Me ficewar ƙasashen Sahel daga Ecowas ke nufi?

Asalin hoton, @GoitaAssimi
- Marubuci, Aisha Aliyu Jaafar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
A ranar Lahadi, 15 ga watan Disamban 2024 ne ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ta amince da ficewar ƙasashen Sahel wato Nijar, Mali da Burkina Faso daga ƙungiyar.
Ƙungiyar ta bayar da sanarwar ne a ƙarshen taron koli da ta yi a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ta ce daga ranar 29 ga watan Janairun shekara mai kamawa ƙasashen uku za su daina zama mambobin ƙungiyar.
A farkon shekarar nan ne ƙasashen uku suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa ta buƙatar ficewa, saboda a cewarsu ƙungiyar ta kasa magance matsalolin tsaro na ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ISIS da al-Qaeda da ke neman wargaza yankin.
Me ya sa ECOWAS ta amince?
BBC ta yi tattauna dakta El Haroon Muhammad, masani a harkar diflomasiyya da dabarun raya ƙasashe, ya ce dole ce ta sa Ecowas ɗaukar matakin saboda babu alama cewa waɗannan ƙasashen za su dawo cikin ƙungiyar.
''Yadda suka rungumi ƙasar Rasha, yadda suke mu'amala da Turkiyya da Iran, suka kawo musu tsare-tsare da zai kawo cigaban ƙasashen da bunƙasar tattalin arziƙinsu, dole ne ECOWAS ta dubi wannan matsayin'' a cewar shi.
A taron da ƙungiyar ta yi ranar lahadi, ta kuma ce kofa a buɗe take ga ƙasashen Sahel din nan da watanni shida idan sun sauya shawara suna so su koma cikin ƙungiyar.
Dakta El Haroon ya ce sake ba su damar ba zai yi amfani ba saboda ƙasashen na duba amfanin kansu ne.
"Abun da zai kara lalata al'amarin shi ne yadda shugaban Najeriya ya zama babban aminin Faransa, wanda ya ce hakan zai ƙara firgita ƙasashen su janye jikinsu."
Wace irin riba ficewar ƙasashen Sahel ukun zai yi ga ECOWAS?
Dakta El Haroon Muhammad ya ce babu wata riba da ƙungiyar ECOWAS za ta ci, illa ta kara faɗuwa.
''Idan aka ɗauki tarihin ƙungiyar ta ECOWAS, yau wajen shekara 40, duk abubuwan da ta sa a gaba za ta yi ba ta yi su ba, idan tafiya ta kama ɗan mamban ƙasar zai je maƙwabciyar ƙasar, irin wahalar da zai sha a hannun jami'an tsaro, kwastam da sojoji sai ya yi wayyo Allah.''
Ya kuma ce ƙasashen ƙungiyar sun kasa yin kuɗin kansu, sun kasa inganta kasuwanci, manufarsu na kawo haɓɓakar tattalin arziki da magance talauci duk sun gaza.
Wace irin riba ƙasashe ukun za su ci bayan ficewarsu?
Masanin harkar diflomasiyyar da dabarun raya ƙasashe Dakta Elharoon Muhammad ya ce janye jikin ƙasashen uku daga ƙungiyar shi ne alheri a gare su kuma akwai riba da yawa waɗanda sun ma fara ganin wasu daga ciki.
''Ga riba nan suna ci, irin tatsar arzikin da Faransa ta yi musu, ta rike musu wuya, da suka kori Faransa ga shi nan suna ta walwala da su na bunƙasa suna kuma faɗaɗa harkokinsu da kasashen waje. Su ke cin riba." inji Dakta El-Haroon.
Ya kuma ce dole ne ƙasashen sun yi haka saboda sun daɗe ƙasar Faransa na bautar da su, suna daga cikin ƙasashen da su ka fi koma baya a duniya, kuma yin haka shi ne mafi alheri a gare su.
''Tsakanin lokacin da ƙasashen suka kai ruwa rana da Faransa zuwa yanzu an ga sauye-sauyen da suka faru a ƙasashen.''











