Barcelona ta hau kan teburin La Liga bayan cin Celta Vigo

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta doke Celta Vigo 3-2 a wasan mako na shida a La Liga da suka fafata ranar Asabar a Sifaniya.

Jorgen Strand Larsen ne ya fara ci wa Celta Vigo kwallo a minti na 19 da fara tamaula, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Anastasios Douvikas ya kara na biyu.

Sauran minti tara a tashi daga wasan Barcelona ta fara farke kwallaye, inda Robert Lewandowski ya zura biyu a raga, sannan Joao Cancelo ya kara na uku daf da za a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta daya a kan teburin da maki 16 kafin Real Madrid mai maki 15 ta buga wasanta.

Ranar Lahadi Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan hamayya a karawar mako na shida.

Ranar Talata Barcelona za ta je gidan Real Mallorca a karawar mako na bakwai a La Liga.

Ita kuwa Celta Vigo za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ranar Alhamis a dai wasan babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wasan da suka kara a bara a tsakaninsu 2022/2023:

Gasar La Liga Lahadi 4 ga watan Yunin 2023

  • Celta Vigo 2 - 1 Barcelona

Gasar La Liga Lahadi 9 ga watan Oktoban 2022

  • Barcelona 1 - 0 Celta Vigo

Kociyan Celta Vigo, Rafael Benitez ya yi nasara a wasa biyu a baya a gidan Barcelona a La Liga na ƙarshe shi ne shekara 20 da ta wuce.

Ya doke Barcelona 4-2 lokacin yana Valencia a Janairu da kuma 1-0 a Oktoba a shekarar 2003 duk a kungiyar.