Takardun kuɗin ƙasashe 10 mafiya rashin daraja a 2026

Ana musayar kuɗin fam na Lebanon da dala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana chanja kuɗin fam na Lebanon da dala
    • Marubuci, Abdalla Seif Dzungu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
    • Aiko rahoto daga, Nairobi Kenya
  • Lokacin karatu: Minti 5

Dalar Amurka ne kuɗin da aka fi cinikayya da shi a duniya, in ma ba a ce shi ne ya fi daraja a duniya (A yanzu Dinar na Kuwait ne ya fi kowane kudi daraja a duniya).

To sai dai a gefe daya ana canja kuɗaɗe mafiya rashin daraja a duniya da dalar Amurka wajen cinikayyar yau da kullum.

A cewar mujallar Forbes, ana sauya dalar Amurka ɗaya da dubban kuɗaɗen wasu ƙasashen.

Cikin wannan muƙala mun duba kuɗaɗen ƙasashe 10 da suka fi rashin daraja a duniya.

1. Fam na Lebanon (LBP)

Ana ganin Kuɗin fam na Lebanon shi ne kuɗin da ya fi kowane rashin daraja a duniya idan aka kwatanta shi da dalar Amurka.

Domin kuwa dalar Amurka ɗaya daidai take da fam 89,556.36 na kuɗin ƙasar Lebanon.

Ƙasar Lebanon - wadda ke a yankin Gabas ta Tsakiya - ta yi iyaka da Tekun Bahar - rum ta ɓangaren yammaci da arewaci, yayin da ta yi iyaka da Isra'ila ta ɓangaren kudanci, Siriya kuma ta gabashi.

Tattalin arzikin ƙasar ya dogara ne da ayyukan ƙwararrun cikinta, sannan takan fitar da ƙarafa masu daraja, da sinadarai da abinci da kuma lemu kala-kala.

Mujallar Forbes ta ce kudin ƙasar ya shafe shekaru yana fuskantar koma-baya sakamakon tafiyar hawainiyar tattalin arzikin ƙasar, da hauhawar farshi da ƙaruwar rashin aikin yi da matsalolin bankuna da kuma rikice-rikice da ƙasar ke fuskanta.

2. Riyal na Iran (IRR)

Wani na ƙirga kuɗin Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kuɗin ƙasar Iran

Mujallar Forbes ta yi ƙiyasin cewa kuɗin Iran shi ne na biyu a jerin kuɗaɗen duniya mafiya rashin daraja.

Forbes ta ce ana canja dalar Amurka ɗaya kan Riyal 42,112.50 na Iran. Kuma an shafe shekaru masu yawa ana canja kuɗin da wannan daraja.

An ƙirƙiro Riyal na Iran a ƙarshen shekarun 1700

Iran - wadda ke yankin Gulf ta yi iyaka da ƙasashen Iraƙi da Afghanistan - na gaba-gaba a ƙasashen da ke fitar da man fetur da iskar gas a duniya, amma takunkuman tattalin arziki da aka sanya mata sun sanya gagarumin matsi kan darajar kuɗin ƙasar.

3. Dong na Vietnam (VND)

Wani na ƙirga kuɗin ƙasar Vietnam, Dong.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kuɗin ƙasar Vietnam, Dong

A cewar mujallar Forbes, Dong na ƙasar Vietnam ne kuɗi na uku cikin mafiya rashin daraja a duniya.

Forbes ta ce ana canja dalar Amurka ɗaya kan Dong 26,345.

Vietnam ta yi iyaka da tekun kudancin China da ƙasashen China da Laos da kuma Cambodia.

Ayyukan gwamnati ne kan gaba wajen tara wa ƙasar kuɗin shiga, daga nan sai kamfanonin makamshi da lantarki da yaduka.

Kuɗaɗen ƙasar sun yi fama da takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa ƙetare da kuma raguwar fitar da kayayyaki daga ketare a baya-bayan nan, ga kuma tsawon lokaci na yawan kuɗin ruwa a Amurka.

4. Kip na Laos (LAK)

Kudin Kip na ƙasar Laos ne kudi na huɗu a jerin mafiya rashin darajar a duniya.

Mujallar Forbes ta yi ƙiyasin cewa ana canja dalar Amurka ɗaya kan 21,663.26 na kip.

Laos ƙasa ce da ba ta da gaɓar ruwa, inda ƙasashen Vietnam da Thailand da Cambodia da China suka zagaye ta.

Ta dogara kusan kacokan kan fitar da kayayyaki kamar ƙarafa da zinare da katako.

Ƙasar na fama da rashin bunƙasar tattalin arziki, da ƙaruwar basukan waje da hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya taimaka wajen durƙusar da darajar kuɗin na kip.

5. Rufiyan Indonesiya (IDR)

Wani na ƙirga kuɗin Rufiyan Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kuɗin Rufiyan Indonesia

An ƙirƙiro da kudin rifiya na Indonesioya a shekarar 1946, kuma a yanzu kudin na cikin kuɗaɗe mafiya rashin daraja a duniya.

Ana can dalar Amuka ɗaya a kan rufiya 16,849.37, a cewar mujallar Forbes.

Indonesiya ta ƙunshi tsibirai fiye da 17,000 a tekun Fasific, ciki har da Java da Sumatra da wasu sassan Boneo da New Guinea.

Ƙasar ce gan gaba wajen tara arzikin cikin gida a ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, saboda bunƙasar ayyukan gwamnati a ƙasar.

Indonesia na da arzikin kayayyaki, amma kudin ƙasar ba shi da daraja saboda matsalar hauhawar farashi da fargabar durƙushewar tattalin arziki.

6. Som na Uzbekistan (UZS)

A shekarar 1993 aka ƙirƙiro da Som a matsayin kuɗin ƙasar Uzbekistan a hukumance.

Sai dai a yanzu kuɗin na cikin waɗanda ba su da daraja idan aka kwatanta da dalar Amurka.

A cewar mujallar Forbes ana canja dalar Amurka ɗaya kan som 11,861.84.79.

Uzbekistan - wadda a baya ke cikin tsohuwar tarayyar Soviet - na tsakiyar yankin Asiya.

Ta kasance ɗaya daga ƙasashen da ke kan gaba wajen fitar da auduga a duniya, sanna tana da tarin ma'adinai da man fetur da iskar gas jibge a ƙarƙashin ƙasa.

A cewar Forbes, Uzbekistan ce ƙasar da ta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, amma ta ci gaba da fama da matsalar tattalin arziki da ƙaruwar hauhawar farashi da rashin aikin yi da cin hanci da rashawa.

7. Franc na Guinean (GNF)

An ƙirƙiro da kuɗin franc a matsayin kuɗin ƙasar Guinea a 1959, sai dai a yanzu kuɗin ya kasance cikin mafiya rashin daraja a duniya.

Ana canja dalar Amurka ɗaya kan franc 8,658.25, a cewar mujallar Forbes .

Guinea - wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka - na yankin kudu da hamadar sahara a Afirka.

Ƙasa ce mai arzikin ma'adinai kamar zinare da azurfa, to amma matsalar hauharwar farashi da rikicin soji da tuɗaɗar ƴangudun hijira daga ƙasashen laberiya da Saliyo sun karya darajar kuɗin ƙasar.

8. Franc na Burundi (BIF)

Franc na Burundi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Franc na Burundi

Ƙasar Burundi - wadda ba ta da gaɓar ruwa - na yankin gabashin Afirka.

Ana canja dalar Amurka ɗaya kan farnc 8,754.96 na Burundi.

Ƙasar - mai yawan al'umma miliyan 14 - ta yi iyaka da Rwanda ta arewaci da Tanzaniya ta gabashi/kudu maso gabashi, da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo a yammci.

Ganyen shayi da gahawa ne kashi 90 cikin 100 na bin da ƙasar ke fitarwa.

9. Ariari na Madagascar (MGA)

A shekarar 1961 aka ƙirƙiro da Ariari, inda a 2005 ya maye gurbin franc a matsayin kuɗin Madagascar a hukumance.

sai dai da alama kudin bai samu daraja da tagomashi ba, domin yanzu haka ana canja dalar Amurka ɗaya kan ariari 4,637.73 a cewar mujallar Forbes.

Madagascar ƙasa ce da ke wani tsibiri a kudu maso gabashin Afirka.

Noma da haƙar ma'adinai da kula da shukoki ne manyan hanyoyin samun kuɗin shigar ƙasar.

Haka kuma tana fitar da turaren wuta da kwalli da kuma kanumfari.

10. Guarani na Paraguay (PYG)

An fara amfani da guarani a matsayin kuɗin Paraguay a 1952.

Yanzu haka ana canja dalar Amurka ɗaya kan guarani 6,619.11 a cewar Forbes.

Ita ma ƙasar Paraguay ba ta da gaɓar ruwa, inda ta yin iyaka da ƙasashen Brazil da Argentina da kuma Bolivia.

Ƙasar ke kan gaba wajen noman waken suya da samar da ɗan zaƙi da naman shanu da noman dawa.

Kuɗin ƙasar na fama da matsalolin hauhawar farashi da cin hanci da ƙwacen kadarori.