Muhammadu Sa'ad Abubakar: Tarihin rayuwar Sultan na Sokoto, Sarkin Musulmin Najeriya

Asalin hoton, Daular Usmaniyya
Mai alfarma Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ya cika shekara 15 a matsayin Sarkin Musulmin Najeriya.
A ranar 2 ga watan Nuwamba ne aka naɗa Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku a matsayin Sarkin Musulmin Najeriya, yau shekara 15 kenan bayan rasuwar yayansa Sultan Muhammadu Maccido a hatsarin jirgin sama a ranar 29 ga watan Oktoban 2006.
Sultan Sa'ad ɗan Sarkin musulmi Abubakar na uku ne shi kuma ɗan Mallam Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu Usman Danfodiyo.
Sultan Sa'ad shi ne Sarkin Musulmin Najeriya na 20 tun daga Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo wanda ya rayu daga shekarar 1754 zuwa 1817.
Sultan Sa'ad na III ya zamo Sarkin Musulmi mai ilimin addini da na zamani wanda ya kawo sauye-sauye na ci gaba sosai a mulkinsa.
Albarkacin wannan rana ne BBC Hausa ta yi duba kan rayuwarsa tare da tattaunawa da Bello N Junaidu na cibiyar da ke tattara tarihin Daular Usmaniya a Sokoto.
Tarihin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad
An haifi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar a ranar 24 ga watan Agusta 1956, kuma ɗa ne ga Sarkin Musulmi na 17 Sir Abubakar na III, wanda ya yi mulki tsawon sama da shekara 50.
Bello N Junaidu na cibiyar da ke tattara tarihin Daular Usmaniya a Sokoto ya ce Sarkin ya samu ilimin addinin Musulunci da na zamani tun daga tasowarsa.
Ya yi karatun addini a makarantar Masallacin Shehu kusa da gidan Sarkin Musulmi - ya yi makarantar Uban Doma a Sokoto kafin ya tafi Kwalejin Barewa da ke garin Zariya.
Bayan nan kuma ya wuce kwalejin aikin soji ta Najeriya wato Nigerian Defence Academy a shekarar 1975.
Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya samu matsayin Second Lieutenant a shekarar 1977, inda daga baya ya zama kwamandan runduna ta musamman da ke tsaron Shugaban kasa na mulkin soja a lokacin wato Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Sarkin ya yi ayyuka da dama na wanzar da zaman lafiya a Najeriya da Afrika da sauran ƙasashen duniya.
Sarki Sa'ad ya jagoranci rundunar hadakar sojojin Afrika a karkashin kungiyar Tarayyar Afrika, da aka girke don samar da zaman lafiya a Chadi a shekarun 1980.
Kazalika ya rike mukamin mai shiga tsakani daga bangaren kungiyar raya tattalin arzikin Afrika wato ECOWAS daga shekarar 1995 zuwa 1999.
Shi ne kwamandan da ya jagoranci bataliyar 231 ta sojojin ECOMOG a yaƙin Saliyo daga 1999 zuwa 2000.
Ya yi karatu da samun horo a Indiya da Canada a matsayin soja - yana cikin wadanda suka tafi babban taron majalisar Ɗinkin Duniya na wanzar da zaman lafiya da rage kwararar makamai da aka gudanar a Accra babban birnin ƙasar Ghana.
Daga shekarar 2003 zuwa 2006 ne Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar ya zama jakadan Najeriya mai ba da shawara kan tsaro a kasar Pakistan.
Kuma saboda nuna ƙwarewa da nasarorinsa aka ƙara girman aikinsa a Paskistan zuwa Iraƙi da Iran da Afghanistan da Saudiyya a matsayin bai bayar da shawara kan tsaro a zamanin mulkin Obasanjo.
Ya kai muƙamin Birgediya Janar kafin aka naɗa shi Sarkin Musulmi. Ya yi ritaya a ranar 30 ga watan Disamban 2006 bayan shafe shekaru 31 a aikin soji.
A ranar 2 ga watan Nuwamban 2006 ya karɓi sarautar Sarkin Musulmin Najeriya, bayan rasuwar yayansa Sultan Muhammadu Maccido a hatsarin jirgin ADC da ya bar Abuja zuwa Sokoto a ranar 29 ga watan Oktoban 2006.
Bayan zamowarsa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya kuma samu matsayin shugaban kungiyar Musulmi ta Jama'atul Nasril Islam (JNI), kuma shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).
Haka ma a 2015 ya shiga jerin fitattun mutane 10 da suka samu karramawar Global Seal of Integrity (GSOI), bisa rawar da ya taka wurin samar da hadin kai tsakanin al'ummu a Najeriya da ma ƙetare.
Gudunmawar Sarkin Musulmi Sa'ad

Asalin hoton, Other
Ana ganin Sultan ya bayar da gundumma a fannoni da dama na ci gaban al'umma.
Haɗin kai - Masana tarihi sun ce Daular Usmaniyya an kafa ta ne saboda karantarwar addinin islama na saukaka wa mutane da kuma yin adalci.
Sarki ne da ke da'awar ganin an fahimci juna tsakanin mabambantan addinai a Najeriya - idan an samu fahimta za a samu zaman lafiya.
Sarki Sa'ad ya yi ƙoƙarin haɗa kan al'ummar Najeriya da ke da bambancin addini ta fuskar fahimtar juna.
Lokacin azumi yakan gayyato mutane da suka ƙunshi musulmi da kirista wurin buɗa baki da nufin samun fahimtar juna duk da bambancin addininsu.
Sarki Sa'ad ya ɗauki matakai na kaucewa samun ruɗani a lokacin ganin watan azumi domin haɗin kan musulmi.
Ba a taɓa samun lokacin da Sarki Sa'ad ya yi jayayya da wani ɓangare na addini ba ko wata akidar musulmi.
Sarkin ya rungumi dukkanin ƴan siyasa, inda ba a taɓa samun rahoton saɓaninsa da shugabannin gwamnati ba a shekaru 15 na mulkinsa.
Ya yi kokarin haɗa kan sarakuna a Najeriya a matsayinsa na shugaban majalisar sarakuna ba tare da nuna bambancin ƙabila ba.
Tsaro - Sarki Sa'ad ya zo zamanin da ake samun matsalar tsaro kamar rikicin Boko Haram da hare-hare ƴan bindiga a Najeriya.
A matsayinsa na tsohon soja kuma masanin tsaro kuma shugaban al'umma an sha gayyatarsa wajen bayar da shawarwarin yadda za a magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Gwamnatin tarayya tana gayyatarsa duk wani taro na tsaro kuma yakan kaucewa haddasa rudani tsakanin masu mulki da mutane.
Saboda matsalolin tsaro da ya jefa mutane cikin mawuyacin hali, Sarkin ya samar da cibiya ta taimakawa al'umma da rikici ya shafa.
Raya ilimi- Ya yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaban ilimi a matsayinsa na uba musamman a jihar Sokoto.
Sarkin Musulmi Sa'ad ne ke jagorantar aikin farfado da ilimi a jihar Sokoto bayan ayyana aikin gaggawa kan farfaɗo da ilimi a jihar.
Sannan a zamaninsa an fassara litattafan mujaddadi na Usman Danfodiyo da Abdullahi fodio da Muhammadu Bello da Nana Asma'u domin al'umma.
"Yanzu ya ruɓanya aikin fassarar da marigayi Abubakar Imam ya yi da aikin da aka yi zamanin Sarkin Musulmi Dasuki," In ji masanin tarihin Daular Usmaniyya Bello N Junaidu.
Haka kuma daga cikin ayyukansa na bunƙasa ilimi da ci gaban al'umma, Sarkin ya ƙirƙiro da wani zama duk ranar Alhamis na ƙara wa juna sani kan matsalolin yau da kullum inda ake gayyayo malamai su gabatar da takarda kan wani maudu'i
Sarkin ya ƙara raya gidauniyar raya ilimi da al'umma a jihar Sokoto wadda tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ke jagoranta wato "Sokoto Development Trust.
Duk lokacin bikin Sallah, Sarkin yakan tara sarakuna da shugabanni da masu hannu da shuni a tattauna kan matsalolin ilimi da bayar da shawarwari, sannan a tara wa gidauniyar kuɗi.
Bello N Junaidu ya ce ana amfani da kudin gidauniyar wajen koya wa mutane aikin hannu da za su yi dogaro da kansu kamar koyon kwafuta da tela da sauran ayyukan hannu.
Gina Masallatai - Masanin tarihin Daular Usmaniyya Bello N Junaidu ya bayyana cewa Sarkin Musulmi ya gina masallatai a wurare da dama wanda a cewarsa ba a san adadinsu ba.
"Ya gina masallatai a Nasarawa da Kogi kuma ba a san yawan masallatan da ya gina ba," in ji shi.
Gyaran Hubbare: Gyaran makwancin magabata na daga cikin gudunmuwar Sarki Sa'ad.
Masarautar Daular Usmaniyya ta ce Sarki Sa'ad ya gyara inda ƙabarin Muhammadu Fodiyo mahaifin Usman Danfodiyo da aka binne a yankin Gwadabawa.










