Kamfanonin man ja da ke ci da gumin miliyoyin mutane a fadin duniya

Ridah, 35, Cilin, 60, Siti, 60, Dan Yenita, 12, duka 'yan kabilar Orang Rimba Desa ne, a yankin Tebing Tinggi

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Kabilar Orang Rimba na daya daga cikin kabilun Fulanin da suka rage a Indonesia
    • Marubuci, Daga Muhammad Irham da Astudestra Ajengrastri da Aghnia Adzkia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Indonesia

Yawancin kayan da ake saya a manyan kantuna suna dauke da man-ja komai kankantarsa. Idan aka yi waiwaye kan yadda aka samar da shi, ba mamaki a samu daya daga cikin bishiyar kwakwar man-ja watakila daga Indonesia.

Sai dai manyan kamfanonin da suke sayar da man-ja kamar Johnson & Johnson da Kellogg da kuma Mondelēz, na ci da gumin miliyoyin mutanen yankunan da ake amfani da kwakwar man ja na kudaden shiga na miliyoyin daloli, kamar yadda binciken hadin gwiwa da BBC ya bankado.

Mat Yadi yana bakin kogi ya dana tarkonsa. Sai dai a yau, kamar sauran ranaku bai kama komai ba.

"Kafin wannan lokacin ana samun aladu, da gada, da barewa, da sauran namun daji," in ji shi. "A yanzu kusan komai ya mutu."

Dan kabilar Orang Rimba - daya daga cikin kabilun Fulani da suka rage a Indonesia. Tun zamanin iyaye da kakanni, sun rayu ne a dajin da ke tsibirin Sumatra - inda suke noman roba da kayan marmari da farauta.

A shekarun 1990, wani kamfanin man-ja ya iso yankin da al'umar Tebing Tinggi ke rayuwa, da alkawarin inganta tattalin arzikin da ci gaba.

Muatane kabilar Orang Rumba sun ce kamfanin ya zo da tsarin ban-gishiri-in-ba-ka manda, wato za su amshi gonakin da suka gada iyaye da kakanni.

Yayin da su kuma za a su samu tagomashin fiye da rabin abin da suka ba da, wanda gonakin cike da bishiyoyin kwakwar man ja, yayin da duniya ke tsananin bukatarsu.

Sama da shekaru 25, bishiyoyin kwakwa sun girma sosai, yayin da 'ya'yan kwakwar masu launin ruwan goro, kuma tuni suka fara cika kamfanonin man ja.

Ana samar da miliyoyin daloli daga cinikin man-jan da ake girki da shi, kamfanin Salim Group ne yake cin gajiyar hakan. Shi ne ya kawo wasu kamfanonin kamar Cadbury wanda ke yin cakulet da sauransu.

Siti Maninah

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Siti Maninah na dogaro ga 'yar kwakwar manjan da ta fado kasa domin samun abin kai wa bakin salati

Sai dai Mat Yadi ya ce ba a ba shi ko kwabo ba kamar yadda aka yi wa kabilarsu alkawari ba.

A yanzu yana rayuwa a cikin karamar bukkar da ke tsakiyar gonakin kwakwa.

"Babu abin da aka ba mu. Sun kwashe mana komai," in ji shi .

Kamar kowa a kabilar Orang Rimba, tsohuwa Siti Maninah ta dogara ga 'ya'yan kwakwar da ke fadowa kasa a lokacin da ma'aikatan kamfanonin yin man ja ke aikin cire ta.

Idan ta yi sa'a, za ta iya samun da yawa domin saidawa ta sayo 'yar shinkafa da kayan miya domin ciyar da iyalanta na kwana guda. "Yana isa," in ji ta. "Sai dai babu wadata."

"Wannan kankanin misali ne, hakan ke faruwa a ko'ina," in ji Daniel Johan, dan majalisa a Indonesia, wanda ya yi nazari kan fannin noma da alkinta dazuka, wanda yake wakiltar kabilun. "Kamfanonin ba su da imani."

Man ja

Yawancin manyan dazukan da ake da su a duniya, an share su tare da shuka bishiyoyin kwakwa, domin samun man-ja.

A wani daji da ke tsibirin Borneo da Sumatra a Indonesia, an shuka kwakwar jere reras ba ka iya ganin karshen ta.

Asalin cinikin an yi shi ne da alkawarin huldar kasuwanci da samar da ci gaba.

Kamfanoni na bukatar samun goyon baya da mu'amalar kai tsaye da gwamnati, sai suka yi alkawarin raba riba daidai da kauyawan da suka ba da gonakinsu a karkashin wani shiri mai suna "plasma".

A shekarar 2007, aka amince da bai wa kamfanonin, su kuma za su bai wa kauyawan rabin abin da aka samar a gonakin.

In da wannan shirin ya yi aiki, zai taimakawa mazauna karkara wanke daudar talauci da suke fama da ita, da ba su damar samun kudaden da suka kai dala biliyan 50 a kowacce shekara a duniya baki daya.

Sai dai danbarwar cin hanci da rashawa da ta bulla daga kamfanonin, ta janyo sun gagara cika alkawarin da suka dauka karkashin shirin plasma.

Hoton tauraron dan adam na bishiyoyin kwakwar man-ja ne suka mamaye dazukan Indonesia

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Bishiyoyin kwakwar man-ja ne suka mamaye dazukan Indonesia

Babu wanda ya san girman matsalar, amma shekaru biyu da suka wuce tawagar BBC da ta hada da 'yan-jarida masu binciken kwakwaf, da masu kare muhalli suka taru wuri guda tare da gano bakin zaren.

Nazari a kan kididdigar gwamnati, bincike ya gano kamfanoni sun gagara ba da eka 100,000, kwatankwacin girman birnin Los Angeles - wanda aka samu ta hanya karkashin shirin Palasma kadai a Borneo da ke tsakiyar yankin Kalimantan.

Idan aka yi kididdiga da kidaya ribar da aka samu ta hanyar gonakin man-ja a hannun al'umomin yakin, ta kai ta dala miliyan 90 a kowacce shekara.

Wannan bincike ne kan kamfanoni biyar kacal da ke gudanar da ayyuka a Indonesia.

Dan kabilar Orangi na tsintar kwakwar da ta fado kasa, domin saidawa masu aikin man-ja

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Idan kauyawan suka samu kilo goma na kwakwa, kudin zai ishe su ciyar da iyalansu na rana guda

Ba za ka taba ganin girman matsalar a ofishin gwamnati ba.

Tawagarmu ta samar da wata kididdiga ta kamfanonin da ake zargi da kasa cika alkawari, ko wadanda ba su cimma ka'aidojin da aka gindaya musu ba, ta yadda za su yi rabon abin da suka samu da kauyawan da ke yankunan.

Wataƙila wayarku ba za ta iya nuna waɗannan hotuna ba

A shekarar 2011, an cimma wata yarjejeniya da 'yan siyasar yankunanan, kamfanin Salim Group sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar cikawa al'umar Orang Rimba alkawarin da suka dauka karkashin shirin Plasma.

Amma a watan Junairun 2017, babu abin da ya sauya. A lokacin kabilun sun gaji da jiran shekaru 20 kenan.

Kabilar Orang Rimba na rayuwa a wuraren da suka samar kusa da gonakin kwakwar

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Kabilun na rayuwa a bukkoki ko rumfunan da suka kafa kusa da gonakin kwakwar

Kabilun da suka fusata kan mamaye musu gonakin da aka yi, da alkawarin kanzon-kurege daga kamfanonin, sun gaji bayan budar ido su wayi gari kamfanonin sun rushe musu matsugunai.

A martanin da suka mai da sun banka wa wani ofsihin jami'an tsaro da ke gonaar wuta, tare da farfasa tagogin babban ofishin.

Sama da mutum 40 aka cafke, kuma jami'an tsaro suka lakada musu domin karen duka, kamar yadda suka shaida mana.

"Ba tare da tambaya ko jin bahasi ba, kawai suka fara dukanmu, sun yi mana jini da majina," in ji wani mutum.

Bakwai daga ciki an yanke musu hukuncin zaman kaso na watanni 18, kan laifin lalata dukiyar jami'an tsaro.

'Yan-sandan Indonesia sun ki mayar da martani kan zargin, lokacin da muka tuntube su.

Bayan zanga-zangar, an bukaci kamfanin Salim Group ya dawo wa da kabilar Orang Rimba gonakin da suka gada tun kakannin-kakanninsu, amma shekara biyar ke nan, kabilun na jiran gawon shanu.

Kamfanin Salim Group ya ce kudaden tallafin da ke kula da gonakin sun ki amincewa su ce uffan kan tambayarmu.

Mat Yadi

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Mat Yadi na kabilar Orangi ya ce kamfanin Salim Group bai cika musu alkawari ba

A lokacin da al'umar yankin su ka yi korafi kan gaza cika alkawarin da aka yi musu, gwamnati ta dogara ne ga tattaunawar sulhu, sai dai binciken da aka yi ya gano an cimma kashi 14 cikin 100 na yarjejeniyar da aka cimma tun da fari.

Samsul Kamar, shugaban rukunin gonaki mafi girma Riau a Indonesia, kuma kamfanin da ya fi samar da man-ja, ya ce ya sake shigar da wani korafin kan shirin Plasma, kusan yana hakan a kowanne mako.

Sai dai mun gano kamfanoni 13 da ke ja gaba ciki har da Colgate da Palmolive da kuma Reckitt , sama da shekaru shida ke nan suna kwasar ganima daga shirin Plasma.

Gonakin man-ja a gabashin Kalimantan

Asalin hoton, Nanang Sujana

Bayanan hoto, Gonakin man-ja a gabashin Kalimantan

Dukkan kamfanonin Johnson & Johnson da Kellogg suna sayen kaya daga Salim Group, wanda shi ke da gonar da kabilar Orang Rimba ta ba da haya.

A martani kan bincikenmu, kamfanonin sun ce suna umartar masu kawo kaya su bi doka da oda.

Sai dai mun gano yawancin masu kayan suna da alaka da kamfanonin da kowa ya san sun gagara cika alkawarun da suka dauka da kuma suke cikin harkar shirin Plasma, ciki har da jami'an gwamnatin Indonesia.

Kamfanin Johnson & Johnson ya ce "ya dauki wadannan zarge-zargen da muhimmanciu" tare da nuna takaici da bakin ciki kan hakan, sun ce za su yi aiki kafada da kafada da abokan huldarsu domin daukar matakin da ya dace.

Shi ma Mondelēz, mamallakin Cadbury ya ce sun tuntubi kwararru domin daukar mataki.

Reckitt ya rubuta cewa ''wannna matsala ce da ya kamata a yi nazari aka yi" domin haka bincike mai zurfi zai fi alfanu a nan.

Shi kuwa Colgate-Palmolive ya ce kamfanin zai dinga alaka kai-tsaye da masu kawo kayayyaki domin kaucewa matsayi irin hakan.

An yi wa kauyawa alkawarin ababen more rayuwa

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, An yi alkawarin inganta rayuwar mutanen karkara da ababen more rayuwa albarkacin man-ja

Kamfanin da ke yin man-ja a Borneo mai suna Golden Agri-Resources, daya ne daga cikin manyan kamfanon man-ja a kasar, ya na da gonakin kwakwa kusan eka 500,000.

Kamfanin ya amince bai cimma ka'idoji kamar yadda ya dace ba a shirin Plasm. Amma ya ce a yanzu za su sake sabon lale.

An rubutawa kamfanonin Golden Agri-Resources da sauransu wasika, inda muka rubuta akwai kalubale da ake fuskanta wajen tunkarar shirin plasma.

Siti tare da iyalanta

Asalin hoton, Nopri Ismi

Bayanan hoto, Iyalan Orange Rimba na jiran ganin ta inda kason gonakinsu zai fito

Ranar Litinin ne za a koma dakon man-ja zuwa sassa daban-daban na duniya, bayan gwamnati ta dage haramcin fitar da kowanne nau'in man girki.

A karshen watanjiya gwamnatin ta haramta fitar da shi, a kokarin magance karuwar farashinsa a kasuwannin duniya daga 'yan sari.

Kamfanonin da alhakin tashin farashin man-ja ke kan su, sun ga yadda suke samu mahaukaciyar riba wadda ba su taba gani ba a dan tsakanin nan.

Kudaden da ke kawo wa Indonesia makudan kudade da suka kai miliyoyin daloli, sun doga ne da sayar da man-ja.

Iyalan Widjajah da ke jan ragamar kamfanin Golden Agri-Resources, sun fito cikin sahu na biyu a masu arziki a mujallar Forbes, cikin masu arzikin Indonesia da aka ambata akwai Anthoni Salim, shugaban kamfanin Salim Group, wanda ya zo na biyu a lissafi.

Amma ga kabilar Orang Rimba, sun gaji da jiran ta inda kason su na arzikin man-jan da akai amfani da gonakin da suka gada kaka da kakanni za su fito.

A karkashin wata biyar kwa-kwa, tsohuwa Cilin ce ke waka cikin murya mai ban tausayi. Cikin baitikan akwi inda ta ke cewa: "zukatanmu za su cika da farin ciki, idan jikokinmu suka kasance cikin koshin lafiya''.

Ta yi karin bayani da cewa: "Muna fatan Allah zai yi wa jikokinmu tsahon rai, mu na fatan za a dawo mana da gonakin kakanninmu, ko ba ma raye, jikokinmu za su ci gajiyar abin da ya kasance hakkinmu," in ji ta. "Wannan shi ne abin da muke fatan gani."