Mece ce makomar Hezbollah da Lebanon?

Sheikh Hassan Nasrallah, the head of the Lebanese Shiite Muslim movement Hezbollah, wearing a black turban and sporting a beard is seen given a speech

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sheikh Hassan Nasrallah ya shafe shekara sama da 30 yana jagorantar Hezbollah
    • Marubuci, Dima Babilie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • Lokacin karatu: Minti 5

An kashe Sakatare Janar na Hezbollah Hassan Nasrallah a wani harin sama da na Isra'ila a kudancin Beirut.

Nasrallah, wanda aka daɗe ba a gani a bainar jama'a ba tsawon shekaru saboda tsoron kada Isra'ila ta kashe shi, yana cikin masu ƙarfin faɗa a ji a Gabas ta Tsakiya.

Mutuwarsa a Isra'ila nasara ce, amma wasu magoya baya a Beirut sun ce sun kaɗu.

Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hari a Lebanon. Hezbollah ma ta ce za ta ci gaba da harba rokoki a Isra'ila.

Faɗa na kwanan nan tsakanin Hezbollah da Isra'ila ya yi ƙamari ne a ranar 8 ga Oktoban 2023 - lokacin da Hebollah ta kai wa Isra'ila hari - kwana guda bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila wanda ya haddasa yaƙin Gaza.

Yanzu tambayar ita ce mece ce makomar Hezbollah da kuma yankin.

Makoma da alƙiblar Hezbollah

A portrait of Hezbollah chief Hassan Nasrallah sits amid destruction in a area targeted overnight by Israeli airstrikes in Saksakiyeh on September 26

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami'ai sun ce kusan mutum 800 aka kashe a hare-haren Isra'ila a Lebanon tun ranar Litinin.

Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, ƙasashe da dama sun bayyana ta a matsayin ƙungiyar ƴanta'adda da suka haɗa da Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashen Larabawa.

Mutuwar Nasrallah tuni ta haifar da shakku game da makomar Hezbollah. Akwai shakku game da ƙarfin ƙungiyar na ci gaba da manufarta ta yaƙi da Isra'ila.

"Wannan ba zai sauya gwagwarmayar Hezbollah ba na tunkarar Isra'ila, musamman yadda ake ci gaba da yakin Gaza, kamar yadda Ibrahim Bayram ya yi hasashe.

Mai sharhi ne kan harakokin siyasa kuma ɗanjarida ne da ke aiki da jaridar An-Nahar. Yayin da yake magana da sashen BBC na Arabiya, ya bayyana kisan Hassan Nasrallah a matsayin wani muhimmin al'amari.

Ya ƙara da cewa Hezbollah "za ta ci gaba da bin tafarkin da Nasrallah ya gina ta a kai."

A ra'ayoyin jama'a a Lebanon, Bayram ya ce akwai saɓanin ra'ayi tsakanin jama'a. Wasu na murna da a asirce kan mutuwarsa wasu kuma na ganin mutuwarsa babbar ɓaraka ce ga Hezbollah.

Ɗanjaridar na Lebanon ya ce Nasrallah ya san abin da ke jiransa. "Nasarallah ya san makomarsa za ta kasance irin ta tsoffin shugabannin ƙungiyar, kamar Abbas al-Musawi.

Musawi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa Hezbolla kuma a 1992 Isra'ila ta kashe shi.

Smoke rises from the site of an Israeli airstrike that targeted the southern Lebanese village of Khiam on September 28, 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jiragen yakin Isra'ila sun tsawwala hare-hare a Lebanon a kwanakin nan

Iran da Hezbollah

Iran ta ce akwai kwamandan rundunar juyin juya hali da aka kashe a harin Beirut na ranar Juma'a. Jagoran Iran Ayatollah Khamenei, ya nanata goyon bayansa ga Hezbollah amma bai bayyana matakin da Iran za ta ɗauka ba kan kisan Hassan Nasrallah.

A jawabinsa na farko, jagoran na Iran Ali Khamenei ya yi la'anci kisan fararen hula a Lebanon. Ya ce wannan ya tabbatar da "sakarci na shugabannin Isra'ila.

Amma a jawabinsa na ranar Asabar bai ambaci sunan Nasrallah ba.

Khamenei ya bayyana cewa "Isra'ila ba ta da ƙarfin gurgunta tasirin Hezbollah, tare da cewa dukkanin mayaƙa na yankin suna tare da ƙungiyar.

Khamenei ya kuma yi yi kiran goyon bayan Musulmi ga al'ummar Lebanon da Hezbollah.

Abin da zai iya faruwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Iran na son jaddada cewa mutuwar Nasrallah ba za ta yi tasiri ga Hezbollah ba a yankin saboda mutuwar shugabanta.

"Hezbollah ta horar da shugabanni da dama, kuma dukkaninsu sun mutu, wani shugaban ya shiga fagen daga," in ji Ahmad Vahidi. Shi ne tsohon kwamandan mayaƙan juyin juya hali na Ƙurdawa Iran.

Sai dai, Kakakin majalisar wakilan Amurka Mike Johnson, ya bayyana mutuwar Nasrallah a matsayin wata babbatar nasara a Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatin Lebanon ta ɗauki Hezbollah a matsayin halattacciyar ƙungiyar da ke yaƙi da Isra'ila kuma an zaɓi mambobin ƙungiyar a majalisar dokokin Lebanon.

Farfesan Jami'a kuma ɗanjarida Muhammad Ali Moqaled na ganin wannan abin da ya faru zai iya zama wata dama ga Hezbollah ta dawo a matsayin "mai sassauci kan manufarta tare da neman yarjejeniyar da za ta ba Lebanon damar ƙwato dukkanin yankunanta."

Ya kuma nuna cewa mutuwar Nasrallah za ta iya bude ƙofar samar da wata mafita ta siyasa ga Lebanon, ciki har da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Wanda zai iya zama shugaba

The head of Hezbollah's Executive Council Hashim Safi al-Din seen with a black turban and predominantly greying beard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana hasashen Hashim Safi al-Din zai zama shugaban Hezbollah

Mutuwar Nasrallah ta haifar da tambayoyi kan girman muhimman abubuwan da ya bari da magajinsa zai fuskanta a fagen siyasa da soji.

"Ba a san ko magajinsa yana iya gudanarwa da kula da ƙungiyar kamar Nasrallah ba, wanda martabarsa babba ce da karfinsa wajen haɗa kan ƙungiyar, a cewar ɗanjarida Ibrahim Bayram.

Ana ganin shugaban majalisar zartarwa ta Hezbollah Hashim Safi al-Din zai zama sabon shugaban ƙungiyar.

Bayram ya ƙara da cewa a shekaru 40 ba a taɓa tunanin wani fitaccen ɗan Shi'a zai iya fito na fito da Isra'ila ba. "Za a ɗauki lokaci kafin a samu wani rin Nasrallah"

Ɗanjaridar na Lebanon ya bayyana shi a matsayin " shugaba kuma jagora wanda ya haɗa kan ƙungiyar a siyasance da kuma ta fuskar soji."

Akwai sarƙaƙiya ga nasarorin marigayin shugaban na Shi'a, kuma za ci gaba da zama batun da za a daɗe ana muhawara akai.

Yanzu hankalin duniya ya koma kan makomar Hezbolla da kuma sauyin shugabancinta mai cike da tarihi.