Bidiyo: Namijin da ke takarar kujerar shugabar mata ta APC a Najeriya

Bayanan bidiyo, Bidiyon hira da namijin da ke takarar kujerar shugabar mata ta APC a Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ameer Sarkee mai shekara 26, wanda yake takarar kujerar shugabar mata a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ya fito takarar ne domin namiji ne ya kamata ya riƙa lura da al'amuran mata a ko wanne lokaci.

Ameer ya taɓa tsayawa takarar kujerar shugabar mata a jam'iyyar PDP reshen jihar Kano a 2019 amma bai yi nasara ba, sai dai ya ce a wannan karon ba zai bari a kayar da shi ba saboda tun yana karamin yaro batutuwan da suka shafi mata ya fi son aiwatarwa.

"Tun ina ƙaramin yaro idan na ga mace tana buƙatar taimako nakan yi ƙoƙarin taimaka mata - kamar ɗaukar kaya ko sayo musu wani abu - kuma hakan ne ya sa nake son zama shugaban mata na jam'iyyarmu," a cewarsa.

"Wasu mutane suna tambayata abin da ya sa nake takarar kujerar shugabar mata kuma amsar da nake ba su ita ce 'Allah ya halicci namiji domin ya zama mai lura da lamuran mata'", in ji Ameer