Wace rawa sojojin Najeriya da Tinubu ya aika Benin za su taka?

Asalin hoton, HQ NIGERIAN ARMY/FACEBOOK
A daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da shirye-shiryen tura dakaru zuwa Jamhuriyar Benin mai maƙwabtaka da ƙasar domin tabbatar da zaman lafiya da dimukuraɗiyya, tuni an fara tafka muhawa a faɗin ƙasar kan rawar da jami'an tsaron Najeriya za su iya takawa.
Tuni majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike mata, yana neman sahalewarta domin tura sojoji zuwa ƙasar domin kwantar da tarzoma bayan wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a baya bayan nan, inda shugaban ya bayyana cewa zaman lafiya a ƙasar na da muhimmanci ga zaman lafiya a Najeriya.
Sanatocin dai sun kaɗa kuri'ar amincewa da tura sojojin da gagarumar, inda suka bayar da goyon bayan majalisa kan batun tabbatar da tsaro a yankin.
Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya bayyana matakin a matsayin matakin da ya dace, yana mai cewa rashin zaman lafiya a kowace ƙasa da ake maƙwabtaka da Najeriya yana barazana ga ɗaukacin yankin.
Shugaba Tinubu dai ya miƙa buƙatar ne a cikin wata wasiƙa da aka karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.
A cikin wasikar, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatin Benin ta yi gaggawar neman tallafin jiragen sama na musamman daga rundunar sojojin Najeriya bayan da sojoji suka yi yunƙurin hamɓarar da shugaba Patrice Talon.
Shugaba Tinubu ya yi gargaɗin cewa Jamhuriyar Benin na fuskantar "yunƙurin ƙwace mulki ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar ruguza cibiyoyin dimokuraɗiyya".
Yunƙurin juyin mulkin Jamhuriyar Benin dai ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da wasu sojoji suka kutsa gidan talabijin na ƙasar su ka kuma sanar da tsige shugaban ƙasar Patrice Talon.
Me ake nufi da tura sojojin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Domin jin me ake nufi da tura sojojin zuwa Benin da ma aikin da za su yi a can da ma rawar da za su iya takawa, BBC ta tuntuɓi Group Captain Sadiq Garba Shehu (Mai Ritaya), wanda tsohon hafsan sojan sama ne a Najeriya, sannan masani kuma mai sharhi kan harkokin soji da tsaro a ƙasar, inda ya ce Najeriya ta zama tamkar giwar Afirka da dole ta kai ɗauki wasu ƙasashen.
A ɓangaren irin makaman da za su iya tafiya da su, Sadig Garba ya ce ai dama ko ina soja yake
"Da bindiga aka san shi. Amma a ɓangaren manyan makamai kuwa, ya danganta da irin aikin da za su yi. Idan wanzar da zaman lafiya ne kawai bindigar ma ta isa, amma idan yaƙi ake yi muraran dole a tafi manyan makamai irin su tankoki da ma jirage."
A game da irin aikin da dakarun za su yi, Sadiq Garba ya ce akwai aikin sintiri.
"Duk inda za su riƙa zagaye suna rangadi. Idan kuma akwai inda aka shata layi tsakanin ɓangarori biyu da suka samu saɓani, a nan ma su ne za su tabbatar kowa bai shiga ɓangaren wani ba. Amma idan yaƙi ne, dole su tabbatar sun kare rayuwa da kadarorin mutane, wani lokacin ma suna shiga cikin yaƙin a gwabza da su."
Sai dai tsohon hafsan sojan ya ce a ƙa'idar Majalisar Ɗinkin Duniya, bataliyar soja take nema.
"Wato sojoji da hafsoshi tsakanin 700 zuwa 800. Amma a Ecowas, saboda rashin kuɗi sai sukan nemi ƙasa da haka. Wani lokacin suka buƙaci kamfani ɗaya ne wanda yake ƙunshe da sojoji 100 zuwa 130."
A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, Kabiru Adamu ya ce akwai ɓangarori guda biyu, "ko dai a tura dakarun a ƙarƙashin Ecowas ko kuma a tura a ƙarƙashin tattaunawa ƙasa da ƙasa."
A ɓangaren irin aikin da za su yi, Kabiru Adamu ya ce babban aikin da ke gabansu shi ne tabbatar da daƙile dukkan abubuwan da za su haifar da barazanar tsaro.
"A ƙa'ida ya kamata a tsaya ne a kariya kawai, amma saboda yanayin da ƙasashen Afirka ke ciki, akwai fargabar za a iya kai musu hari, ka ga kuwa dole su mayar da martani. Shi ya sa akwai buƙatar a fayace inda ƙarfinsu ya ƙare da irin ƙarfin da za su iya amfani da shi wajen bayar da kariyar."
Gida ya ƙoshi?
Sai dai tun bayan da aka fara batun tura dakarun wasu ƴan Najeriya suka bayyana fargabar cewa ai gida bai ƙoshi ba, ballantana a aiki maƙwabta, inda suke cewa Najeriyar ma tana buƙatar tsaro.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan yunƙurin Amurka na tura sojoji domin taimakon Najeriya ta magance matsalolin tsaronta, sannan Faransa ma ta yi tayin taimakon ƙasar.
Sai dai Sadiq Garba ya ce wannan ba matsala ba ce domin a cewarsa, a harkar diflomasiyya, ba sai ƙasa ta ƙoshi ba ne za ta kai wa wata ƙasar ɗauki.
"Ko Amurka idan za ta je yaƙi, wasu ƙasashen sukan tura mata sojoji duk da ƙarfin sojinta. Wasu ƙasashen ma za ka sun tura sojoji biyu ne kacal. Don haka ya zama kamar biki ne. Najeriya kuma tun bayan samun ƴancin kai, daga cikin abubuwan da take tunƙaho da su akwai aikin wanzar da zaman lafiya. Ko a lokacin da ake tsaka da da Boko Haram da ma matsalar ƴanbindiga Najeriya ta tura sojoji wasu ƙasashe."
Shi ma Kabiru Adamu ya yi na'am da wannan fahimtar, inda ya ƙara da cewa wannan matsalar ta ƙara nuna wa Najeriya cewa abubuwan da ke faruwa a maƙwabta suna da muhimmanci ga tsaron Najeriya.
"Jamhuriyar Benin na da iyaka mai faɗi da Najerya kuma iyakar ta ratsa jihohi da yawa. Don haka duk da cewa akwai fargabar da mutane suke yi cewa Najeriya ma ana buƙatar sojojin, lallai saboda muhimmancin Benin ba zai yiwu Najeriya ta sa ido kawai ba, dole ne ta ɗauki mataki."
Sai dai ya ce akwai buƙatar a ɗauki matakin ta hanyar bin tsare-tsare da muradun tsaro na Najjeriya.
"Akwai muradun tsaro na ƙasa da ake kira 'National security strategy' kuma aikin majalisa ne ta tabbatar tura dakaru zuwa Benin ya dace da muradun tsaron ƙasar wata buƙatar daban ba," in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar a yi gyara a muradun tsaron Najeriya domin wanda ake amfani da shi tun 2019 aka fitar, "kuma ya kamata ne a riƙa gyarawa duk bayan shekara biyar."










