Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Trump ya iya dakatar da yaƙin Gaza amma ya gaza a Ukraine?
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Arewacin Amurka
- Lokacin karatu: Minti 4
Da alama an kuzuzuta shirin ganawar da shugabannin Amurka da na Rasha za su yi game da yaƙin Ukraine fiye da kima.
'Yan kwanaki bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya tsara ganawa da Shugaban Rasha Vladmir Putin a birnin Budapest - "cikin mako biyu ko kusa da haka" - an dakatar da shirin har sai abin da hali ya yi.
Shi ma wani taron gaisawa da juna tsakanin jami'an difilomasiyyar ƙasashen biyu an soke shi.
"Ba ni son na yi taron shan shayi kawai," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai a fadar White House ranar Talata. "Za mu ga yadda za a yi dai."
Rikita-rikitar ita ce ta baya-bayan nan a yunƙurin Trump na samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha - wanda yake so ya ɗora kan nasarar da aka samu ta dakatar da yaƙin Gaza.
Da yake magana a Masar a makon da ya gabata wajen ƙulla yarjejeniyar yaƙin Gaza, Trump ya bai wa hadiminsa Steve Witkoff sabon aiki.
"Ya kamata mu kawo ƙarshen yaƙin Rasha," in ji shi.
Sai dai kuma, abubuwan da suka bai wa Witkoff da tawagarsa damar samun nasara a dakatar da yaƙin Gaza sun sha bamban kuma za su yi wuyar cimmawa a yaƙin Ukraine, wanda aka shafe kusan shekara huɗu ana yi.
Ƙarancin dama
A cewar Witkoff, babban abin da ya jawo Isra'ila teburin tattaunawa shi ne harin da ta kai wa shugabannin Hamas a Qatar. Matakin ya ɓata wa Larabawa ƙawayen Amurka rai, wanda kuma ya bai wa Amurka damar matsa wa Firaministan Isra'ila Netanyahu wajen amincewa da yarjejeniyar.
Trump ɗin ya yi amfani da goyon bayan da ya saba bai wa Isra'ila, ciki har da mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Birnin Ƙudus da amincewa da wuraren Yahudawa da suka saɓa wa doka, da kuma goyon bayan hare-haren da Isra'ila ta kai wa Iran.
Hasali ma, Trump ya fi Netanyahu farin jini tsakanin Isra'ilawa - wanda hakan ya ba shi damar takura wa firaministan.
Idan aka haɗa wannan da kyakkyawar tattalin arziki da soji da yake da su wajen sauran ƙasashen Larabawan yankin, Trump na da dama mai yawa ta tilasta ƙulla yarjejeniyar.
A yaƙin Ukraine, Trump ba shi da wata damar kirki. Ya sha yunƙurin tilasta wa Putin da Zelensky cikin wata tara da suka gabata, amma babu wata nasara.
Trump ya yi barazanar saka wa Rasha sababbin takunkumai a fannin makamashi da kuma bai wa Ukraine makamai masu linzami masu cin dogon zango. Amma ya ji tsoron yin hakan zai illata tattalin arzikin duniya da kuma ta'azzara yaƙin.
Trump ya sha nuna alfahari da ƙwarewarsa wajen ƙulla yarjejeniya, amma har yanzu ganawar da ya yi da Zelensky da Putin ba ta kama hanyar kawo ƙarshen yaƙin ba.
A watan Yuli, Putin ya amince da wata ganawa a Alaska a daidai lokacin da aka yi zaton Trump na gab da sanya hannu kan dokar takunkumai kan Rasha. Amma sai aka dakatar da batun daga baya.
A makon da ya gabata kuma daidai lokacin da aka ce Amurka na shirin aika wa Ukraine makamai masu linzami na Tomahawk da Patriot na tsaron sararin samaniya, Putin ya kira Trump wanda shi kuma ya nemi su gana a Budapest.
Washegari Trimp ya karɓi baƙuncin Zelensky a Fadar White House, amma ya bar fadar ba tare da samun komai ba bayan wata ganawa mai cike da hayaniya a tsakaninsu.
Trump ya haƙiƙance cewa Putin shi yi masa wasa da hankali.
"Kun sani cewa mafi ƙwarewa daga cikinsu sun sha yin mani wasa da hankali, amma kuma a ƙarshe na yi nasara," a cewarsa.
Daga baya shugaban na Ukraine ya yi bayani kan abubuwan da suka faru.
"Jim kaɗan bayan ta bayyana ba za mu samu makaman masu cin dogon zango ba - sai Rasha ta ƙara ja da baya game da maganar tattaunawar difilomasiyya," kamar yadda ya bayyana.
Saboda haka, cikin 'yan kwanaki Trump ya rikiɗe daga mai shirin bai wa Ukraine makamai zuwa mai shirin ganawa da Putin a Budapest da kuma matsa wa Ukraine a asirce ta amince da bai wa Rasha yankin Donbas - ciki har da wuraren da Rashar ma ba ta mamaye ba tukunna.
Trump ya sha faɗa yayin yaƙin neman zaɓensa cewa zai iya kawo ƙarshen yaƙin Ukraine cikin 'yan awanni. Tuni ya daina wannan batun, yana mai cewa abin ya wuce yadda aka yi tsammani.
Ba a saba jin sa yana bayyana gazawa ba game da ikonsa.