Saudiyya za ta biya diyya ga iyalan ma'aikatan lafiyar da cutar korona ta kashe

Al'ummar Saudia

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa za ta samar da tsarin biyan diyya ga iyalan ma'aikatan lafiyar da suka rasa ransu sakamakon annobar cutar korona.

Majalisar ministocin kasar ta ce za a bayar da dala dubu 130 ga iyalan mutanen ko da kuwa ba 'yan ainihin kasar ba ne matuƙar dai sun mutu sakamakon aikin taimakon da suka bayar a asibiti ga waɗanda suka kamu da cutar ta korona.

Za a fara bayar da diyyar ne daga farkon watan Maris mai zuwa bayan an kammala tattara dukkan bayanan mamatan.

An samu waɗanda suka mutu sakamakon cutar korona a ƙasar fiye da dubu biyar, yayin da adadin wadanda suka kamu kuma ya zarta 340,000.

Annobar korona dai ta sa kasahen duniya ba su samu damar zuwa kasashen aikin Hajjin bana ba, abin da ya sa 'yan kasar 10,000 ne kadai suka sauke farali a shekarar 2020.

A cikin watan Oktoba ne mahukuntan kasar suka sanar da sake bude masallacin Al-Haram na Ka'abah - wuri mafi tsarki da daraja ga Musulmai bayan an rufe shi na tsawon wata bakwai.

Kafofin watsa labarai na Saudiyya, kamar tashar talabijin ta Saudi Television da shafin Tuwita na Haramain Sharafain, sun ruwaito cewa an ƙyale 'yan kasar har da mazauna birnin Makkah shiga harabar Masallacin Ka'abah domin yin salloli biyar na farali da ma sauran ibadu.

An dai rufe masallacin ne saboda annobar cutar korona wadda har ta shafi ayyukan ibada kamar aikin Hajji da na Umarah.

Maniyyata daga ƙasashen waje ma ba a bar su a baya ba, domin daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2020 ne za a kyale maniyyata daga dukkan kasashen duniya su fara gudanar da Umarah har ma da ziyartar Rawdah Sharif - wanda shi ne mataki na uku cikin shirin mayar da al'amuran ibada yadda aka san su a ƙasar ta Saudiyya.