Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa zai fi ƙoƙari a muhawara tsakanin Trump da Kamala?
- Marubuci, Jeremy Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
- Lokacin karatu: Minti 5
Za a yi muhawara ta biyu kafin zaɓen shugaban Amurka ranar Talata, kuma ita ce ta farko da za a fafata tsakanin Donald Trump da Kamala Harris.
Ana kallon muhawarar 'yantakarar shugaban ƙasa sosai a talabijin kuma takan yi tasiri kan yadda Amurkawa za su yi zaɓen.
An ce Kamala Harris ta ƙware wajen muhawara amma kuma Trump ya nuna cewa shi jajirtacce ne a muhawarar 2016 da 2020.
Yaushe za a yi muhawarar kuma mene ne dokokinta?
Za a tafka muhawarar ne a Philadelphia ranar 10 ga watan Satumba. Za a fara da ƙarfe 9:00 na dare agogon Eastern Time.
Wannan ce muhawarar ƴantakarar shugaban ƙasa ta biyu a 2024. An yi ta farkon ne a watan Yuni tsakanin Trump da Shugaba Biden, kafin daga baya ya yanke shawarar janyewa daga takarar.
Za a yaɗa ta a tashar ABC ta talabijin, da ABC News Live, Disney+, da Hulu duka a intanet.
An saka tsauraran sharuɗɗa kan lokacin magana. Kowane ɗantakara na da minti biyu domin amsa tambayoyin da masu gabatarwa za su yi, kuma yana da wani minti biyun na mayar da martani.
Za a kashe makirfo na mutum idan ɗayan yana magana, kuma ba za a bari 'yan kallo su shiga zauren ba.
Kamala ta so a bar makirfo ɗin a buɗe tun daga farko har ƙarshe amma daga baya ta amince da kashewa.
An fara yin hakan ne shekara huɗu da suka wuce bayan muhawarar Trump da Biden ta ƙare da yi wa juna kutse da cecekuce.
Muhawarar za ta kasance ƙarƙashin gabatarwar mutum biyu, David Muir da Linsey Davis waɗanda masu gabatar da labarai ne a kafar ABC.
Me Kamala ta fi ƙwarewa a kai wajen muhawara?
Kamala Harris ta shiga muhawarar zaɓe tun daga 2003, lokacin da ta lashe zaɓen zama babbar mai shigar da ƙara ta gundumar San Fransisco.
Ta kuma shiga muhawara a zaɓen zama antoni janar ta California, da kuma kujerar sanata mai wakiltar jihar.
Ta yi muhawara da Joe Biden a 2019 lokacin da suke neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat, kuma ta fafata da Mike Pence a muhawarar 'yantakarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2020.
Ta nuna irin yadda take iya mamaye al'amura. A muhawarar 2020 tare da Mista Pence, ta gargaɗe shi loakcin da ya yi ta katse ta tana magana da cewa:"Mai girma Mataimakin Shugaban Ƙasa ina magana."
Kamala ta samu ƙwarewa sosai a fannin muhawara saboda zamanta a majalisar dattawa da kuma aikin da ta yi a matsayin mai shigar da ƙara a kotunan California, inda babban aiki a nan shi ne fito da gazawar wanda ake tuhuma.
Wannan zai iya taimaka mata idan tana son ƙalubalantar wasu abubuwan da Trump ya faɗa a muhawarar.
Sai dai kuma, ta gaza wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa a 2020, inda ta fice daga takarar tun kafin kaɗa ƙuri'a a Iowa kuma ɗaya daga cikin sukar da aka yi mata ita ce ba ta da cikakkun tsare-tsare.
A muhawarar Talata, akwai yiwuwar za a tambayi Kamala tambayoyi masu tsauri kan tsare-tsarenta.
Kamala ta kuma sha yin kalamai masu yawa idan tana yin jawabi.
Misali, a hirar kwanan nan da ta yi da CNN ta ce: "Abu ne da ke buƙatar kulawar gaggawa wadda ya kamata mu tunkara da mizanai domin ganin ba mu wuce lokacin da muka tsara ba."
A muhawarar shugaban ƙasa, lokaci a ƙure yake kuma dole ne a aika wa masu zaɓe a fayyace.
Mece ce ƙwarewar Trump a muhawara?
Muhawarar da Kamala za ta yi da Trump ranar Talata, ita ce abu mafi tsauri da za ta fuskanta tun bayan zama 'yartakara.
Ya yi muhawarar shugaban ƙasa sau biyu a 2016 da 2020, kuma ya nuna shi ɗin fa ba abokin adawar da aka saba gani ba ne.
A muhawarar 20216 da Hillary Clinton, ya dinga fuskantar 'yan kallo kuma yana tsaye a bayanta a lokacin da take magana, abin da ya sa ta ce "ta ɗan ji wani abu".
A karon farko na muhawarar 2020, ya yi ta katse Joe Biden har ma ya ce masa: "Za ka yi mana shuru malam?"
Irin wannan salon kan janye hankalin abokin muhawararsa kuma ya sa 'yan kallo su dinga mayar da hankali a kansa.
Sai dai kuma, Mista Trump kan sauka daga kan maudu'in da ake magana a kai, kuma ya dinga faɗar abubuwan da ba su da tushe.
Wane ne kan gaba a ƙuri'ar ra'ayin jama'a?
Kafin ya haƙura da takarar a watan Yuli, Joe Biden na bayan Trump a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a ta ƙasa baki daya da kuma jihohin da ba su da alƙibla.
Cibiyar RealClearPolitics da ke sharhi kan harkokin siyasa, ta ce Kamala ta ƙara shahara sama da Trump tun da ta zama 'yartakara. Ta ce tana gaban Trump da maki 1.9 a ƙuri'ar ƙasa ya zuwa 3 ga watan Satumba.
Amma kuma, Hillary Clinton ta taɓa wucewa gaba da maki biyar a ƙuri'ar ƙasa a lokaci irin wannan a 2016 kuma ta faɗi zaɓen.
Ƙuri'un ra'ayioyi a cikin jihohi, ana kallon sun fi muhimmanci sama da na ƙasa.
Saboda ƙuri'un da aka kaɗa a jihohi ne ke tantance adadin abin da ɗantakara ya samu, sai kuma ƙuri'u na musamman (electoral college) su tabbatar da wanda ya ci zaɓen.
Akwai 'yan jihohin da ba su da alƙibla a siyasance kamar Arizona da Georgia da Michigan da North Carolina da Pennsylvania da ke da muhimmanci ga ɗantakara. Babu tazara tsakaninsu a duka waɗannan jihohi.
A farkon watan Satumba, RealClearPolitics ta ce Kamala ta yi ƙoƙarin bai wa Trump tazara a Michigan da Georgia kuma tana kankankan da shi a Pennsylvania, amma har yanzu take bayansa a Arizona da North Carolina.
Abin da masu sharhin siyasa suka amince da shi shi ne ba za a iya hasashen wanda zai cinye zaɓen ba saboda kusanci.
Ɗantakara na buƙatar ƙuri'u na musamman 270 kafin ya yi nasara. Yanzu ƙuri'ar ra'yoyi na nuna cewa 'yan Democrat (kamala) na da tabbacin cin 226 daga cikinsu, 'yan Republican kuma (Trump) za su ci 219, sauran kuma kowa zai iya cinye su.