Ƴan takara 16 za su fafata a zaɓen gwamna a jihar Ekiti

A yau ne ake bude rumfuna domin gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.
`Yan takara goma sha shida ne suke fafatawa a zaben.
Masu sa-ido a kan zabe dai na fargabar cewa wasu `yan siyasa za su yi amfani da kudi wajen sayen kuri`u, amma hukumar zabe ta ce ta dauki matakai.
Bayan hamayyar zahiri da ake gani a tsakanin `yan takara, akwai kokawar manya da ake yi a badini.
Tsohon gwamnan jihar Ayo Fayoshe, wanda ke goyon bayan dan takarar jam`iyyar PDP da kuma gwamna mai barin gado, Kayode Fayemi da ke fatan jam`iyyars ta APC ta ci gaba da mulki, duka sun yi wa juna kaye a baya.
Wannan ne ma ya sa wasu ke ganin cewa hamayyar da ke tsakaninsu ta fi ta masu takara.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Segun Oni da ke takara da tutar jam`iyyar SDP ya mulki jihar na shekara uku kafin kotu ta tube shi a shekara ta 2009.
Sauran jam`iyyun da ke fafatawa a zaben su ne Accord da AAC, da ADC da ADP da APGA, da APM Da APP da jam`iyyar Labour da NNPP da NRM da PRP da YPP da ZLP.
Rahotanni da masu sa ido a kan zabe ke fitarwa sun nuna cewa idon wasu `yan takaran ya rufe suna amfani da salo da dabaru daban-daban domin su kai bantensu, ciki har da sayen kuri`u.
Mista Paul James jami`i ne kungiyar YIAGA, da ke sa ido a kan zaben a jihar Ekiti, ya ce 'yan takara na amfani da kudi wajen sayen kuri'u.
A cewar sa ana sayen kuri'ar ne da kudin da suka kama daga Naira 500 zuwa dubu ashirin.
Sai dai hukumar zaben Najeriyar, kamar yadda jami`arta Hajiya Zainab Aminu ke cewa ta dauki matakan magance matsalar.
Daga cikin matakan da hukumar zaben ta dauka a cewar jami'ar, akwai hana yin amfani da waya mai daukar hoto a cibiyoyin kada kuri'a, da ajiye akwatin kada kuri'a a bainar jama'a da kuma gayyato jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, wadanda za su lura da abubuwan da ke wakana da kuma kama duk wanda ake zargi da kokarin sayen kuri'a.
Kusan mutum miliyan daya ne suka yi rajistar zabe a jihar Ekiti, fiye da kashi 70 cikin dari sun karbi katin zabensu, kuma su ne ake sa ran za su yi tururuwa a rumfunan zabe domin kada kuri`a a kananan hukumin jihar 16.
Rundunar `yan sandan Najeriya ta ce ta tura jami`anta sama da dubu goma sha bakwai, ga kuma sauran jami`ai daga hukumar tsaron na Civil Defense da DSS da sojoji da sauran ma`abota damara domin samar da tsaro a lokacin zaben.
Zaben gwamnan dai na cigaba da jan hankali kasancewar za a yi shi ne a karkashin da sabuwar dokar zabe, wadda shugaba Buhari ya rattaba mata hannu.











