Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makaman Rasha masu gudun walƙiya da ke yi wa ƙasashen Turai barazana
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin a fannin tsaro
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin wani faretin soji a birnin Beijing, makamai masu linzami rundunar sojin China ta People's Liberation Army na wucewa a hankali rataye a kan manyan motoci masu launin kakin soji.
Makaman masu tsawon mita 11 da nauyin tan 15, kowannensu na ɗauke da kalmomi da lambobi na "DF-17".
A wannan lokacin ne China ta ƙaddamar wa duniya da sabon makaminta Dongfeng mai linzami mai gudun walƙiya - wanda ake kira hypersonic a Turance.
An yi hakan ne ranar 1 ga watan Oktoban 2019.
Da ma Amurka na sane da shirin na China, amma kuma tuni Chinar ta ci gaba da inganta makaman tun daga lokacin.
Saboda tsabar gudunsu da kuma zilliya - inda suke da sauri ninki biyar na gudun sauti - makamai ne da ka iya sauya yadda ake fafata yaƙi a yanzu.
Hakan ta sa yanzu ƙasashe ke rige-rigen samar da su.
Rasha, China, Amurka: rigegeniyar nuna iko
Bikin faretin na Beijing ya jawo raɗe-raɗi game da barazanar da China ke yi wa ƙasashen Yamma da makamanta masu linzami. Yanzu ita ce kan gaba wajen samar da su, sai kuma Rasha da ke biye mata.
Amurka kuma, na ƙoƙarin kamo su ne, yayin da Birtaniya kuma ba ta da su.
William Freer, wani mai nazarin harkokin tsaro a cibiyar Council on Geostrategy, na ganin dalilin da ya sa Rasha da China suka zarce saura abu ne mai sauƙi.
"Sun yanke shawarar zuba kuɗaɗe masu yawa a waɗannan fannonin tun shekaru baya."
A gefe guda kuma, ƙasashen Yamma sun fi mayar da hankali tun daga shekara 20 da suka wuce wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi a gida da kuma ƙasashen waje.
A lokacin, yiwuwar gwabza yaƙi tsakanin manyan ƙasashe masu ƙarfin soji iri ɗaya ba ta da yawa.
"Abin da ya faru shi ne, mun gaza wajen lura da barazanar China wajen inganta rundunar sojinta," kamar yadda Sir Alex Younger, wanda ya bar muƙamin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Birtaniya a 2020, ya bayyana.
Sauran ƙasashe na ta ƙoƙari su ma: Isra'ila na da makamin hypersonic mai suna Arrow 3 wanda aka ƙirƙira domin kakkaɓo makamai.
Iran ta yi iƙirarin cewa tana da shi, wanda ta ce ta harba wa Isra'ila lokacin yaƙin kwana 12 da suka gwabza a watan Yuni.
(Tabbas makamin ya yi gudun walƙiya amma ba a tunanin yana da ikon zilliya mai yawa da za a kira shi cikakken hypersonic).
Koriya ta Arewa ma na ta yin aiki kan nata tun 2021, har ma ta yi iƙirarin cewa tana da makamin.
Yanzu Amurka da Birtaniya na zuba kuɗaɗe a fannin makaman hypersonic, kamar yadda saura kamar Japan da Faransa ke yi.
Amurka ta ƙaddamar da nata makamin mai gudun hypersonic mai suna "Dark Eagle".
Amma dai a yanzu China da Rasha ne kan gaba sosai - inda wasu masana a ƙasashen Yamma ke cewa abin damuwa ne.
Ɗankaren gudu da mummunar ɓarna
Kalmar hypersonic na nufin wani abu mai gudun tsiya kan ma'aunin March 5 ko sama da haka. Ma'ana mai gudu ninki biyar na sauti ko kuma gudun mil 3,858 cikin awa ɗaya.
Wannan gudun nasu shi ne abin da ya sa ake fargaba game da su.
Makamin da aka sani mafi gudu zuwa yanzu shi ne na Rasha mai suna Avangard - wanda aka ce yakan yi gudun Mach 27 (kusan mil 20,700 cikin awa daya) - kodayake an fi ambato gudun Mach 12.
Game da ɓarnar da suke haifarwa, irin waɗannan makaman ba su fi sauran makamai masu linzami haɗari mai yawa ba, a cewar Mista Freer.
"Wahalar ganowa da kuma kakkaɓo su ce ke sakawa ana tsoronsu sosai."
Akan harba su ne da taimakon wani roka, idan suka kai ƙololuwar tashi sai kuma su shiga wani yanayi da ake kira "scramjet engine" wanda shi kuma zai yi musu jagora domin dira inda aka aika su.
Akan yi amfani da su ta hanya biyu, ma'ana bam ɗin suke ɗauke da shi zai iya zama na nukiliya ko kuma gama-garin bam.
Kafin a ayyana makami a matsayin mai gudun walƙiya na hypersonic, dole ne sai ya mallaki ikon zillewa makaman kariya. Wanda ya harba shi zai dinga sassauya masa hanyar tafiya ta yadda abokin gabarsa ba zai iya gane shi ba har sai ya dira kan wurin da ya nufa.
"Ta hanyar kauce wa nau'rorin leƙen samaniya, sukan kauce wa abokan gaba har sai lokacin da suke dab da isa wanda hakan zai sa babu damar da za a iya tare su," Patrycja Bazylczyk, mai bincike a sashen Missile Defence Project na cibiyar Centre for Strategic and International Studies da ke Amurka.