Yaushe za a samu sauƙin matsalar tsaro a jihar Zamfara?

...

Asalin hoton, Getty Images

Dawowar da hare-hare da garkuwa da mutane da kuma kisan al'umma suka yi a jihar Zamfara a ƴan kwanakin nan ya sa al'ummar arewacin ƙasar da ma na Najeriya dasa ayar tambaya - shin akwai yiwuwar jihar ta samu zaman lafiya nan kusa kuwa?

Bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa aƙalla ƙauyuka 50 ƴan bindiga suka tasa a ƙaramar hukumar Zurmi da ke jihar ta Zamfara, inda kuma aka kashe gommai baya ga yin garkuwa da adadin da ba a sani ba.

Wannan lamari ya tilasta wa jama'ar waɗannan ƙauyuka neman mafaka a wurare daban-daban, lamarin da ya ƙara jefa su cikin mummmunan hali na rashin tabbacin yadda rayuwa za ta kasance.

A wata hira da BBC, ɗan majalisa mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilan Najeriya, Bello Hassan Shinkafi ya ce yanzu haka akwai mutane aƙalla 500 da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su daga ƙauyukan yankin.

Shin ko mene ne ke sa matsalar yin kome bayan ta lafa?

Mene ne ke sa matsalar tsaron yin kome?

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare

Asalin hoton, fb/Dauda Lawal Dare

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare

Masanin harkar tsaro kuma lauya mai zaman kansa, barista Bulama Bukarti ya lissafa wasu dalilai guda biyar da ya ce su ne ke sa matsalolin tsaro ke lafawa na ɗan wani lokaci kafin daga bisani su sake yin kome:

  • Nasarar Jami'an tsaro: A duk lokacin da jami'an tsaro ke kai wa 'yan bindiga hari, za ka ji an lafa kai hare-hare saboda an kora 'yan bindigar zuwa cikin dazuka inda suke ɓuya. Saboda haka da zarar sojojin sun janye sai ka ji hare-hare sun dawo.
  • Lokacin tattaunawa kan kuɗin fansa: Akwai lokacin da hare-hare ke lafawa sakamakon yin garkuwa da jama'a masu yawa saboda haka wannan ɗn lokacin da za su kwashe suna karɓar kuɗin fansa sai hare-hare su lafa.
  • Ƙarewar makaman 'yan bindiga: A kan samu yanayin da ake daina kai hare-hare a lokacin da makamansu suka ƙare saboda haka za su dakata da kai hari har zuwa samun sabbin makamai.
  • Amincewa da biyan haraji: 'Yan bindiga kan dakatar da hare-hare idan mutanen gari suka amince su biya harajin da 'yan bindigar suka ɗora musu. To amma da zarar mutanen sun yi turjiya daga baya sai ka ji hare-hare sun yi kome.
  • Sauyin yanayi: Yanayi kamar damuna kan tilasta 'yan bindiga rage kai hare-hare saboda yin amfani da babura a wannan yanayi zai yi wuya.

Girman matsalar tsaro a jihar Zamfara

Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting, ya ce babban abin da ke nuna girman matsalar tsaro a jihar Zamfara shi ne kasancewar ta a gaba-gaba a duk lokacin tattara alƙaluman da kamfanin nasa ke yi.

"A duk lokacin da muka tattara alƙaluma na wata-wata za ka ga jihar Zamfara ta kan zo kodai na ɗaya ko biyu ko uku a Najeriya. Amma ba ta wuce ta uku. Wani lokaci jihar Kaduna ko Benue na shiga gabanta" In ji Malam Kabiru.

Shi ma barista Bulama Bukarti wanda masanin harkar tsaro ne kuma lauya ne mai zaman kansa a Burtaniya, inda ya ce "a iya binciken da nake yi kan matsalar tsaro a ƙasashen tafkin Chadi, ban ga wani wuri a baya-bayan nan da ake kwasar mutane ko kuma a kashe sannan masu kisan da satar suna ƙafafa.

Na saurari hirar da BBC ta saka ranar Talata da safe da wani ɗan majalisa daga jihar wanda ya bayyana yadda ake kora jama'a kamar awaki." In ji Bukarti.

Dalilan rashin tsaro a Zamfara

Masana sun lissafa wasu dalilai da suka ce su ne ke sa matsala ƙin ci ta cinye kamar haka:

  • Yawan makamai a hannun mutanen da bai kamata su mallaka ba
  • Rashin adalcin gwamnatoci
  • Ma'adanai - Zamfara na da albarkatun ƙasa amma ba a tafiyar da su yadda ya kamata.
  • Talauci da jama'ar jihar da dama ke fuskanta.
  • Girman dazukan da hukuma ba ta da iko da su.
  • Taɓarɓarewar zamantakewa.
  • Rashin ingancin tsarin tsaro.
  • Matsalar haɗin-kai tsakanin shugabannin jihar Zamfara - misali yadda babu haɗin kai tsakanin ministan tsaro, Bello Matawalle da gwamna Dauda Dare.

Matakan da gwamnati ke ɗauka

Jihar Zamfara dai ta kwashe shekaru fiye da 10 tana fuskantar wannan matsalar tsaro inda gwamnatoci daban-daban suka yi ta iƙrarin ɗaukar matakan magance matsalar.

Gwamnan jihar na yanzu, Malam Dauda Dare dai ya ce yana ɗaukar dukkan matakan da suka kamata wajen shawo kan matsalar, inda ya sha faɗin cewa "ba zai yi sulhu da 'yan ta'adda ba".

Sai dai yanzu haka gwamnan na ta kai gwauro da mari tsakanin Gusau da Abuja domin sanar da shugaban ƙasa halin da ake ciki.

A baya-bayan nan ya shaida wa BBC cewa "mun gana da shugaba Tinubu kuma na faɗa masa wasu abubuwan da bai sani ba ni kuma ya faɗa min irin shirin da gwamnati ke yi."

Wasu daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka sun haɗa da yin amfani da 'yan sa-kai da hana sayar da man fetir cikin jarka da hana sayar da buredi da kuma sanya dokar hana shigar ababan hawa cikin jihar da daddare.

Mece ce mafita ga jihar?

...

Asalin hoton, ZAMFARA STATE GOVERNMENT

Malam Kabiru Adamu da barista Bulama Bukarti dai na ganin cewa alhakin magance matsalar tsaron jihar ta Zamfara ya fi rataya a wuyan gwamnatin tarayya kasancewar gwamna ba shi da ɗansanda ballantana soja, duk da cewa gwamnatin jihar da ma al'umma na da rawar takawa.

Masanan guda biyu sun yi ittifaƙin cewa lallai akwai mafita ga jihar da ma sauran jihohin arewacin Najeriya da ke fuskatar matsalar tsaro.

"Nan gaba ma idan aka faɗa wa ƙananan yara cewa jihar Zamfara ta fuskanci matsalar tsaro, za su yi mamaki kasancewar ba su sami matsalar ba." In ji barista Bulama Bukarti.

Bukarti da Malam Kabiru dukkanninsu sun amince da waɗannan hanyoyin guda takwas da idan aka bi su matsalar tsaro a jahar Zamfara za ta zama tarihi:

  • Rage amfani da ƙarfin soji da ɓullo da hanyoyin tattaunawa.
  • Idan jami'an tsaro sun samu nasara su daina janye jiki.
  • Rage yawan makaman da ke hannun al'umma.
  • Tabbatar da dakarun sa-kai na aiki bisa tsarin dokokin duniya na kare hakkin ɗan adam.
  • Tabbatar da adalci tsakanin al'umma ta hanyar hukunta duk wanda ya yi laifi ba tare da tsoro ko nuna fifiko ga wani ɓangaren al'umma ba.
  • Shugabanci na gari domin rage talauci.
  • Samar da hanyoyin ilmantar da jama'a.
  • Shigar da sarakunan gargajiya.