Babu adalci a zargin shugaba Buhari na jan kafa kan dokar zaɓe - Garba Shehu

Shugaba Buhari

Asalin hoton, BUHARISALLAU

Fadar Shugaban Najeriya ta ce babu adalci idan aka zargi cewa shugaba Muhamamdu Buhari na jan kafa wajen sanya hannu a kan kudirin dokar zaɓe ta 2022.

Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyoyin fararen hula da wasu masu ruwa da tsaki sun zargi shugaban da jan ƙafa wajen sa hannu a kan dokar duk da ɗumbin muhimmancinta.

Mai magana da yawun Shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu ya ce masu waɗannan zarge-zarge ba su yi wa shugaban adalci ba.

Sannan ya sake sake jadada cewa a ranar Juma'a 26 ga watan Fabarairu shugaba Buhari zai sa hannu kan ƙudurin dokar zaɓen da ake ce-ce-ku-ce a kanta.

Abubuwan da fadar ta faɗa

Malam Garba Shehu ya ce ba wai da zarar an kai wa shugaba Muhammadu Buhari takardu sai ya rattabawa hannu nan ta ke ba, dole sai ya duba ya yi nazari kafin hakan.

Dalilansa na yin haka kuwa shi ne da zarar ya yi kuskure ba kan shi kadai zai tsaya a ciki ba, zai shafi Najeriya baki daya, in ji Garba Shehu.

''Ko yanzu haka da ake shirin sa hannu a kan dokar, kar a yi mamaki nan gaba idan lauyoyi suka dauki wani ɓangare na su, suka gabatar da ita gaban shari'a, kuma indai aka gano an yi ba daidai ba ko saɓawa kundin tsarin mulki, zai iya bada umarnin a rushe ta baki daya.

Wanda duk ya san tsarin mulkin Najeriya bai ce sai dole an kafa dokar zabe watanni shida gabannin zaben ba, maganar harkar zabe idan an yi mata kyakkyawar fahimta aba ce mai sauki".

A baya dai an kai wannan doka gaban shugaba Buharin amma ya ce ba zai sanya hannu ba saboda wasu dalilai. Aka sake maidawa majalisa ta yi wasu gyare-gyare, tare da sake maidawa shugaban, wanda 'yan Najeriya sukai tunanin nan take zai rattaba hannu,sai kuma hakan ba ta faru ba.

Sai dai Garba Shehu ya ce babu laifi a cikin sake dawo da dokar, domin sake nazarinta baki daya.

Wasu dai na ganin in dai ba a sanyawa dokar hannu ba kan lokaci, hakan zai shafi jadawalin zaben shekarar 2023. Amma Garba Shehu ya ce tsarin mulkin Najeriya ne gaba da hukumar zabe.

Kuma tsarin mulkin ya bai wa shugaban kasa kwanaki 30 kan duk dokar da ta zo gabansa kafin ya sanya mata hannu, sai idan wannan wa'adi ya cika bai yi hakan ba ne dokar ke komawa hannun majalisa idan sun samu rinjayen kashi biyu bisa uku su na da damar aiwatar da ita.

''Ko hukumar zabe da ta ce ta fito da tsarin zabe daga nan zuwa shekara guda, ina dokar da ta bada izinin yin hakan? babu ita, don haka hukumar zabe ba ta da izinin aiwatar da dokar da bata cikin tsarin mulkin Najeriya, ko dokokin majalisar kasa.

Wani ya zo ya ce shugaba Buhari ya ci zabe da tsafta, yanzu ya zama cikas ga harkar zabe, babu adalci a cikin wadannan gunduma-gunduman maganganu, a dinga yi wa shugabanni adalci.''

Karin haske

Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, domin matsa wa shugaban ƙasar lamba ya sa hannu a kan ƙudurin dokar zaɓen 2022.

Kungiyoyin sun ce rashin sa hannun a kudurin dokar ya sa an makara a shirin tunkarar zaben shekarar 2023.

Sun kuma ce doka ta yi tanadin cewa hukumar zabe ta sanar da takamaimai ranakun zabe shekara guda kafin zuwan lokutan.