Man U da City da Madrid na rububin Lautaro Rivero, Arsenal za ta bayar da Jesus da Martinelli

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan na tattaunawa da Liverpool kan dan wasan tsakiyarta Curtis Jones, mai shekaru 25. (Fabrizio Romano)
Arsenal za ta iya bayar da 'yan wasan gaba na Brazil Gabriel Jesus, mai shekaru 28, da Gabriel Martinelli, mai shekaru 24, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar siyan dan wasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekaru 25. (Teamtalk)
Kazalika Arsenal na daf da kammala sayar da dan wasan bayanta Oleksandr Zinchenko ga Ajax. Dan wasan na Ukraine mai shekaru 29 ya koma Nottingham Forest a matsayin aro a bazarar da ta gabata amma sau hudu kacal ya soma wasa a gasar Premier. (Athletic)
Nottingham Forest na duba yiwuwar siyan golan Manchester City mai shekaru 33, Stefan Ortega, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara. (Florian Plettenberg)
Dan wasan gaba na Holland Joshua Zirkzee, mai shekaru 24, na son ci gaba da zama a Manchester United har zuwa sauran kakar wasan nan, bayan da aka soma danganta shi da komawa Italiya, musamman kungiyar Roma, da aka ce tana sha'awarsa. (Sun)
Manchester City na sa ido kan dan wasan tsakiya na Argentina Lautaro Rivero, na River Plate. Ita ma Manchester United, da Tottenham, da Atletico Madrid, da Juventus da Strasbourg na sa ido kan dan wasan mai shekaru 22, da farashinsa ya kai fan miliyan 86. (El Crack Deportivo)
Real Madrid ta shirya tsaf don siyan ɗan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga, inda suma Arsenal da Liverpool ke sha'awar siyan ɗan wasan mai shekaru 23. (Fichajes)
Karim Benzema yana tunanin komawa Turai bayan kasa cimma matsaya da wata kungiya a Saudiyya. Tsohon dan wasan gaba na Real Madrid da Faransa mai shekaru 38 zai kare kwangilarsa a Al-Ittihad a watan Yuni. (ESPN)
Manchester City na tunanin dawo da dan wasan tsakiyarta na Norway Sverre Nypan, mai shekaru 19, wanda ke zaman aro a Middlesbrough, cikin tawagarsu har zuwa sauran kakar wasa. (Manchester Evening News)
Barcelona na shirin taya dan wasan baya na Manchester United da Argentina Lisandro Martinez mai shekaru 28 a bazara. (Fichajes)











