Shugaban Rasha ya jefa duniya cikin haɗari, in ji Tarayyar Turai

Vladimir Putin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vladimir Putin ya yi jawabi ga taron jama'a a Moscow, inda aka rubuta kalmar ''Muna tare har abada'' a saman allon talabijin din

Kasashe da hukumomin duniya na ci gaba da yi wa Rasha Allah-wadarai da kakkausar murya kan matakinta na mamaye wasu sassan kasar Ukraine hudu.

Shugaba Biden na Amurka ya ce ba za a bar Moscow ta tsira da kwace yankunan na makwabciyarta ba, yana kuma gargadin Shugaba Putin da cewa ba zai iya razana Amurka da kawayenta ba.

Yayin da su kuma kasashen Turai suka zargi shugaban na Rasha da jefa tsaron duniya cikin hadari.

Daga irin suka da caccaka da Rashar ke ci gaba da sha bayan da Shugaba Putin ya sanar da mamaya ko shigar da yankuna hudun da Rashar ta kame na Ukraine.

Karkashin ikonta, bugu da kari da lasar takobin da ya yi cewa Moscow za ta kare su ta kowace hanya.

Shugaba Biden ya yi gargadin cewa babu wata barazana ta gaba-gadi daga Rashar da za ta razana Amurka.

Mista Biden wanda ke magana a fadar White House bayan Mista Putin ya sanya hannu a kan dokar shigar da yankunan karkashin ikon Rasha tare da bayyana yakin na Ukraine a matsayin wata gwagwarmaya da Yammacin Duniya.

Ya ce Rasha ba za ta sha ba, da wannan kwace da ta yi na kasar makwabciyarta, yana mai alkawarin ci gaba da tallafa wa Ukraine da makamai domin kare kanta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Biden ya ce kalamai da barazanar shugaban na Rasha ganganci ne kawai, kuma bikin da aka yi a Moscow shirme ne da aka saba yi domin nuna karfi – amma kuma maimakon haka ya kasance ya nuna cewa Mista Putin na neman tsira ne kawai.

Ya kuma gargadi Rasha da akul ta sake ta kai wani hari yankin da ya wuce Ukraine, yana mai cewa a shirye Amurka da kawayenta suke su kare kowane takin a yankin kungiyar NATO.

Sakataren Harkokin Waje na Amurkar, Antony Blinken, ya ce kasar ba za ta taba amincewa da yankunan da Rashar ta mamaye ba.

Ya ce, ''ba ta da inganci, ba halacci ba matsayi na doka. Wannan yanki har yanzu na Ukraine ne.

''Har kullum zai kasance bangaren Ukraine. Ba za mu taba amincewa da wannan mamaya ta wannan yanki ba, kuma kamar yadda na ce Ukraine tana da duk wani ‘yanci na ta kare dukkanin yankinta.

Ta kare mutanen da ke nan kuma ta kwato yankinta da aka kwace mata ba ta doka ba tun da farko.''

Sai dai kuma Rashar ta hau kujerar-naki a yayin wata kuri'a da aka kada a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don yin Alla-wadarai da mamayen.

China da India da kuma Brazil sun kaurace wa zaman kada kuri'ar.

Tun da farko a wani kakkausan jawabi na adawa da Yamma da kuma kishin kasa da shugaban Rashar ya yi a Moscow.

Mista Putin ya ayyana cewa mutanen da ke zaune a sassan wadannan yankuna hudu da Rashar ta mamaye – Donetsk da Luhansk da Kherson da kuma Zaporizhzhia, har abadar abadin za su ci gaba da kasancewa Rashawa.

Amurka ta kara kakaba wa jami'an Rasha takunkumi.