Muhimman abubuwa 10 na sabuwar dokar zaben Najeriya ta 2022

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar zabe ranar Juma'a 25 ga watan Fabrairu bayan da majalisar dokokin kasar ta yi wasu gyare-gyare kan wasu tanade-tanade na dokar.
Ga muhimman abubuwa 10 da sabuwar dokar ta tanada kan 'yan takara da masu zabe:
1. Ba hukumar zabe kudi da wuri
Sashe na 3(3) na dokar ya tanadi cewa a rika bai wa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, dukkan kudin da take bukata ta gudanar da babban zabe akalla shekara guda kafin ranar zaben.
Dokar na son a bai wa hukumar zaben kudade da wuri ne domin ta sami damar shiryawa da wuri.
2. Amfani da fasahar zamani domin tura sakamako
Sashe na 50 na dokar na cewa hukumar zabe mai zaman kanta na da ikon yanke hukunci kan aikawa da sakamakon zabe a takarda ko ta hanyar amfani da fasahar zamani wato kwamfuta.
3. Ikon sake duba sakamakon zaben da aka tursasa wa jami'an zabe
Sashe na 65 na sabuwar dokar zaben ya bai wa INEC ikon sake duba sahihancin sakamakon zaben da aka tursasa wa jami'an zabe fitarwa.
Dokar na son hana 'yan siyasa samun damar matsa wa ma'aikatan hukumar domin su ayyana wani sakamako na bogi.

4. Mataki na 'yan ba-ruwanmu
Sashe na 8(5) ya bukaci ma'aikatan hukumar zaben su zama wadanda ba su karkata bangaren wata jam'iyar siyasa ba ko su kasance masu ra'ayin wata tafiya ta siyasa.
Wannan na nufin ba zai yiwu 'yan siyasa su rike mukamin jami'an zabe ba.
Sashen ya kuma tanadi cewa dukkan jami'in hukumar INEC da aka samu yana da alaka, ko yana rike da ra'ayi na wata jam'iyyar siyasa, ya aikata laifi.
Kuma za a iya yanke masa hukuncin biyan tara ta naira miliyan biyar ko a daure shi na shekara biyu, ko ma a dora masa nauyin duka biyun.
5. Za a rika tantance masu zabe da Card Reader
Sashe na 47 na sabuwar dokar zaben ta Najeriya na cewa tilas a tantance masu zabe da na'urar nan ta 'Card Reader', ko da wata na'urar da hukumar zaben ta bukaci a yi amfani da ita.
6. Ba a bar masu lalura a baya ba
Sashe na 54(2) kuwa ya bukaci hukumar zabe ta Najeriya ta tabbatar ana bai wa masu lalura da nakasa kulawa ta musamman a rumfunan zabe ta hanyar samar musu da hanyoyin sadarwa da suka dace da nakasar da suke da ita.
7. Hana yin aringizo a akwatin zaɓe
Sashe na 51 na dokar zaben ya tanadi cewa za a rika amfani da "adadin wadanda aka tantance" ne gabanin fara zabe idan rikici ya biyo bayan sakamakon da aka wallafa a rumfar zabe.
Irin wannan sakamakon na biyo bayan aringizon da ake yi ne, inda yawan wadanda suka kada kuri'u ke zarce yawan wadanda aka tantance a akwatin zabe.
8. Gudanar da zaben fitar-da-gwani da mika sunayen 'yan takara
A karkashin Sashe na 29(1) na sabuwar dokar, tilas ne dukkan jam'iyyun siyasa su mika wa hukumar zabe sunayen 'yan takararta, wadanda aka zaba daga halastattun zabukan fitar-da-gwani na jam'iyyar.
Kuma ana bukatar sunayen akalla kwana 180 (wata shida ke nan) kafin ranar zaben.

9. Gudanar da gangamin siyasa da wuri
A Sashe na 94 na dokar zaben, an tsawaita kwanakin da jam'iyun siyasa ke da su na yin gangami da yakin neman zabe daga kwana 90 (wata uku) zuwa kwana 150 (wata biyar) kafin ranakun zabe.
Kuma ana bukatar jam'iyyun su dakatar da gamgamin kwana guda kafin ranar zaben.
10. Sauya dan takarar da ya mutu da makomar masu yi wa gwamna da shugaban kasa hidima
Kashi na 34 na dokar kuwa ya bai wa jam'iyyun siyasa a Najeriya damar gudanar da wani zaben fitar da gwani domin maye gurbin dan takarar da ya mutu bayan an fara gudanar da zabuka.
Amma kafin a sanar da sakamakon zaben, sannan gabanin a sanar da wanda ya lashe zaben.
Idan zaben na wata mazaba a majalisa ne, za a sake yin zaben ne, inda za a ba jam'iyyar da dan takararta ya mutu kwana 14 domin ta zabo wani dan takarar da zai maye gurbin mamacin.
Idan kuma mutuwar dan takarar mukamin shugaban kasa ake magana, abokin takararsa (wanda ke takarar mukamin mataimakin shugaban kasa) ne zai maye gurbin dan takarar da ya mutu.
Akwai kuma Sashe na 84 da ya ce tilas dukkan masu taimaka wa gwamna da shugaban kasa, kamar ministoci da kwamishinoni da masu bayar da shawara da sauransu, su ajiye mukamansu kafin su sami damar shiga zaben a matsayin dan takara ko wakilin jam'iyya.










