Charlie Hebdo: 'Harin maƙabartar Jiddah na da alaƙa da zane-zanen ɓatanci ga Annabi

A watan da ya gabata an kashe wani mai gadin ofishin jakadancin Faransa a Jiddah

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Karamin ofishin jakadancin Faransa a Jiddah
Lokacin karatu: Minti 2

Fashewar da wani abu ya yi a wata makabartar da ba ta Musulmi ba a birnin Jiddah da ke Saudiyya yayin wani biki na ranar tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu ta tayar da hankulan hukumomin kasar.

Jakadun kasashen waje har ma da 'yan kasashen waje mazauna Saudiyya sun halarci bikin, kuma gommai cikinsu sun sami raunuka.

Ma'aikatar harkokin waje a Faransa ta ce abin fashewar bai kashe kowa ba, sai dai ya raunata bakin da aka gayyata bikin da ake yi daga shekara sai shekara domin karrama dakarun sojin da suka sadaukar da rayukansu domin kare kasashensu.

Gwamnatin Faransa ta kira wadanda suka kai harin matsorata, kuma ta bukaci gwamnatin saudiyya ta gano kuma ta hukunta wadanda ke da alhakin kai harin.

Duk da babu cikakken bayani, amma wani dan jarida dan kasar Faransa da ke makabartar a lokacin da ka kai harin ya ce maharan sun jefa gurnati ne, amma gwamnatin Faransa cewa ta yi wani abin fashewa da aka hada a ne aka kai harin da shi.

Entrance to Jeddah Ceremony for non-Muslims following a suspected bomb attack on 11 November 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hoton makbartar da aka kai harin a birnin Jiddah

Akwai kuma wasu hotunan da wani dan jarida dan kasar Faransa da ke aiki a Saudiyyar ya wallafa a Tiwita da ke nuna jinin wadanda suka suka sami rauni ya fallatsa kusa da furannin da aka tara a makabartar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai har lokacin da ake hada wannan rahoton hukumomin Saudiyya ba su ce komai ba kan wannan harin da aka kai cikin kasar tasu ba.

Amma an tsaurara matakan tsaro a birnin na Jiddah tun bayan da wasu wanda ba a san ko su wane ne su ba suka daba wa wani mai gadin karamin ofishin jakadancin Faransa wuka kusan mako biyu da ya gabata.

Saudi police close a street leading to a non-Muslim cemetery in the Saudi city of Jeddah where a bomb struck a World War I commemoration attended by European diplomats on 11 November 2020

Asalin hoton, Getty Images

Ko shakka babu, wadannan jerin hare-haren kan 'yan kasar ta Faransa da kaddarorinsu a Saudiyya na nuni ga abu guda ne kawai.

Harin mayar da martani ne kan hotunan batancin nan na Annabi Muhammad da mujallar Charlie Hebdo ta wallafa, wadanda kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya rika kare matakin da mujallar da ma wasu 'yan kasar Faransa suka dauka na ci gaba da wallafa hotunan - inda yake cewa wallafa hotunan yana karkashin 'yancin fadin albarkacin bakin 'yan Faransa ne.