Najeriya: Anya shugaba Buhari zai sanya hannu kan dokar zabe?

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, @BUHARISALLAU

Ɗaya daga cikin manyan alƙawurran Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari shi ne inganta zaɓen ƙasar tsawon mulkinsa, sai dai ga alama wankin hula yana neman kai shi dare.

Kungiyoyin fararen hula dai sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, suna matsa wa shugaban ƙasar lamba don ya sa hannu a kan ƙudurin dokar zaɓen 2022.

Kungiyoyin sun yi zanga zangar ce don neman shugaban na Najeriya ya yi abin da ya dace.

Kungiyoyin sun ce rashin sa hannun a kudurin dokar ya sa an makara a shirin tunkarar zaben 2023.

Kungiyoyin sun ce doka ta yi tanadin cewa hukumar zabe ta sanar da takamaimain ranakun zabe shekara guda kafin zuwan lokutan.

Masu magana da yawun shugaba Buharin, na ta nanata cewa shugaban na dab da sa hannu kan kudurin dokar to amma har yanzu shiru.

A baya dai shugaba Buhari ya sha nanata alkawarin inganta zabe a zauruka da dama kamar a zauren cibiyar tabbatar da zaman lafiya ta Amurka.

Rashin sanya hannu a kan dokar ballantana a tabbatar da fara aiki da ita na kara sanyaya gwiwar 'yan kasar.

Masana kimiyyar siyasa a Najeriyar kamar Dakta Abubakar Kari ya shaida wa BBC cewa, shi a ganinsa abubuwan da ke faruwa game da dokar zaben sun wuce shugaban na jan kafa.

Ya ce. "A hankali abubuwa na fitowa fili karara a kan cewa shugaban Najeriyar, baya son ya sanyawa dokar hannu ne".

Masanin siyasar ya ce "Wannan shi ne karo na shida a tsawon shugabancin Buhari da ake kawowa masa wannan doka amma sai ya samu wani dalili don yaki saka mata hannu".

Dakta Kari, ya ce " A yanzu fa 'yan Najeriya da dama sun daina gamsuwa ko kuma ba zasu gamsu da duk wani hanzari da zai bayar ba ganin cewa a baya ya ce idan aka cire wasu abubuwa a dokar zai sanya hannu gashi kuma an yin amma bai sa ba".

Babban abin da ke daure mini kai shi ne kamar shugaba Buhari bai damu da abin da tarihi zai fada a game da shi ba, in ji Dakta Kari.

Masanin siyasar ya ce, duk da ya ke shugaba Buhari shi ya fi kowa cin gajiyar tsaftataccen zabe, to amma kuma ya zamo cikas game da yunkurin da ake shekara da shekaru na ganin cewa an gyara wannan doka ta zabe.

Sharhi

Masana da masu fafutuka a Najeriya sun ce wannan lamari dai na da matukar hadari ga tarihin siyasar shugaba Buhari dama dimokradiyyar Najeriya.

Da yawansu dai na ganin cewa jan kafar da shugaban kasar ke yi wajen kin sanya hannu a dokar zaben zai sanya a dauko dokar zaben 2010 ayi amfani da ita a 2023, hakan kuwa wani gagarumin koma baya ne ga siyasar Najeriya.