Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tsadar kuɗin haya ke jefa iyalai cikin mummunan yanayi a Legas
- Marubuci, Dara Onipede
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Video Journalist
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 4
Lokacin da Sade George ta auri mijinta, Tade, shekara 18 da suka wuce, ta yi imanin cewa za su kasance har abada. Suna matukar son junansu kuma sun haifi yaro ɗaya.
Sai dai ba ta taɓa tsammanin cewa lokaci zai zo da za su rasa wurin zama ba. Waɗannan ba sunayensu na asali ba ne. Sun buƙaci mu sauya sunayen.
A tsawon shekara goma, iyalan sun zauna a gida mai ɗaki biyu a yankin Yaba da ke jihar Legas, kusa da wata jami'a inda Sade ke aiki.
Sai dai a bara, lokacin da wadda ta mallaki wajen da suke zama ta ƙara kuɗin haya da kashi 177 daga naira 650,000 zuwa naira miliyan 1.8, lamarin da ya zama silar durkusar da iyalan.
"Mun kasance muna zama a matsayin iyalai har sai da aka ƙara mana kuɗin haya," kamar yadda Sade ta faɗa wa BBC. "Tilas na kom gidan ƴan uwanmu a anguwar Ikorodu, sai dai mijina ya ki komawa can. A yanzu, ina zaune tare ɗiyata."
Yayin ma'auratan suka kasa biyan ƙarin kuɗin haya da aka yi musu da kuma samun wani sabon wurin zama, Sade ta samu damar komawa gidan ƴan uwanta a Ikorodu, mai nisan kilomita 32 daga wajen da take aiki da kuma zama a baya.
Mijinta, Tade yana aiki a Onipanu, mai nisan shida da tsohon gidan da suke zama.
Lokacin da suke zama a Yaba, Sade na biyan naira 200 domin zuwa wajen aiki a kowace rana, amma yanzu, tana biyan kuɗin mota aƙalla 3,000 a kowace rana don zuwa aiki tsakanin Yaba da Ikorodu.
Ƙarin kuɗin hawan mota ba shi ne kaɗai take biya a yanzu ba. Lamarin ya fara taɓa lafiyarta.
Ta kasance tana fama da wata lalura ta rashin lafiya a tsawon kuruciyarta, kuma tana zuwa ganin likita lokaci zuwa lokaci a asibiti a Ikeja, mai nisan kilomita 13 daga tsohon wajen da take zama a Yaba.
Yanzu, tana tafiyar kilomita 25 don zuwa ganin likita daga Ikorodu, tafiya mai nisa ga kuma cunkoson ababen hawa da aka san jihar Legas da shi.
Sauya muhalli don dole
A shekarun baya-bayan nan, matsalar tsadar rayuwa ya kasance abu da ƴan Najeriya ke fama da shi, inda miliyoyin mutane da kuma iyalai a faɗin ƙasar ke shiga uƙuba.
Daga fafutukar samun abinci da kuma sauran abubuwa na rayuwa, mutane na nisan tafiya ta kilomitoci daga wajen aiki da kuma barin maƙwabta waɗanda suke so, zuwa wurare masu sauki - musamman a wajen birane domin zama - sai dai a can ɗin ma yanzu kuɗin haya na ƙaruwa.
Sai dai yayin da kuɗin haya ke ƙaruwa a waɗannan wurare, mutane da dama na sauya muhalli daga nan zuwa can domin samun sauki.
Wannan shi ne labarin Paul Jegede, wanda ke aiki da kamfanin gine-gine a Ajah, wata anguwa da ke Legas Island, inda yake zama a wani gida mai ɗaki ɗaya da kuɗin hayarsa ya kai naira miliyan 1.1 a duk shekara. Yunkurin neman babban gida lokacin da ya tashi yin aure ne ya sa ya gano cewa kuɗin hayar gidaje a Ajha ya fi karfinsa.
"Tsadar kuɗin haya ya sa na tashi daga Ajah zuwa wani wuri," kamar yadda Jegede ya faɗa wa BBC.
A yanzu ya ƙaura zuwa wata anguwar Egbeda mai nisan kilomita 60. Kafin ya bar Ajah, minti 15 yake ɗaukarsa zuwa aiki, amma yanzu yana shafe kusan sa'a huɗu a kan hanya kafin ya isa wajen aiki, musamman idan ya haɗu da cunkoso.
A sabon gidansa a rukunin gidaje na Gowon, a Egbeda, yana biyan naira 900,000 a gida mai ɗaki biyu da yake zaune a ciki.
Yana kuma biyan kuɗin mota naira 80,000 don zuwa a kowane wata, inda a baya yake biyan 35,000 lokacin da yake zama a Ajah.
Kuɗaɗen mutane na ƙarewa - 'Ana kai su makura'
Wannan ba shi ne ɗaukacin sadaukarwa da ya yi ba. A yanzu, Jegede na tashi narci da misalin karfe 4 na asuba, inda yake barin gida da karfe 5:15 na safe domin kauce wa cunkoson ababen hawa da kuma isa aiki a kan lokaci.
"Akwai ranar da na tashi karfe 4 na asuba ian ta kuka. Na gajiya matuka. Na faɗa wa kaina, 'shin dole ne sai na je aiki yau?" in ji Jegede.
Samun wurin zama abu ne na wajibi da ɗan'adam ke buƙatar samu, sai dai miliyoyin mutane a Legas, birni mafi yawan jama'a a Afrika, hakan yana ƙara yi wa mutane wahala. Yayin da wasu mutane ke cewa ana ƙoƙarin talautasu sakamakon ƙara kuɗin haya, wasu kuwa na rasa komai, musamman ƴan kuɗaɗe da ke hannunsu - inda suke yin duk mai wuya wajen samun wurin zama.
Kofo Williams, wata ɗaliba a kwalejin kimiyya da fasaha da kuma mai aikin gyaran farce - ta kasance tana aiki da kuma zama a Akoka, wata anguwa mai cike da ɗalibai inda kuma sana'ar ke tafiya yadda ya kamata.
Lokacin da mamallakin gidan da suke ciki a baya da kuma shagon da take ciki suka ƙara kuɗin haya - a lokta daban-daban - hakan ya tilasta mata samun wuri mai sauki har ta kai ta koma haɗa gidan zama da kuma san'ar ta zuwa wuri ɗaya. Ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin hayar wurare biyu ba.
Kuɗin hayar da take biya a tsohon gidan da take zama mai ɗaki biyu ya ƙaru daga naira miliyan 1.2 zuwa miliyan 1.8 duk shekara, abu kuma da ba za ta iya biya ba. Sabon wurin da ta koma, kuɗin ɗaki ɗaya ya kai N800,000.
Amma Iyana Oworo, inda ta koma yana da nisa da wurin da makarantar ta da kuma kwastomominta suke.
Kofo da ke biya wa kanta kuɗin makaranta - wadda kuma ke samun N300,00 a kowane wata lokacin da take da shagonta a Akoka, da kyar take samun N50,000 a wata yanzu.
Legas, wadda ake ɗauka a matsayin babbar cibiyar kasuwancin Najeriya na cike da damarmaki, amma ga mutane da dama, tsadar rayuwa a Legas na ƙorarsu sannu a hankali a birnin da kuma kashe musu mafarkin samun cigagan rayuwa.
Labaran Paul da Kofo da kuma Sade kaɗan ne daga cikin irin mawuyacin hali da miliyoyin mutane ke shiga wajen samun wurin zama a jihar mai al'umma sama da miliyan 21.