Ɗaya daga bala'o'in ƙwallon ƙafa mafiya muni ya kashe mutum 124

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

Mutum aƙalla 124 ne suka mutu sakamakon rushewar gini a wani filin wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Indonesia, wanda ya zama ɗaya daga cikin hatsarin ƙwallon ƙafa mafiya muni a duniya.

Haka nan ɗaruruwan mutane sun ji raunuka bayan wasan da ƙungiyar Arema FC ta yi rashin nasara har gida a hannun babbar abokiyar hamayyarta Malang ranar Asabar a yankin Gabashin Java.

Hatsarin ya faru ne bayan 'yan sanda sun harba barkonon-tsohuwa kan magoya bayan da suka antayo cikin filin wasa. Yayin da hankali ya fara tashi, sai dubban magoya baya suka nufi hanyar fita daga filin na Kanjuruhan, abin da ya sa wasu da yawa suka sume.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa, ta ce "bai kamata" 'yan sanda su harba barkonon-tsohuwa ba" kan 'yan kallo yayin wasanni.

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya faɗa wa BBC cewa 'yan sanda "sun yi ta harba hayaƙi mai sa hawaye cikin sauri" bayan lamarin ya fara ƙamari.

Lamarin ya wuce gona da iri - 'Yan sanda

Indonesia

Asalin hoton, AFP

Tun da farko hukumomi sun ce waɗanda suka mutu sun kai 174 amma daga baya sai aka rage yawan adadin.

Shugaban Ƙasa Joko Widodo ya ba da umarnin dakatar da dukkan wasannin babbar gasar ƙasar har sai an kammala bincike.

Wasu bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna 'yan kallo na shiga fili a guje bayan busa tashi, yayin da su kuma 'yan sanda ke harba hayaƙi.

"Abin ya fara wuce gona da iri. Sun fara kai wa 'yan sanda hari tare da lalata motoci," a cewar Nico Afinta, shugaban 'yan sanda na yankin Gabashin Java.

Ya ƙara da cewa 'yan sanda biyu na cikin waɗanda suka mutu.

"Muna tabbatar da cewa ba dukansu ne suka tayar da fitina ba, mutum 3,000 ne kawai da suka shiga cikin fili," in ji shi.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Indonesia ta ce ta ƙaddamar da bincike, tana mai cewa "lamarin ya ɓata sunan ƙwallon ƙafar Indonesia".

Tashin hankali a filayen wasa na Indonesia ba sabon abu ba ne kuma Arema FC da Persebaya Surabaya daɗaɗɗun abokan hamayya ne.

Ɗaya daga cikin bala'o'ii mafiya muni

Motocin 'yan sandan Indonesia

Asalin hoton, EPA

Turmutsutsin da ya faru ɗaya ne daga cikin mafiya muni a jerin waɗanda suka faru a filayen wasan ƙwallon ƙafa.

A 1964, jimillar mutum 320 ne suka mutu sannan wasu 1,000 suka ji raunuka sakamakon turmutsitsin da ya afku a wasan neman shiga gasar Olympic tsakanin Peru da Argentina a Lima.

A 1985, mutum 39 sun mutu sannan wasu 600 suka jikkata a filin wasa na Heysel da ke Belgium lokacin da aka ritsa 'yan kallo a jikin wani bango yayin wasan ƙarshe a kofin European Cup tsakanin kulob ɗin Liverpool da Juventus.

A Birtaniya, wani hatsarin rushewar gini a filin wasa na Hillsborough da ke Sheffield a 1989 ya yi sanadiyyar mutuwar magoya bayan Liverpool 97 da ke halartar wasan na gasar FA tsakaninsu da Nottingham Forest.