Yadda za ku tsaftace firji domin kauce wa kamuwa da cutuka

Asalin hoton, Getty Images
Ɗakin dafa abinci ne zuciyar gida, domin daga can ne ne iyalai suke shirya abin da za a girka, sannan daga can ake fara cin abinci.
Amma anya daga can ake fara shirin girki? daga firji ne. A firji ne ake adana yawancin kayan abincin. Kuma yanzu da aka samu ci gaba kimiyya, su kansu firjin ana samun sauye-sauye; suna iya adana ɗanɗanon abincin, sannan akwai masu yaɗa labarai.
Amma duk da waɗannan ci gaban da aka samu, lura da yanayin sanyi ya fi muhimmanci. Muna amfani da firji ne domin adana abinci, amma idan yanayin sanyin bai yi daidai ba, abincin lalacewa zai yi, inda yake zama matattara ƙwayoyin cuta.
Da muka yi nazarin gidaje da dama, mun gano cewa firjinsu yawancinsu yana ɗauke ne da yanayin sanyin maki 5.3 a ma'aunin celsius, wanda ya haura matakin da aka amince da shi na tsakanin maki 0 zuwa 5 a ma'aunin Celsius.

Asalin hoton, Getty Images
Abin da ya fi ɗaga hankali shi ne yadda yanayin sanyin ke sauyawa. Yawancin firji sun fi ɗaɗewa a yanayin sanyi sama da wanda ya ake buƙata.
Wasu firjin ma suna kai har yanayin maki 15, a wasu sassan na Birtaniya, wannan yanayi ne mai ɗan ɗumi.
A wannan matakin, ƙwayoyin cuta suna hayayyafa cikin sauri, wanda ke jawo saurin lalacewar abinci, da ma jawo rashin lafiya.
Don haka mece ce matsalar? daga cikin matsalolin akwai kasancewa yawancin firjin ba su da na'urar kula da matakin sanyi. Maganar gaskiya yawancinmu ba mu ma san amfanin lambobin da suke cikin firginmu ba.
Haka kuma a lokuta da dama idan muka buɗe firji, iska na fitowa. Sannan irin daɗewar da firjin ya yi buɗe, shi ne irin yadda yanayin sanyin firjin zai yi daidai da na ɗaki, wanda ke ƙara ba ƙwayoyin cuta dama su ƙara hayayyafa.
Kula da ƙwayoyin cuta
Ga wasu hanyoyi da za a kula da abinci domin hana ƙwayoyin cuta gurɓata su:
• A rage yawan buɗe firji. A guji barin firji a buɗe na tsawon lokaci idan ana saka kayan abinci a ciki.
• A riƙa goge robobin da ke jikin ƙofar firji. Duk bayan wasu ƴan watanni a riƙa dubawa tare da tabbatar da robobin suna ƙalau.
Haka kuma yanayin sanyin cikin firji yana bambanta. Yawanci can baya ya fi sanyi, sannan kusa da ƙofa ya fi ɗumi.
Shi ya sa ya fi kyau a riƙa ajiye kayan abinci irin su madara da ɗanyen nama a can baya. Kusa da ƙofa kuma ya fi dacewa da lemun kwalba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa yawancin firji na zamani suna da na'urar la'akai da yanayin sanyi a cikinsu, suna bayyana yanayi ne wa wani lokaci kawai. Haka kuma kusan kashi 68 na gidaje ba sa canja yanayin sanyin na tsawon lokaci.
Ta yaya za a gane? a sanya na'urorin ɗaukar yanayin zafi ko sanyi a ɓangarori da dama na firjin. Idan ɗaya daga cikinsu ya nuna maki 5 a lokuta da dama daban-daban, lokaci ya yi da za ka ƙara ko ka rage.
Haka kuma yana da kyau a guji cike firji maƙil. A yi ƙoƙari ya zama bai fi kashi 75 ba ne ake cikewa domin iska ya samu damar gudana a ciki. Za ka iya rage cika firjin ta hanyar adana wasu kayayyakin irin su tumatur da zuma da gyaɗa a waje saboda ba su cika buƙatar yanayin sanyi ba.
Haka kuma wani bincike ya nuna cewa firji kan zama matattara ƙwayoyin cuta, waɗanda wataƙila suke yawo a ciki a sanadiyar gurɓataccen abinci da aka ajiyewa.
Idan yanayin sanyin firjin ya yi ƙasa, zai hana ƙwayoyin cutar hayayyafa, amma akwai na'ukan ƙwayoyin cuta irin su Listeria da suke iya hayayyafa ko a yanayin sanyi kaɗan ne.
Za a iya samun ƙwayar cutar Listeria a bamdan kifi da kayan lambu, kuma ƙwayar cutar na da illa ga mata masu ciki da tsofaffi.

Asalin hoton, Getty Images
Domin rage gurɓacewar abinci, za a iya bin waɗannan matakan:
• A ajiye ɗanyen abinci irin su kifi fa nama daban daga ɓangaren irin su kayan lambu da kayan ƙwalama.
• A ajiye ɗanyen nama da kifi da ƙasan firjin saboda ko da ruwan naman ya zuba, ba zai gurɓata abin da ke ƙasa ba.
• A ci abincin da ba sai an dafa da zarar an ciro su daga firji da aƙalla sa'a huɗu.
• A wanke hannu a kai-a-kai da ruwa da sabulu bayan kammala aiki.
Lura da firji ba dole ba ne ya zama abu mai daɗi, amma yana taimakawa wajen adana abinci, su kuma ƙara daɗewa, sannan shi kan shi firjin zai fi yin aiki da yau, sannan hakan zai taimaka wajen inganta lafiyarka da na iyalinka.

Asalin hoton, Getty Images
* Oleksii Omelchenko masanin ƙwayoyin halitta ne da ke nazari kan ƙwayar cutar Listeria da sauran ƙwayoyin cututtuka a cibiyar Quadram Institute da ke Norwich a Ingila. Judith Evans kuma farfesan kimiyyar injina ne a jami'ar London South Bank University.











