwakkwaran bincike domin gano silar al'amarin da ma yadda za a kawo wa mutanen Moriki dauki don gane da wannan hali da suka shiga."
"Ba jin dadin gwamnati bane ya kasance akwai bangare na al'ummar jihar na shiga cikin yanayi marar dadi a sanadin ayyukan ‘yan fashin daji ba."
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke cikin yanayi na rashin tsaro, kodayake gwamnatin tarayya da ma ta jihar a kodayaushe na cewa suna iyakacin bakin kokari don shawo kan matsalar tsaron data ki ci taki ci cinyewa a kasar.











