Tsananin zafi: Muhimman shawarwarin da hukumomin Saudiyya suka ba maniyyata

....

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Maniyyata sun fara gudanar da ayyukan ibada na aikin hajjin shekara ta 2025 a birnin Makkah da ke Saudiyya.

Hajji, aiki ne da ke buƙatar zirga-zirga da ayyukan motsa jiki da dama, wani abu da ya sanya hukumomi ke fadakarwa game da yanayin tsananin zafi da ake fuskanta a ƙasar daidai lokacin da ake gudanar da waɗannan ayyuka.

Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.

Ma'ikatar, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce wannan yanayi na tsananin zafi na da haɗarin jefa maniyyata cikin yanayi na galabaita da jefa rayukansu cikin hadari.

Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya ƙunshi ɗawafi da zaman Mina da sa'ayi da tsayuwar Arfa da kuma jifar shaiɗan.

Matsakaicin yanayi a Saudiyya na kamawa ne kimanin digiri 45, amma akwai lokutan da yanayin zafi kan zarce maki 50 a wasu yankunan na ƙasar.

Hakan na faruwa ne kasancewar Saudiyya ƙasa ce da ke a yanki ami rairayin hamada.

A kan haka ne Ma'aikatar aikin hajji da Umara ta ƙasar ta bayar da shawarwari kan yadda maniyyata za su gudanar da ayyukan ibada domin kare lafiyarsu.

Zama cikin tanti

Maniyyaci a cikin tanti

Asalin hoton, Getty Images

Shawarar farko da ma'aikatar aikin hajjin da umara ta Saudiyya ta bai wa maniyyata ita ce zama a cikin tanti a lokacin garjin rana.

Sanarwar ta ce "a guje wa fita daga tanti daga ƙarfe 10 na safe zuwa ƙarfe hudu na yamma."

Tsakanin waɗannan lokuta ne rana ke ƙwallewa kuma yanayin zafi ke tsananta.

Sallolin Azahar da Asr

Hukumomin na Saudiyya sun kuma buƙaci maniyyata su guje wa ziyartar masallacin Namirah da kuma Jabal Al-Rahma domin sallolin Azahara da La'asar.

A maimakon haka ma'aikatar ta buƙaci maniyyata su yi sallolinsu a cikin tantunansu.

Yin amfani da abin hawa

...

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomin sun buƙaci maniyyata su yi amfani da hanyoyin sufuri da aka tanada, kamar motocin safa da kuma jiragen ƙasa wajen zuwa Muzdalifah.

Muzdalifah wani fili ne da ke kusa da birnin Makka, inda maniyyata ke shafe dare suna ayyukan ibada.

Amfani da kariya

Maniyyaci a cikin tanti

Asalin hoton, Getty Images

Wata shawarar da hukumomin suka bayar ita ce ta amfani da lema da hulunan malafa domin kare kai daga zafin rana.

Amfani da lema a cewar mahukunta zai taimaka wajen bai wa maniyyaci damar yin aikinsa cikin sa'ida da kare shi daga zafin rana da ka iya kai wa jikinsa kai-tsaye.

Shan ruwa

Ana buƙatar maniyyata su yawaita shan abu mau ruwa-ruwa da kuma shi kansa ruwa domin kauce wa ƙarancin ruwan jiki.

Shan ruwa na mayar da ruwan jiki da maniyyaci ya ƙona a lokacin tafiyar da lamurransa tare da rage hadarin faɗawa cikin yanayi na gajiya ko gazawa.