Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

Mista Oyebanji ya samu kuri'u 178,057.

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, Mista Oyebanji ya samu kuri'u 178,057.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.

A daren da ya gabata ne hukumar INEC ta ce Mista Oyebanji ya samu kuri'u 178,057.

Hakan ya sanya jam'iyyar All Progressive Congress ta zamo wadda ta samu kuri'u mafi yawa a zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022.

Dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party, Olusegun Oni, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri'u 82,211.

Sai jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) wadda ta zo ta uku, inda dan takararta Bisi Kolawole ya samu kuri'u 67,457.

Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam'iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya tal.

Tun da maraicen ranar Asabar ne dai jami'an hukumar INEC suka dukufa wajen kirga kuri'u bayan rufe rumfunan zabe.

A bangare daya kungiyoyin farar-hula da suka sa ido a zaben sun yaba da shirin da hukumar zabe ta yi.

Kama daga nagartar na`urorin tantance masu kada kuri`a da isar da malamai da kayan zabe zuwa rumfunan zabe a kan kari.

Sannan an fara zaben a kan lokaci. An kuma kammala lafiya-lafiya ba tare da samun wani yamutsi ba, face zargin sayen kuri`a.

Sai dai jami`an hukumar EFCC sun cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi suna sayen kuri'un.

Amma masu sa idon sun koka a kan rashin sanin adadin mutanen da suka karbi katinsu na zabe a jihar ta Ekiti.

A daya bangaren wata jami'ar hukumar zaben ta tabbatar da cewa INEC din ta sanar da adadin tun a can baya.

Sakamakon zaben na nufin Biodun Abayomi Oyebanji zai jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa a matsayin gwamna.

Sai dai wani abu shi ne tun bayan dawowar mulkin demokradiyya a Najeriya, ya zuwa yanzu babu gwamnan da ya yi nasarar cin wa`adi biyu a jere.

Adeniyi Adebayo din shi ne aka zaba gwamna a tutar jam'iyya Alliance for Democracy a shekarar 1999, ya nemi wa`adi na biyu amma sai Ayo Fayose ya masa kaye a 2003.

Shi ma bai wuce shekara uku a kan kujerar ba sai `yan majalisar dokokin jihar suka tsige shi a shekara ta 2006 bisa zargin kama shi da rashawa.

Da aka yi zabe a shekara ta 2007 sai Segun Oni, wanda a wannan karo ya yi takara a jam'iyya SDP ya samu nasarar zama gwamna.

Sai dai shi ma bai gama cin wa`adin na farko ba kotu ta sauke shi, inda aka nada dan takarar jam`iyyar ACN, Kayode Fayemi a matsayin wanda ya ci zaben gwamna a shekara ta 2010.

Shi ma Fayemi ya so wa`adi na biyu a shekara ta 2014, amma sai Ayo Fayose ya ba shi ruwa.

A shekara ta 2018 Fayose ya so ya bar magaji daga jam`iyyarsa ta PDP, amma sai Kayode Fayemi ya dauki fansa ya sake hayewa kujerar gwamna, wa`adi na biyu.